TAKUN SAAKA 15

“Ummi inje in kwanta?”.
Hibbah ta katse mata tunani. Shafa kanta Ummi tai tana murmushi. “A’a ban gama da ke ba. Dan banji ita autata tana da saurayi ba ko a’a?”.
Da sauri Hibbah ta ɓoye kanta tana dariya. “Kai Ummi ni banda wani saurayi. Nifa bazanyi aure ba muna tare mutu karaba”.
“Tab, to auta an taɓa haka kuwa. Muma ai munason zaman gidanmu aka ɗakkomu aka kawo mu naku gidan muka haifeku.” Ummi ta faɗa tana dariya.
“Ni dai bazanyiba ALLAH Ummi. Banason nesa da ke da su Yaya. Indai zanyi aure sai dai mutafi tare ko mijin yazo ya zauna a gidanmu to”.
Dariya sosai Ummi keyi, irin wadda ta jima batayi ba a rayuwarta. Tanee ɗinta kayan shirme da wauta kenan. Da ana haka da ƴaƴa da yawa na tare da iyayensu ai.
Tashi Hibbah tai da gudu ta haye gadon Ummi ta kudundune a bargo ita a dole kunya ta kama ta. Ummi da ke dariya tace, “To shikenan ai ke baki da matsala tunda Junaid ɗan gidan nan ne sai kiyi zamanki tare dam……”
“ALLAH Ummi bana sonsa. Da na auri mugun nan gara na mutu”. Hibbah tai saurin yaye bargon idanunta na cikowa da hawaye. Yayinda fuskarta ke nuna tsananin tsoro da tsanar Junaid ɗin da Ummi ta ambata.
“To shikenan naji. Amma ai kina son Isma’il ko?”.
Idanu Hibbah ta zaro waje a firgice. “Wane Isma’il ɗin Ummi?”.
“Mai zuwa nan gidan mana”.
“Ni dai wlhy a’a Ummi. Shi yayana ne dan ALLAH kibar faɗa.”
“Oh ALLAH, ke kuwa Tanee wa kike so a rayuwarki? To ko wanda yazo dubani a asibiti jiya? Muhammad Shuraim ko?”.
Baki Hibbah ta turo amma batace komai ba. Ummi ta cigaba da faɗin, “Tanee kinga shima alamunsa sun nuna mutumin kirki ne nutsatstse. Ina ƙyautata masa zaton alkairi insha ALLAH. Amma zansa ai bincike a kansa inhar kina son nasa”.
Kwanciya Hibbah tai ta juyama Ummi baya. “Ni Ummi ALLAH ya cika iyayi. Gashi baida fara’a. ga shishshigi ”.
“Duk shi kaɗai?. To lallai tunda kika iya gano waɗan nan kina sonsa kenan, zaki kuma auresa”.
Da sauri Hibbah taja bargo da cewa, “Nifa Ummi a’a baiminba. Sai naje China na dawo zanyi aure”.
“Tanee wannan mafarkinki ne. Amma ban fidda miki ran zaki cikashi ba idan kinyi aure mijinki ya kaiki da kansa”.
Shiru Hibbah tayi dan an taɓo mata inda kuma bata son. Itama Ummi sai bata sake tankawa ba ta cigaba da hidimarta da lissafin ƙullawa da kwancewa.
Zuwa takwas Ammar ya shigo ya tada Hibbah dansu haɗa breakfast su wuce islamiyya duk da sunyi latti. Hibbah kamar zatai kuka ta bisa. koda sukaje kitchen ɗin suna aikin suna faɗa har sai da Yaya Abubakar ya shigo ya tsawatar musu saboda kuka da Ammar ya saka Hibbah.
Suna kammalawa sukai shirin islamiyya. karyawar ma a tsaitsaye sukayita suka fice.
★★★
A yinin ranar su Yaya Muhammad duk a gida sukayisa. Suna tare da Umminsu suna shan hira. Basu sake mata maganar tarinta ba, itama batai musu ba. Sai bayan sallar zuhur suma suka wuce islamiyya. Ganin dai har zuwa yamma babu motsin Abbah da su Hajiya Mama yasa Ummi fita wajen maigadi ta tambayesa ko sunyi tafiya ne.
Baiyi mamaki ba. Dan yasan kaf yaranta a fusace suke da Abban. Bayanin faɗuwar Abban ya bata da kaisa asibiti da akai. Kuma har yau babu wanda ya shigo gidan tun jiyan. Duk da abinda suke mata bataji tayi farin ciki da tsautsayin daya afkawa Abban ba. Sai ma komawa tai falonta ta faɗa duniyar tunani……..
