TAKUN SAKA 21
*_Typing????_**_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
_________________________
*_Chapter Twenty one_*
…………A matuƙar hargitse Abba ya samu gidan, da ƙyar ya iya kutsa kai ya isa ga su Hajiya mama da Garba kema bayanin yanda akayi. Saboda labarin yanda ɗaurin auren ya kasance na faruwa Hajiya mama ta nufi sashen Ummi a hargitse zata fara zubar da tujara Garban ya dakatar da su.
“Sam ba laifin Asiya bane. Dan a wannan gaɓar tafi kowa cancantar aima jaje, a kuma tausaya mata.”
A fusace Hajiya mama ta juyi garesa kasancewar ɗa ne a gareta. dan kuwa ɗan ƙanwarta ne. “Garba har yaushe kasan makircin Asiya? da shaiɗancinta da zakayi ƙoƙarin kareta akan abinda yake zahiri. Ni dama nasan shurun da tai da yarda da wannan auren bana arziƙi baneba. To wlhy yau ɗin nan……”
“Inna ku saurareni”. Garba ya katse hajiya mama. A dai-dai lokacin kuma Abba ya iso da ƙyar garesu, dan illahirin ƙafarsa rawa ma take tamkar karayar tasa na neman dawowa sabuwa ne.
Garba ya cigaba da faɗin, “Sam ba laifin Asiya bane. Dan ba kowa ne ya canja ɗaurin auren nan ba sai shi yaron da ya auri ita Muhhibatu.
Cikin matuƙar mamaki hajiya mama ta ce,“Shi Shuraim ɗinne ya canja ɗaurin auren? To a dalilin mi zaiyi hakan?”.
“Wlhy Inna nima ban saniba. Sai dai gaskiya kunyi ganganci haɗa auren yarinyar nan da yaron. Dan hatsabibin mutumne fiye da hasashen mai hankali. Na tabbatar da hakan da idanun. Shine ya hanani kiran Yaya Halilu. Ya tsaramin abinda naje na sanarma Sheikh Aliy. Ya tsoratani da inhar banyi yanda yake so ba zai kasheni. Ya nunamin mutanensa da ke a kowace kusurwa na cikin massallacin, wanda alama kawai zai musu numfashin duk wanda ke cikin massallacin ya dakata da aiki. Na tsorata matuƙa, dan nasan zai iya aikata abinda yafi haka. Mutumin daya iya zuwa muku da fuskar mutanen kirki ya yaudareku sai kasheni zai gagaresa. Hakanne ya sani bin umarninsa naje na faɗama malam yanda yace. Wlhy ban sake kiɗima ba sai da na tsugunna gaban malam ina faɗa masa wani yaro dake gefen malam ɗin ya ɗoramin bindika akan ciki batare da kowa a cikinku ya lura ba. Tayaya kuke tunanin zan iya ƙin bin umarninsa.”
Yaya Abubakar da zukatansu ke neman faso ƙirazansu su fito a rikice yace, “Uncle Garba kace shine Shuraim?”.
“Abubakar wlhy shine Shuraim, na tabbatar da shi kuka ɗaurama ita wannan yarinyar Muhibbatu aure”.
Ai gaba ɗaya wajen ya sake ruɗewa. Ummi tai baya zata faɗi sai da Hajiya Mardiyya ta tarota. Abba kam wata mummunar hajijiyar ruɗani ce ke neman zubar da shi shima. Yayinda wani tsoro-tsoro firgici-firgici ya sashi fara waige-waige tamkar Shuraim ɗin na tare da su a wajen.. Abinda bai ganeba anan, miyasa Shuraim zai dakatar da ɗaurin auren ƴaƴansa da su Usman? Tunda gashi ya cika umarnin aikin auren ita Muhhibat?. Wayarsa ya shiga lalube yana ƙoƙarin fita a wajen.
A.G ya kira, wanda sai da tana gab da tsinkewa ya ɗaga cikin ɓacin rai. “Malam miye kuma na kiran….?”
Katseshi Abba yay da faɗin, “Ko kasan Master ne ya rusa ɗaurin auren ƴaƴana bayan shi an ɗaura nasa da yarinyar nan”.
Cikin taɓe baki A.G yace, “To kai mi kake tunani? Kasan dai shi baya abu da ka, zata iya yuwuwa akwai dalilinsa nayin hakan, dan kawai ya bada ƙafa kamar yanda ya saba”.
