Uncategorized

TAKUN SAAKA 15

     Wata muguwar cafka Hajiya mama ta kaima Hibbah ta ko kwasa a guje tabar sashen. Zata bita Junaid ya riƙota cikin masifa. “Barta kakus. Nine nan zanci uban uwarta, wancan bakin nata mai kama da na reza yau sai na ɓaɓɓarkasa wlhy. Shegiyar yarinya mai bakin akku. Idanma an sakata tazo ta faɗa ne to ina dai-dai da kowane shege a gidan nan. Wama ya sani ko kada mana shi akaiyi. Kai bama zan yardaba ALLAH sai munje kotu”.

        Tsaki Ammar yaja tare da kama hannun Ummi suka fice. Su Yaya Muhammad ma kai kawai suka girgiza sukai gaba abinsu da barin su Hajiya mama da takaici. Dan so sukai su tanka su kwashe komai sukai wajen ƴan sanda. Daga nan a wuce kotu har ALLAH yasa sukai gaɓar da suke fata. To sai akai rashin sa’a yaran Ummi masu lurane suka manna musu hauka.

      Koda suka koma sashensu basuga Hibbah ba. Sun san ta boye kanta a daki ne saboda tasan tayo laifi, tunda suma suna hanata rashin kunyar. Alwala ma duk sukayi suka fice masallaci. Ummi ma ta nufi ɗakinta gabatar da tata duk da tana jiyo hayaniyar su hajiya mama daketa zage-zage har yanzun. 

       Koda suka dawo bayan sallar isha’i Hibbah bata yarda ta fitoba har suka ci abinci sukai hira kowa ya tafi makwanci. Babu kuma wanda ya nemeta dan a tabbatar mata batai dai-daiba. 

      Tun a daren maƙwafta ke shigowa duba Abba dan sunji ihun da yayta zugawa. Duk wanda ya shigo sai su hajiya mama suce yaran Ummi ne suka jima Abban ciwo. Da yawa ba yarda suke ba, saboda sunsan halin matsi da Ummi ke fuskanta a gidan da yaranta tun suna kanana. Dan tunkan ma Hajiya mama ta dawo gidan da zama idan tazo da ga ƙauye haka zataita zubda tujara wa Ummi kala-kala, tunda kuwa mijinta ya rasu ta dawo da zama baki ɗaya sai Ummi ta shiga uku ta lalace itada ƴaƴan ta, gashi nan har yanzu basu huta ba. 

  *_______________________________*

               Shiru kakejin Master da yaransa tamkar basa ƙasar. Babu kalar takalar da jami’an tsaro basu masa ba a kafafen ƴaɗa labarai yay kunnen uwar shegu da kowa. Ko randa zancen kai matar gwamna koto ya fito da ga hukumar yaƙi da ta’annatin kayan gwamnati babu wanda yaji ko tarin master. Shi dama ba sanin taka mai-mai accaunt na duka handles nashi akai ba. Dan kullum cikin canja salo yake. 

        Sun cigaba da saka idon ganin kozai tanka amma shiru, dan haka suka cigaba da shirya masa tarkuna ta ƙarƙashin ƙasa dan sunsan tabbas zaije kotun.

    ★★ 

      Yau da yamma Hibbah na makaranta ta fito class cike da gajiya da yunwa. Fatanta kawai ta samu motar komawa gida da wuri dan su Hafsat tuni sun wuce saboda ba department nasu ɗaya ba. Su kuma yau duk lecture ɗin safe sukayi. Ita kaɗaice tayi na yamma.

          Ta samu da yawan ɗalibai dake ta tutsutsun shiga motar da duk tazo wucewa. Dan haka tai gaba saboda kanta dake ciwo. Cikin sa’a kuwa tana matsawa gaban sai ga wata taxi ta faka gabanta. Batare da tunanin komaiba ta afka ciki bayan ta sanarma direban inda zai kaita, shi kuma ya faɗa mata kuɗin. Ko ragi bata nema ba dan buƙatarta kawai taje gidan da wuri. Saboda tana tsoron abinda zaije ya dawo ne musamman akan dangin Abbansu dake cike da gidan nasu dubiyar Abba. Dan zuwa yau da yake cika kwana uku jikin nasa da sauƙi. 

      Ƴan can asalin kauyensu ne sukazo mota guda duba shi. Sai dai hakan ya bama Ummi mamaki da su kansu, dan sam da ga Abba har hajiya mama bason mu’amula da ƴan ƙauyen sukeba yanzun. Shiyyasa har ƙasan ranta takejin akwai wata a ƙasa da suke ƙullawa. 