_________________________________
A ɓangaren Abba ba ƙaramar jigata yay ba kafin safiya. Ƙafafu sun kumbura suntum. hakama fuskarsa tamkar ƙwaɓun fulawar sabon burodi. Sauƙinsa ma allurar barci da likitocin sukai masa ganin yanda yake rusar kuka ƙafarsa na masa zogi.
Sai kusan huɗu na maraice mai gyaran yazo, a cewarsa sun sami lalacewar motane a hanya. Sai dai kuma a zahirin gaskiya ƙaryama yake bai taho ba sai da safen. Komai likitocin basu ce ba. Sai ma damar yaje yay aikinsa da suka bashi, dan haka suka basu sallama.
Ummi na tsaka da tunaninta taji shigowar motoci, mikewa tai ta leƙa ta windown falonta sai ta hango ana fita da Abbah da ga motar Junaid tamkar gawa. Wani irin faɗuwa gabanta yay. Babu shiri ta fito zuwa tsakar gidan itama. Kusan tare suka shiga sashen Momy da su Hajiya mama da ke biye da mai-gyara da Junaid da suka ɗakko Abba ranga-ranga.
A tsakkiyar falon momy aka shimfiɗe Abba. Sai dai ganin yana numfashi yasa Ummi batace komaiba tabi layin ƴan kallo. Mai-gyara ya fito da kayan aikinsa. sanin abinda zaije ya dawo ya sashi faɗama Junaid cewar ya samo wanda zasu tayasa riƙe Abba dan shi kaɗai bazai iyaba. Badan Junaid yaso ba ya mike ya fita. Babu jimawa sai gashi tare da mai-gadinsu da na maƙwafta. Sai wasu yaran makwaftansu su biyu sa’annin Ammar.
“Yauwa kayi farar dabara da kukazo da yawan”. Cewar mai gyara yana gyara zamansa sosai a gaban kafafun Abba da sukai suntum har ƙyalli sukeyi.
Junaid da mutanen daya gayyato baki ɗaya suka zagaye Abba mai-gyara ya fara aikinsa. Sai dai abin mamaki duk da barcin da Abba keyi ana taɓa ƙafar yay wata iriyar mahaukaciyar zabura da ballara ihu. “Wayyyyyyyoooooo!!!!!! ALLAH na zasu kasheni na shiga uku ni Halilu!!!”.
Babu wanda ihun Abba bai gigita ba a falon. amma ahaka mai-gyara ya cigaba da aikinsa ko tausayi babu. Ihu Abbah yake da iya ƙarfin iko. Tun yana zufa har takai ga sakin fitsari. Can fa abin mamaki da kunya sai ga kashi.
Hanci su Ameerah suka shiga toshewa. Su kansu masu riƙon nashi ji suke kamar su sakesa su gudu dan azabar warin kashin. Suma kuwa yayi ya farfaɗo yafi sau uku. Tun yana ihu da murya mai kauri har ya koma siririya. Daga baya ma akabar jinta gaba ɗaya.
Duk yanda Ummi taso daurewa sai da taji hawaye sun ciko mata idanu. Tai ƙasa da kanta saboda tausayi.
A cikin wannan halin su Hibbah suka fara dawowa gidan. Ihun Abba ne ya ringa jan hankalinsu suka dinga nufo sashen duk da sun manta shekarar karshe da suka shiga sashen. Su kansu tsoro ya kamasu ganin yanda Abban ya koma. Badan sun so ba dole suka dinga toshe hancuna suma saboda wari.
Mai gyara ya ɗora kafa da hannun Abba. Sauran raunikan ma aka gyara. Ya shafa magani ya bada wanda za’a cigaba da masa amfani da shi. Kafin a cake masa ƴan kuɗaɗensa masu nauyi. Aka kuma kaisa masauki dan yace sai da safe zai wuce yamma tayi.
Sai lokacin Hajiya Mama ta farga da su Ummi da yaranta. Ido ɗaya ta kanne ta shiga zazzaga bala’i wai sunzo ganin ƙwaƙwaf. Cikin subutar baki Hibbah taja wani wawan tsaki da faɗin, “Kaɗan ma ya gani. Ummin mu yaso gani a wanann kwatankwacin bala’in sai shi ALLAH ya tsundumasa. In takamarsa zalunci wataran ƙafar za’a guntule…..”