TAKUN SAAKA 8

A sakawa ɗaya kuwa ƙofar ta buɗe. kusan rabi a cikinsu suka shiga ciki akabar wasu a waje. Akan idon mai-gadi suka shiga hargitsa gidan tako ina. Sai dai abin mamaki babu wani alamun abun rashin gaskiya da sukayi gamo da shi. Cikin glass ɗin nan da computers ke ciki ɗazun yanzu babu shi, sai wasu ƙayatattun flowers masu ɗaukar hankali da ƙamshinsu ya cika falon.
“Tabbas yarinyar nan ƙarya take mana. Ko tana ɗaya da ga cikinsu ne yawo da hankalinmu kawai take son yi”. Ɗaya daga cikin jami’an ya faɗa a hasale.
“Sam banajin hakan a raina, akwai dai wani ɓoyayyen abunda bamu sani ba. Karku manta shiɗin mutum ne mai matuƙar wayo da dabaru kala-kala. Tabbas ya fahimci ana bibiyarsa ne ya bada ƙafa. Kokuma yayi amfani da wanann location ɗin domin sakamu zargi.”
“Nima zuciyata tafi rayamin hakan yallaɓai”. Wani ma ya sake faɗa cikin jin zafi.
“Karku samu damuwa. ai rana 99 da tara na ɓarawo, ɗaya tak na mai kaya. Inhar kere na yawo, zabo na yawo watarana dole a gamu. Tunda yace shi hatsabibi ne ya samu dai-dai da shi kuwa. Zamu bar wasu a gidan nan har sai mun tabbatar da gaskiyar babu wani abun zargi a cikinsa”.
Duk sun amsa da girmamawa. Shi dai mai-gadi kallonsu kawai yake yana kwasar dariya a zuciyarsa. Koda suka fito harabar gidan sun tsara wanɗanda za’a bari, wanda zasu koma kuma suka nufi hanyar barin gidan. Karaf idon ɗaya ya sauka akan bag dake rataye acan ƙarshen gate ɗin gidan ta waje. Saurin zuwa yay ya ɗakko yana nuna musu. Commander ɗin operation ɗin nasu ya amsa yana zazzage jakkar cikin kulawa gudun kar a saka musu bom a ciki.
Agogon Hibbah ne ya fara faɗowa tare da takarda mai ɗauke da sunansa akoda yaushe da facemark. Sai ɗan gajeren rubutu a bayan takardar.
*_“Bibiyata na nufin ƙare rayuwarku a wahala. Inhar bani naso kusan niɗin wanene ba, bazaku taɓa ganoni da kanku ba har abada insha ALLAHU rabbi. Dan haka ku daina azabtar da kanku wajen bibiyata komai yana da lokacinsa”_*
_Master????????_
Wani wawan tsaki jami’in daya gama karanta takardar yaja. Ya cije leɓensa na ƙasa da ƙarfi, cikin alwashi yace, “Ni kuma na maka alƙawarin da wannan hannun nawa zan kamaka, sannan na maka horo mai tsananin gaske wanda sai ka gwammaci mutuwarka da rayuwarka shaiɗani”.
Suma sauran zukatansu na matukar ƙuna suka ɗauki nasu alwashin…..
___________★★★__________
Yaya Abubakar ya shiga tashin hankali matuƙa lokacin da yake isowa cikin makarantar su Hibbah yaji abinda ya faru a bakin Ammar da Zahidah. Tare da samun ƙarin bayani a bakunan wasu ɗaliban.
Da taimakon wani malamin su Hibbah ya shiga Computers room nasu yay bincike a computer ɗin da ta gudanar da binciken. Sai dai kuma ta saka security, shiga yay gwada passwords kala-kala yayi wanda yasan tana amfani da su a gida ko zata iya amfani da su. Sai dai sam babu wanda ya buɗe. Cike da ɓacin rai ya mike yana bugar desk ɗin cikin ƙunar zuciya. Lalubo wayarsa da ke ring a aljihu yayi. Yaya Muhammad ne, ɗagawa yay sukai yar magana ya yanke. Wani abokinsa ya kira kasancewar shi jami’i ne a hukumar ƴan sandan ta farin kaya. Ya tabbatar shine kawai zai iya bincika masa idan Hibbah na hukumar tasu. Bayan ya ɗaga ko gaisuwar kirki ba suyi ba ya sanar masa bukatarsa. A take jami’in ya tabbatar masa lallai Hibbah na’a headquarters ɗin tasu dan yaji ƙishin-ƙishin ɗin zancen yanzu a bakin wani ogansu cewar akwai yarinya da ke da alƙa da case ɗin na jiya.