        Wasu hawayen tausayin Ummi da su kansu ya cika mata ido. bayan hannu tasa ta share tare da kwantar da kanta jikin sit ɗin ta lumshe idanu ko kanta zai sassauta sara mata…….

         Ummi nacan na dakon jiran dawowar Hibbah itama, dan yau da kanta ta soyama Hibbar wainar filawa da tasan tana matuƙar so. Yayinda can ƙasan ranta ke cike da fargabar taruwar dangin mijin nata da nata a gidan. Dan tasan akwai abinda suke ƙullawar da gaske. Sai dai kuma ta saka a ranta komi zasu ƙulla insha ALLAHU ta gama shirya musu a wannan karon. dan itama tun a jiya data fita ta gama tsara komai akan makomar ƴaƴanta. Nasu kawai take jira yanzu ta ɗora da ga inda ta tsaya.  

        Ilai kuwa hasashen Ummi yayi dai-dai, dan tana tsaka da wannan tunanin akai kiranta sashen Abba ɗin. Hijjab ta saka har ƙasa ta tafi. Tun a falo Maomy ta sakar mata wani habaicin da ya tsaya mata a rai. Sai dai batace komai ba ta ƙarasa falon Abba.

        Su kawu Bello ta samu da wasu a dangin Abban. Sai hajiya mama. Bayan ta gaishesu ta nema waje ta zauna duk da ba dukansu suka amsa ba.  

            A gadarance Kawu Ayuba ya fara bayani. “Hasiya basai mun sake ɓata lokacin tisa magana ba. Nasan kema tunda kika ganmu anan kinsan zancen. Kamar yanda su Yaya Ballo sukazo kwanaki akan maganar auren ƴaƴanki da yaran wajen Alhaji Halilu yanzu batun saka rana ne ya tashi. Saboda tsabar halacci da hangen nesa irin nasa yace kawai tunda munzo dubasa a saka. Shi baya wani bukatar ƴan kunji-kunji tunda batun tuwona maina akeyi. To a yanzu haka dai ga kayan saka rana nan ma duk ya saya dan yace shine uban anguna shine na amare, kuma koma bai faɗa ba dama shine, tunda tun suna kananunsu shiketa wahala akansu. Koda kuwa mahaifinsu na raye shine mai bada auren nasu ai dama. Basai na jaki da nisa ba. Yanzu haka dai an yanke ranar aure wata biyu kacal. Batun kayan aure na akwati da kukeyi anan binni duk yace zaiyi baya buƙatar komai da ga yaran nan. Ita kuma Muhibbatu tunda kun saka yarinya ta nuna bata bukatar wannan haɗin, da azo ta bijire bayan auren kota illata yaro kawai za’a fasa. Za’a bata shi wanda ta kawo ɗin ALLAH ya basu zaman lafiya…..”

      A firgice Ummi ta dago ta dubi Abba. Wani shegen murmushi ya sakar mata tare da kashe mata ido ɗaya. Zatai magana yay saurin katseta cikin marairaicewa. “Hakan ai shine yafi kwanciyar hankali Kawu Ayuba. Kaga da alalata zuminci gara dai abi komai a sannu zaifi. Kuma ita mace ce. Banason a cuta mata akan abinda bataso. Dan yarinyace mai hankali da nutsuwa. Duk da damuwar da Junaid ɗin ya shiga nace ya haƙura kawai tunda tana da zaɓinta. Kuma zaɓin nata ma naga mutumin kirkine sunansa Muhammad Shuraim. Ɗan gidan Alhaji Aliyu ne mutumin kirki. Inajin kunyar ma nace bazan bashi jinina ba”.

        Harga ALLAH Ummi ta shiga ruɗani, ta kuma ji ɗan sanyi ta wani fannin. Dan tana mamakin ta yaya shi Abban yasan da zancen zuwan Iyayen Muhammad Shuraim ɗin? Kodai su masu kawo kuɗinne sukai mistake ɗin zuwa nan kawo kuɗin maimakon gidan Sheikh Aliyu Abdul-ra’uff Maina? Lallai akwai abinda bata sani ba. Dan akwai manufa da dalilin yin hakan ga Abba, saboda halin makircinsa da ta sani. Hakanan salin alin bazai hana ɗansa ba ya bama wani………

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button