TAKUN SAAKA 38

Abbah dake a birkice ya sake rikice musu akan shi baya buƙatar kowa tare da shi, kuma lafiyarsa lau doctor bai isa yay masa allura ba shi kawai su kira masa Master ya bashi kuɗinsa. Su Hajiya mama da basu fahimci ainahin alaƙar Abban da Master ɗin ba tuni suka sake aminta Abban ya zare da gaske. Dan haka suka bada goyon bayan ai masa allurar musamman ma da ƙafarsa mai karaya ta sake gocewa.
A ɓangaren su Alhajin Mande kuwa duk da ƴan jaridu sun ishesu da yawan tambayoyi musamman akan sakin videon Master harma da jami’an tsaro yasasu killace kansu waje na musamman sunata tattaunawa akan al’amarin na master mai matuƙar ban mamaki da firgici. Duk abinda A.G keyi kuwa da yawunsu. Sun bada ɓoyayyun sirrika na inda Master ke zama wa jami’an tsaro cikin ɓaddabamin cewar binciken su A.G ne ya gano hakan.
Bayan kammala meeting jami’an suka rarraba kawunansu a hanyoyin da duk ake tunanin za’a iya kama master, tare da bin diddigin abubuwansa da dama da su A.G ɗin suke tunanin sun sani…..
★★★★★★★
Ba ƙaramin azaba Hibbah taci a hannun master ba, tayi kuka har muryarta ya dishe, tun tana gane da yaren da yake tare da ita harta bar fahimtarsa komai ta koma a halin gushewar ji da gani harma da ɗaukewar numfashi. bama ita ba shi kansa ya jigatu dan sam hankalinsa baya tare da shi, baima san a yanda ya wajiga rayuwar Hibbah ɗin ba sai da ya cimma burin abinda bai taɓa tunanin amsa ba a yanzu, kodan halin mutuniyar tasa. Babu abinda yake sai sauke ajiyar zuciya a jajjere, a karon farko na rayuwarsa ya mallaki abu mai daraja da ada sam baya sakashi a lissafinsa. Bai taɓa tunanin zaiyi aure nan kusa a rayuwarsa ba, sai gashi Hibbah ta canja dukkan lissafinsa. Ita ɗin ta zama ta musamman, a lokaci na musamman, ga ahali na musamman da suka kutso cikin ƙaddararsa ta dalilinta. Sake rungumota yay jikinsa da kyau ganin yanda jikinta ke karkarwa haƙoranta na haɗuwa waje guda tamkar maijin sanyi, ji yake tamkar ya tsaga fatarsa ya tura ciki. Cikin dasashshiyar muryarsa mai gauraye da mura da azabar wahalar da yasha kafin mallakarta yake magana a kunnenta hawayenta masu ɗumi na sauka bisa ƙirjinsa, “I’m sorry autan Ummi, ki yafema yaya isma’il ɗinki uhyim”.
Duk da halin da take a ciki na azabar raɗaɗi da jigata ga tashin hankali da tsananin damuwar rabata da budurcinta da yay sai da taji zuciyarta ta tsarga jin ya ambaci kansa da Isma’il. Tana son ɗagowa ta sake kallonsa dan tabbatarwa tsananin kunya da jigata ta hanata hakan. Sai wasu hawaye ne masu ɗumi da suka sake ziraromata suna sauka a kan jikinsa. Idanunsa dake a rufe ya buɗe a hankali jin sabbin ɗumin hawayen nata. Yay ƙoƙarin ɗago kanta dake a jikinsa amma taƙi yarda. Rashin ƙarfin dake tattare da jikinta ya bashi damar ɗagotan duk da shima jikin nasa babu ƙarfi ga shi da ciwuka ga mura. Fuskarta kawai ya tsurama idanunsa yana kallon yanda take shaƙar zuciya tamkar zata suƙe. Ga idanunta da ke rufe duk sun kumbura. Hannunta ya kamo ya ɗaura akan fuskarsa ya danne da nasa batare da yace komai ba. Sai dai har ƙarƙashin zuciyarsa yanajin kukanta na sukarsa. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da sumbatar goshinta da hancinta ya dire laɓɓansa saman nata da sukaci matuƙar wahala a hannunsa sai zogi suke mata.
Sabuwar rawa jikinta ya ɗauka. Ta fashe masa da kuka tana mutsu-mutsun son matsawa da ga jikinsa. Dan duk zatonta zai sake ne kuma. Tausayinta da dariya suka riskesa a lokaci guda. Amma sai yadake baiyiba ya cigaba da abinda yakeyi dan kawai yaga yazatayi.
