TAKUN SAAKA 16

Murmushi Hibbah ta saki wanda ita kaɗai tasan ma’anar kayanta. Ta ɗan muskuta zamanta da faɗin, “Na amince zan muku aiki, sai dai ku sani hakan ba yana nufin idan baku sami nasarar kamashi ba zan cigaba da dawowa nan wajen. Zan muku abinda kuke buƙata ko ba’a sami nasara ba nima zaku kuɓutarmin da ahalina”.
“Tabbas mun amince, harma da wata gagarumar ƙyauta da zaki samu inhar yazo hannun namu.”
“Yallaɓai na bar muku ƙyautar basai kun bani ba. abinda kawai nakeso shine ranar auren yayuna ana gab da halartar ɗaurin aure ku kama Abba ku ɓoye min har sai an kammala ɗaura auren yayuna da matan da suke so da kwanaki biyu. Abu na ƙarshe kuma inason amin cikakken bincike akan Muhammad Shuraim da Abba ya iya hana ɗansa ya yarda na auresa duk da zaɓin Ummi na ne shi”.
“Duk mun amince da sharaɗinki”.
Murmushi Hibbah ta saki a karo na biyu. “Inhar ya kasance Muhammad Shuraim bashi da wani aibu a rayuwarsa zan auresa na rayu da shi matsayin miji kodan son da Ummi na da Yayuna ke masa. Zanbi duk hanyar da zanbi na ganin ya ɗaukeni zuwa ƙasar China yin karatuna akan ilimin kimiya da fasaha. Ni kuma a wannan lokacin zan muku aiki. Ko wanene wanan master ɗin nayi alkawarin insha ALLAH sai na zama sanadin da zaku kamashi a tafin hannunku. Dan haka na baku dama kafin kwanakin aurenmu 60 da aka saka nasan wanene Muhammad Shuraim ciki da bai. A samama ahalina waje na musamman da zasu rayu a lokacin da zan fara farautar MASTER. Dan ko ƙwarzane bana son ya samu koda farcinan hannunsu”.
Wani irin tattausan murmushi dattijo A.G ya saki, yayma Hibbah jinjina. “Tun a ranar farko da kikazo nan na tabbatar zaki iya a cikin idanunki, tabbas zaki iya. Kuma insha ALLAH dukkanin bukatunki zasu biya Muhibbat, daga ƙarshe ƙyautar dana ambata zata kasance biya miki kuɗaɗen tafiya ƙasar China ko wata ƙasa daban yin karatunki. Abinda kawai zakiyi shine neman yardar mijinki”.
A take wani irin farin ciki ya baibaye Hibbah. Ta ɗaga hannu tana addu’ar godiya ga UBANGIJI da fatan nasara akan alƙawarinta.
Shiko dattijo A.G na tayata da amin. Sai da ta sauke hannayenta sannan ya tura mata takarda da pen.
Ki rubutamin dukkan sunayen ƴan gidanku da duk wanda kike tunanin kawo tangarɗa akan auren yayunki anan”.
Takardar ta jawo gabanta tana wani irin dariyar ƙeta. Dan babu wanda take hangowa a idanunta sai Hajiya Mama da su Kawu Hannafi. Bayan ta gama zana masa ya bata wata bag dake ɗauke da tarin files da suka shafi Master. Ya ɗora da gargaɗinta akan muhimmancin riƙe musu sirrinsu.
“Dukkan abinda zaki buƙata da ya shafesa na tanadar miki anan, dole ne sai kin fara shiga kansa, kinyi irin tunaninsa. Ke mace ce, kuma ƙaramar yarinya. Inaji a jikina kafin ya ganoki ko ya farga da ke kin kammala aikin nan insha ALLAH. Kisa a ranki ALLAH na tare da ke, kuma duk inda kika shiga akwai jami’an dana tanada zasu dinga bibiyarki ke da ƴan uwanki domin baku kariya.”
Kai kawai Hibbah ta jinjina masa. Da ga haka ta fito mai taxi ɗin da ya kawota station ɗin ya sake ɗaukarta domin maidata gida.
★★
Kamar yanda Hibbah tai fata koda ta shigo gidan nasu bata sami kowa a falo ba, yayunta babu wanda ya shigo, Ummi kuma tana ɗakinta. Ɗaki ta wuce ta adana bag ɗin da tazo da ita sannan ta fito ta sanarma Ummi ta dawo.
