Uncategorized

TAKUN SAAKA 16

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

_________________________

*_Chapter Sixteen_*

………Da sauri ta dafe kanta da ya sara mata da ƙarfi. Cikin ɗacin murya da zafin da takeji a zuciyarta tace, “Wai nikam mina muku ne na laifi? Dan ALLAH kubar rayuwata ta cigaba da tafiya a yanda take karku sakamin ahali a masifa. Wancan karon kunce dan na bibiyi wanine. Wannan karon kuma mina aikata zaku kawoni nan?”.

            “Duk bani da amsoshin tambayoyin nan naki. Aikina kawai shine ɗakkoki na kawoki nan wajen. Gashi kuma na cika. Amma idan muka shiga da ga ciki harma abinda baki tambaya ba za’a baki amsarsa na sani”.

          A fusace Hibbah ta dubesa zatai magana aka katseta……

      “Gaskiya ya faɗa miki, bashi da amsar da zai baki. Dan haka bismilla ɗiya ta”. Dattijon wancan karon da aka kaita office ɗinsa ya faɗa dai-dai yana ƙarasowa inda suke. Dan tun shigowar taxi ɗin cikin station ɗin yake kallonsu ta window. A fahimtar da yay mata na tsiwa da rashin tsoro da kafiya ya sashi yanke shawarar sakkowa da kansa ƙila tafi jin shakkarsa ta shiga.

     Sai dai kuma ina. Shima a fusace ta kallesa wasu hawaye masu zafi suna sakko mata. Ganin tana motsa  laɓɓanta alamar sonyin magana ya girgiza mata kansa. “Nan ba muhallin da ya dace ki cigaba da cewa komai bane ɗiyata. Ina mai tabbatar miki wannan kiran yasha ban-ban dana farko. Dan kai tsaye ke zai taimaka bamuba Muhibbat. Bakomai yasa nace hakaba sai ƴan uwanki dake gab da shiga haɗari”.

       “Ƴan uwa na?!”.  

Hibbah ta faɗa ƙirjinta na wani harbawa. Uffan jami’in dattijo A.G baice ba ya juya zuwa office ɗinsa. Da sauri tabi bayansa har tana haɗawa da ɗan gudu. Dan ba ƙaramin hargitsa tunaninta maganarsa ta ƙarshe tayi ba. Duk da yanajin tana binsa da gudu bai tsaya ba sai da ya isa har office ɗinsa. Kusan a tare suka shiga da Hibbah. Tai saurin zuwa gabansa ta durƙusa.

       “Uncle dan ALLAH karku cutarmin da ƴan uwa. Ku daina tursasani yi muku abu ta hanyar yimin barazana da su. Kunsan kuwa mi kuka nema haddasama rayuwata a wancan karon? Saura kaɗan na rasa Ummi na, gatana ni da yayuna. Farin cikinmu madubin rayuwarmu. Miyasa kuke son saka alkairi da sharri? Miyasa kuke son yin amfani da ni saboda ku haskaka kanku ma duniya? Miyasa ku ke……..”

        “Ya isa ɗiyata. Duk yanda kike tunani ba haka abin yake ba a wannan gaɓar. Yanda kiɗan ya sauya itama rawar zata sauya ne dole. Inason ki nutsu ki bani dukkan hankalinki nan, domin haɗa hannu wajen tabbatar ma mutanenmu abinda suke ganin bazai yuwu ba saboda rauni da ƙarancin shekaru da suke kallo kai tsaye”.

       “Ni bazan nutsu ba, bazan taɓa nutsuwa ba dan ku taurarine masu wutsiya. Dan ALLAH ku daina saka rayuwata data ahalina cikin *_TAKUN SAƘAR KU_* da bawan ALLAHn nan. Bani da alaƙa da komai nasa kamar yanda kuma bani da alaƙa da ku. Indai harkar computer ce na barta har abada duk da kuwa itace burina, itace mafarki na, itace zummata, itace kaifina. Amma saboda cigaba da rayuwar ahalina cikin salama na tattarata na ajiye. Na manta kaina cikin waɗanda suka iya koda kunnata. Please na roƙeku ku barmin rayuwa data ahali su huta. Ku barni naji da damuwar cikin gidanmu ita kaɗai ta isheni”.