Ganin yanda take juya kai da son ja baya ne ya sashi sakin bakin nata. Tanaji an saketa ta saki kukan da take riƙewa mai sauti. Cikin wahalalliyar murya ta fara roƙonsa. “Dan ALLAH, dan ALLAH kayi haƙuri wlhy zan mutu, ka kaini wajen Ummina”.
Cikin ɗan murmushin daya kufce masa babu shiri, da disashshiyar muryarsa ya ce, “Sai naga kin daina rashin ji”. Yay maganar yana son tashi ya ɗan ranƙwafo kanta yanda yake iya ganin fuskarta data juyar da kyau. Ganin yanda taja bargo ta rufe har fuskartane ya sashi sake sakin murmushin. Sauka yay a gadon cikin dauriyar rashin ƙarfin jiki dan har lokacin sallar azhar ya gota sosai. Toilet ya nufa kai tsaye, ya gyara jikinsa a gurguje ya fito. Shashashar kukan Hibbah da ke tashi a hankali a ɗakin ya bashi tabbacin kuka take har yanzun. Yafasan yau ya taɓoma kansa jangwam, dama yaya lafiyar giwa.
Jallabiya ya zura a jikinsa kawai ya ɗan saka turare ya tada salla yana kauda tunanin dake ta masa kai kawo a rai tun bayan samun kansa da ga shan shayi. Lallai yau sai yaci ƙaniyar su Habib gwargwadon iko dan baya raba ɗayan biyu wani abu suka zuba a shayin daya kawo masa. Shidai lafiyar ALLAH ya tashi duk da kuwa a shekarunsa ya jima yana bukatar abokiyar halittarsa. Sai dai shi mutum ne da hidimomin kansa kansa ya kasance busy har damuwar bata tasiri mai nisa a garesa. Yana kuma ƙoƙarin ganin ya kiyaye idanunsa da kunnuwansa da ga dukkan abinda zai iya motsa masa sha’awa. Idan kuma yaji ya takura sosai ko baida aikinyi sai ya ƙirkirarma kansa dan gudun faɗawa tarkon saɓon ALLAH.
Sallarsa ya gabatar a nutse bayan ya tattara tunanin ya tureshi gefe. Koda ya idar zaune yay a wajen yana addu’a da jiran lokacin sallar la’asar ya ƙarasa dan yaji Hibbah shiru da alama barcin wahala ya ɗauketa. Kansa na masa ciwo sosai, harma yanajin wani zazzaɓi tare da shi, ga jikinsa sam babu wani ƙarfi zuwa yanzun, har ɗan jiri-jiri yakeji cikin idanunsa amma duk ya dake ya shanye dan yasan Hibbah duk ta ninka wannan wahalar tasa. Duk da rakin da taketa masa yaga dauriyarta, a yanda ya rutsatan ba cikin hayyacin nan nasa ba.
Koda lokacin sallar la’asar ɗin ma ya karasa a ɗakin yayita. Dan baya buƙatar su Habib su gansa a haka. Tunanin ta yanda zai bama Hibbah taimako ne ya sashi ture hukuncin da yake shiryama su Habib ɗin a ransa. Ganin ya rasa mizai hasaso ya sakashi tashi cikin dauriya ya koma bakin gadon ya zauna. Wayarsa da baisan a ina take ba ya shiga duddubawa a gadon. Da ƙyar ya samota ta shige tsakanin jikin gado da katifa. Sai da yay ɗan shiru alamar tunanin ta ina zai fara saboda sanin halin iya shegen aminin nasa. Bazai sake kirasa ba. dan yasan a muryarsa kaɗai zai iya gano halin da yake ciki tunda shiɗin ba kanwar lasa bane, ɗazun ma ba karamin sheri yay masa ba, dan shi ya fargar da shi cewar kodai wani abu yasha ma. Sanin iya shegen Abdull ɗin ne ya sashi yanke hukuncin tura masa massege kawai.
Yana tura saƙon ya matsa kusa da fuskar Hibbah ya janye bargon. Sosai jikinta yay masifar ɗaukar zafi har numfashinta kansa ya canja alamar akwai damuwa. Duk da shima jikin nasa akwai zazzaɓi sai ya samu nata ya shanye nasan dan zafi sosai. Shigowar saƙo ya sashi janye hannunsa dake a saman goshinta ya ɗauka ya duba. Abdull ɗinne kuwa tamkar yanda yay hasashe sai dai tambayar daya turo masa ta shaƙiyanci maimakon amsar daya nema ta sakashi jan tsaki yana harar wayar tamkar Abdull ɗinne a gabansa.