Sosai Ummi ke binta da kallon mamaki ganin tanata washe haƙora kamar ba itace ta fita da ɓacin ran zancen aurensu ba. Komai Ummi batace mata ba akan walwalar tata. Sai ma ce mata da tai idan ta gama taje tai mata list na kayan kwalliya da kayan underwears.
Cike da zumuɗi Hibbah ta fice dan tasan na kayan lefen yayunta ne da za’a haɗa a gidan Sheikh Aliyu Abdul-Ra’uff Maina. A gurgije tai wanka ta kimtsa kanta. Ko abinci bata nema ba duk da yunwa da ciwon kan da ke damunta har yanzun, tai zaman rubuta list ɗin bayan ta kunna wayarta ta shiga WhatsApp ɗinta tana bugar cikin Hafsat da Zahidah akan kalo da sayis ɗinsu.
Cikin awa ɗaya ta kammala komai ta fito ɗauke da takardar. Kai tsaye ɗakin Ummi takai ta ajiye sannan ta fito wajen yayunta suka cigaba da hira. Su kansu sunyi mamakin ganin yanda taketa faman walwala tamkar yanda suka santa tun fil’azal. Sai dai komai basuce mata ba suma.
*________________________*
Kwana uku da faruwar haka Muhammad Shuraim yazo gidan su Hibbah a karon farko. Ya sami ƙyaƙyƙyawar tarba da ga wajen su Yaya Umar, inda aka saukesa ƙaramin falonsu da Dadynsu kan sauke baƙi kafin rasuwarsa.
Da farko Hibbah catai ita bata gayyatarsa, dan haka bazataje ba. Sai da Ummi tai mata jan ido sanann ta zumbula hijjab ta fita ɗauke da karamin tire da aka ɗora ruwa.
Tunda ta shigo da sallama ya kafeta da idanunsa manya da ke neman rikitata. Tiren ta ajiye saman Centre table ɗin falon tana harararsa da kumbura fuska.
“Malam lafiya?”.
Ta faɗa cike da tsiwa.
Kansa ya ɗan girgiza kawai yana lumshe idanunsa dake a kanta ya sake buɗewa. “Ina tausayin bakin nan naki saboda tsiwansa, amma babu komai lokaci kaɗan ya rage ya daina”.
Baki ta taɓe da kaiwa zaune cikin kujera tana faɗin, “Karka ɗauka maganin da kaima iyayena suka yarda da kai lokaci guda nima ya cini. Wasu dalilai ne kawai sukasa na yarda da aurenka badan kayi dai-dai da ra’ayin mijin da naima kaina buri ba”.
“A hakanma na gode. Na kuma sake tabbatar da cewa nazo inda ya dace neman aure. Dan biyayyar da kikai ga iyayenki kawai cikakkiyar amsace akan nagartaciyar tarbiyyar da kika samu da ga garesu mai inganci.”
“Humm” kawai Hibbah ta faɗa batare da tace komai ba.
Shuraim ya murmusa batare da ya nuna damuwa da yanayin nata ba. “Kamar yanda na faɗa miki sunana Muhammad Shuraim Aliyu. A garin nan aka haifeni, anan na tashi, anan na girma, anan nai karatun addini dana boko har zuwa secondary. Kafin na ƙetare wajen ƙasar nayo karatun jami’a har zuwa matakin degree na biyu. A yanzu haka ina akan haɗa degree na na uku tare da harkar kasuwanci tamkar yanda na taso na gani anayi a gidan mu. Abinda ban faɗa miki ba bayan wannan kuma na baki damar yin bincike a kaina dan ki sani. Ƙwarai da gaske naji daɗi matuƙa na samunki musamman da ya kasance ban zaci hakan ba. Abinda zance kawai kiyi haƙuri banyi kamar yanda samarin wannan zamanin keyiba na fara shimfiɗa soyayya kafin aure. Ni sam hakan ba ra’ayina bane ba, shiyyasa tun farko ban taɓa zuwa ƙofar gidanku ba kai tsaye sai dai bibiyarki kawai. A randa kuma iyayena sukazo domin neman izinin zuwa zance gunki sai akace anma bani ke, dan ƙa’idarku ku ba’a barinku dama yin zance. Nagode ƙwarai da gaske Muhibbat. Ina fatan zaki amsheni da hannu biyu batare da tunanin nayi miki kutse cikin rayuwarki ba?”.