Yanke wayar kawai yayi batare da sun ƙarasa maganar tasu ba, ya kira Yaya Muhammad yana sanar masa a inda zasu haɗu yanzun nan……
__________________________
Master da yaransa kam bayan ƴar tafiyar da sukayi ta cikin hanyar kwata sai gasu sun ɓilla ta wani ƙaramin gida. Gidane ginanne mai ƙyau na dai-dai mai matsakaicin ƙarfi. Yanda yake bin ko ina cike da nazari haka suma suke kallon gidan. Bayan kamar mintuna biyu ya gyara tsaiwarsa sosai yana fuskantarsu. Binsu ya gamayi da kallo ɗaya bayan ɗaya batare da su suna kallon ko ƙwayar idonsa ba. Tabbas sun jima suna kwaɗayin ganin fuskarsa, amma sam yaƙi basu damar hakan koda da kuskure..
_Gyaran muryar da yay ne ya katse tunaninsu. Ya sake gyara tsaiwarsa yana tura hannayensa duka cikin aljihun wandonsa. Muryarsa a kausashe da tabbatar musu da fushinsa ya fara magana cike da nutsuwa da ƙasaitar sa,
“Yau mun tsallake rijiya da baya, amma wataran saboda sakacinku tabbas bazamu tsallake ba. A kullum ina faɗa muku duk sanda zakuyi aiki, ku ringa yinsa da *_ƘWAƘWALWA DA ZUCIYA_* a haɗe. Dan duk lokacin da ɗan adam yay amfani da ƙwaƙwalwa kawai wajenin aikata muhimman abubuwa to ya tabbatar zai kasance mai yawan shiga ruɗani da tafiya yana dawowa baya saboda wani ya fika kaifin basirar. Idan ko da zuciya kaɗai ka dogara wajen ginin muhimman abubuwa, kasani nasararka ragaggiyace saboda zuciya abinda ke mata daɗi kawai take ayyanawa da buƙatar ya kasance mata. Bai kuma zama lallai ka kasance cikin jin daɗi da farin ciki ba a kowanne daƙiƙa na rayuwarka. Dan wani lokacin hanyar jin daɗi wahala ce, wata hanyar wahalar kuma jin daɗi ce. Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe, idan ba hakaba ni ɗin nan da kaina zan bada ƙafar da za’a kama duk wanda ya cigaba da sakaci a cikinku. Ba kuma zan taɓa kuɓutar da shi ba har sai ya jigata yasan muhimmancin bama kasan kariyar yin aiki cikin tsantseni. Duk wanda ya haremu ya sokemu akan dai-dai kuma na jinjinama ƙwaƙwalwarsa da kaifin tunani. Sai dai na baku awa goma kacal ku ganomin koshi ɗin ɗan gidan uban wanene. Dan sai ya amshi hukunci dai-dai da iyawarsa!”_.
“Insha ALLAHU zamu kiyaye sir. Muna kuma neman afuwa daga gareka”. Suka faɗa a tare cike da girmamawa a garesa. Yayinda Habib da yasan komai ya farune ta sanadinsa yay ƙasa da kansa bayan ya sake matsowa gabansa. “Ka gafarceni Master, dan wannan tabbas sakaci na ne. Amma wlhy sam bansan ta yaya akai hakan ta kasance ba. Sannan koda muka dawo kuma ban fargaba.”
Hannu kawai ya ɗaga masa batare da yayi magana ba. Sai kuma ya nufi ƙofar fita da ga gidan baki ɗaya. Da kallo duk suka bisa har ya isa ƙofar ya buɗe sannan ya juyo yana kallonsu shima.
“Zan sake maimaita muku awa goma kacal, na samu cikakken labarin akan ko shiɗin wanene!……” Daga haka ya ida ficewa baki ɗaya.
A tare suka sauke ajiyar zuciya. Sun tabbatar a salon da yay maganar babu wasa a cikinta, dama can kuma ba wasan ya ke musu ba ballema su ɗauketa wasa. Suma kuma har cikin ransu suna bukatar sanin wanene wanda yay musu wannan tarkon da suka tsallake rijiya da baya?……….✍
*_Gadai jami’an tsaro basu sami nasarar aikin Hibbah ba, ga kuma Master ya bada awanni goma domin binciko wanda ya haresu, hibbah dai kuma itace ta kai harin da babu niyyar dalilin da su suke kallo. To yaya zata kasance kenan tsakanin Muhibbat Aliyu Hamza da Jami’an ƴan sanda da Master kenan?????. TAKUN SAAƘA wasa farin girki????????_*
*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*