“Ina ba haka banee!!”.
Abbah da ke a birkice ya faɗa cikin matsananciyar tsawa.
“Ya kake min ihu haka ne? Alhaji Halilu?”.
“Ya bazan maka Ihu ba bayan kai ne ka tsara komai…..”
“Muka dai tsara, tunda komai da yardarka akayi, a kuma gabanka bawai a boye ba.”
Abba ya buɗe baki zaiyi magana A.G ya katsesa da faɗin,
“Kaga ina zuwa gashi ana kirana da ga office. Zan kiraka”. Bai jira cewar Abba ba ya yanke kiran dan ogansa ne ke kiran nasa, da alama tsiyar da Master ya tafka harta fito kenan. Wani irin ƙarajin baƙin ciki Abba ya saki shi kaɗai a ɗakinsa, ji yake tamkar ya rotsa wayar tasa da ƙasa kawai ya huta. Jikinsa kansa ta ko’ina rawa yake da tsatstsafo da zufa, kansa ya kulle ya kasa fahimtar komai game da abinda Master ya aikata.
Hargitsewar gidan yasa babu wanda ya farga da rashin Hibbah. Dan ita kanta Ummi ƴaƴanta nacan zagaye da ita kowa nason ganin hankalinta ya dawo jikinta. Yayinda acan tsakar gida Hajiya mama ke doka rantsuwa tana direwa akan sam bata yarda ba wanann shirin Ummi ne da ƴaƴanta. Tabbas sune suka saka Shuraim ɗin yayi haka. Da yawan mutane maganar Hajiya maman tayi tasiri a garesu, musamman da ya kasance alaƙar Hibbah da Shuraim ɗin kawai kowa ke kallo a zahiri da kuma ɗaura auren su Yaya Muhammad da wasu matan daban alhalin su su Hajiya mama basu san da zancen ba sai yanzu da aka ɗaura.
Gidan ya ruɗe sai cece kuce ke tashi ta ko ina. Kowa na faɗin albarkacin bakinsa da hasashen zuciyarsa.
Cikin ƙarfin hali Ummi da tun fara tujarar Hajiya Mama yaranta suka kamata suka shige ciki da ita ganin yanda duk suka tattara kansu gareta ta haɗiye tashin hankalinta da ruɗani tana mai duban su Yaya Usman ɗin da su kansu bawai suna cikin cikakken hankalinsu bane akan al’amarin. Kan Yaya Abubakar da ke kusa da ita ta dafa tana murmushi. “Har yanzu zuciyata ta kasa daina yimasa ƙyaƙyƙyawan zato. Dukkanin cikamakin kamala da mutunci a bayyane suke garesa, shiyyasa nai saurin aminta da aura masa Tanee. Amma ta yaya fari zai koma baƙi a wanan ranar?, bayan har yanzu idanuna da zuciyata sun ƙi kallon komai da baƙin”.
Cikin taraddadi da jan gwauron numfashi Yaya Abubakar yace, “Dama nasan hatsabibin nan bazai ƙyale Hibbah ba. Dan ta masa tabo irin wanda bazai gogu a cikin tarihinsa ba. Hakan yasani yarda da amincewar aima ta aure ko zata kuɓuta daga garesa. Ashe mun riga mun daɗe da kasancewa cikin lissafinsa, ko tantama banayi akan lallai shu’umin nan Master ne yazo mana da fuskar Shuraim. Sai dai ina mamaki matuƙa ta yanda ya kuɓutar da mu daga auren waɗan nan yaran. Mi hakan ke nufi ne?”.
Ammar ya ɗago kansa da ga ɗorawar da yay bisa cinyar Ummi a firgice yana faɗin, “Yayamu Master fa kace? Gawurtaccen ɓarawon da kuke nema ruwa a jallo ko wa? Danni ban gane ba”.
Numfashi yaya Abubakar ya fusga da ƙarfi yana jinjinama Ammar kai alamar tabbatarwa. Tare da bin fuskokin sauran ƴan uwansa da suma ruɗanin ne ƙarara ya bayyana akan fuskokinsu har suka gaza motsawa.
Cikin ɗan rawar jiki Ummi tace, “Abubakar mi kake faɗane haka? Kana nufin yaron kwanaki da ƴan sanda suka sakata tai aiki akansa?”.