Uncategorized

TAKUN SAAKA 15

          “Wannan shaiɗancin dai nasan ita ta kitsashi. Duka yarinyar nawa take da tasan wani bijirema zaɓin iyaye. Ni wlhy dan Halilun yace a barta ne da baza’a bari ba. Sai dai idan an aura mata Junaidun ta mutu”. Sababin Kawu Bello ya katse ma Ummi tunaninta.

      Cikin makirci Abba ya amshe da faɗin, “A’a kawu bello ba’ayi hakaba ai. shima wnanan ɗin mutumin kirki ne wlhy. Dan yamafi Junaid nagarta. Muyi fatan ALLAH yasa haka shine yafi alkairi”.

     A take duk ƴan falon suka shiga yabon Abbah da jinjinama ƙoƙarin sa, Ummi kam anata zaginta wai bata da godiyar ALLAH akan ƙoƙarin da Abban keyi tun bayan rasuwar mahaifin su Ammar. Tare da yi mata gugar zana na habaicin asalinta.

     Ita dai uffan batace da su ba. Hasalima hankalinta ya rabune gida biyu. Duk sauran bayanan da suka cigaba dayi sai tama koma bata fahimtar komai. Jinsu kawai dai take da kunne da binsu da ido har aka tashi a taron ko nace suka sallameta. 

       Koda ta fito a sashen taso zuwa gidan malam sai dai gudun abinda zaije ya dawo da fitar tata yasa ta haƙura. Dan haka tai kiran numbar wayar matarsa da yake ƙawarta ce suna zuminci sosai duka biyun. Sai dai tasan uwargidan Maimunatu yanzu haka tana Oman da autan gidan dake karatu acan.

     Bugu biyu Malama Jiddah ta ɗauka. Bayan sun gaisa da ɗan barkwancin ƙawaye Ummi take tambayarta ko Malam na nan kuwa?.

        Malama Jiddah tace, “Eh yana nan, sai dai yana tare da kamar baƙin da naji kunyi magana ranar zasuzo yau ɗin. Lafiya dai ko?”.

        “Tofa, kaji wani kuma ruɗanin. Umm Muhammad! Lafiya dai ba lafiya ba. Akan baƙin dama na kirasa ban samu ba……” (Komai Ummi ta zayyane mata da ya faru yanzun anan gidansu).

         “Bara muga baƙin su wuce to sai na sanar masa. Duk da dai inaji a raina ko duk shine ya tsara hakan dan mijin nan naki sai da siyasa ake iya kamasa a hannu. Ya riga ya zama mai fuska biyu inba ka saniba babu mai cewa zai iya sheɗancin da yake zubawa shi da uwarsa Umm Abubakar. Amma ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, ALLAH yana tare damu”.

        “Shikenan Umm Muhammad ALLAH yay mana jagora. A gaishe da yaran sai na jiki”.

     Sallama sukai da ga haka zuciyar Ummi fal waswasi da saƙe-saƙe.

*__________________*

             Ido Hibbah ta buɗe a ɗan yanayin razana saboda barcin da ya figeta. Gabanta ya faɗi lokacin da idanunta ke kaiwa waje ta windown motar da aka sauke gilashi baki ɗaya. Mazaunin direban ta kalla tana haɗiyar yawu da ƙarfi saboda bushewar da maƙoshinta yayi lokaci guda. Tai saurin ɓalle murfin motar ta fito domin tabbatar ma kanta inda ya kawotan fa ba anguwarsu bane……………✍

*_Tofa. Ina mai taxi ya kai Hibbah?. Wane ruɗanine ya shiga kan Ummi game da kawo kuɗin auren Hibbah da ga gidan su Shuraim? da alama ta nuna tasan da zancen. Shin malam Aliyu Abdul-Ra’uff Maina ne ya fara aika iyayen Shuraim ga Abba kokuwa yaya abin yake ne? Wane shiri Ummi keyi akan yaranta da takejin ƙarfin gwiwar nasarar kubutar dasu ne haka? Minene shirin Abba shima game da fasa bama Junaid ɗansa auren Hibbah ya yarda ya bama Muhammad Shuraim? Shin kodai dama shine ya turosa batare da ita Ummin ta farga ba?. ????tambayoyinfa da yawa. Yayinda ni kaina amsarsu nake nema????????????._*

________________________

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????

#team ZAFAFA BIYAR????????????????????

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button