      Yanda ta haɗe hannaye tana roƙonsa hawaye na kwarara a kumatunta duk sai tausayinta mai tsanani ya kamashi. Idanunsa suka kaɗa sukai jajur. Kansa ya shiga girgiza mata yana ƙoƙarin kamo hannayenta dake haɗe har yanzu waje guda alamar rokonsa????????. Sai dai yana kawo hannu ita tai azamar jan nata baya. 

        Da sauri yace, “Shike nan naji zan barki ki tafi. Amma ki tabbatar Tabbas kinada alaƙa da Master Muhibbat, saboda wannnan ɗin kasarki ce, kuma a ƙasar taki yake aikata dukkan ɓarnarsa. Sannan rayuwar yayunki da mamanki na cikin haɗari a hannun ƙanin mahaifinku da shi wanda kike ganin baki da alaƙar komi da shi. 1Mu kaɗai ne kawai kuma zamu iya cetosu tare da ke kanki. Zakuma muyi hakanne kawai idan kin amince kin yarda zaki cigaba da mana aiki akan mutumin nan Master. Idan kuma bazakiyi ba zaki iya tafiya kawai”.

       Shiru Hibbah tai tana kallonsa. Kallo mai cike da ma’anoni da yawa da ita kanta ko ca’akai ta fassarasu bazata iya ba. Kansa ya jinjina mata alamar tabbatarwa.

      Sosai zuciyar Hibbah ke ƙara wani irin lugude, babu abinda ke mata kai kawo a zuciya sai batun auren yayunta da ƴaƴan Abba. Dama har cikin ranta tanaji akwai manufa, amma batasan miyasa Ummi ta amince ba bayan kuma ta sanar mata yayun nata nada waɗanda suke so. Wani tunani da yazo mata daban a cikin rai ya sakata kai hannu kawai taja kujera ta zauna tana share hawayenta da suka kasa tsayawa. Shima sai ya sauke ajiyar zuciya da takawa wajen kujerar zamansa ta office ɗin ya zauna yana fiskantarta.

          “Miyasa sai ni kaɗai ce zan muku aikin? Bayan nasan akwai mutane da yawa masana kuma jajirtattu akan wannan harkar, waɗanda idan a gabansu nake ni ɗin bakomai bace, bansan kuma komaiba?”.

           “Tunani mai ƙyau Muhibbat. Tambayarki na da matuƙar muhummanci kuma ta birgeni. Har cikin raina na sake yarda zaki iya domin kina da kaifin ƙwaƙwalwa. Kafin kiyi mana wancan aikin tunanina irin nasune, ina kallon raunin mace matuƙa nima. Ko a cikin hukumar nan aka bama mace aiki raina kan ɓaci naga babu abinda zata iya. Amma sai ke kika ruguza dukan wannan tunanin nawa a waccan ranar, dan kinyi abinda ƙwararru da yawa suka kasa matsayinki na mace mai ƙarancin shekaru kuma ɗaliba da iya ƙasarta kawai ta samu ilimin kimiya da fasaha. Na zauna nayi dogon nazarin da yasa na fahimci irinku ba’a sakaci da al’amarinku, dan da irinku ƙasashen turawa suka cigaba a nasu ƙasashen da suke birgemu a yau. Muhibbat na miki alƙawarin wannan aikin ƙashin kanki zakiyi. wanda dole duniya tasan da zamanki bayan kammaluwar komai insha ALLAHU. Inason barinma bayana alkairi bayan na ajiye aiki, kuma kece wanan alkairin da nake fatan bari insha ALLAH. Da kuma wanan damar zakiyi amfani kema wajen ceto ahalinki da sake darajasu cikinƴan uwanku, ki wanke baƙin fentin da ƙanin mahaifinku da kakarku sukai muku wanka da shi. Da wanan damar zaki canja masu irin tunanina game da ɗiya mace”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button