HALIN GIRMA COMPLETE HAUSA NOVEL

HALIN GIRMA 21

 Halin Girma      21

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

**************

Ta kofar ya koma ya fice bayan ya tabbatar da ya isar mata da sakon da yake son isarwa, yana kallon yadda tayi laushi sosai ta bishi da kallo har ya fice gaba daya.

   Kai tsaye wayar sa ya dauka ya kira Bashir, ya daga yana tafiya zuwa shashen Takawa dan yana son ganin shi

“Ya akayi Bashir?”

“Barka da warhaka Ranka ya dade”

” Barka dai, ya taro?”

” Mun gode Allah, an kawo amarya yallabai.”

” Yayi kyau, Allah ya baku zaman lafiya, ka kula da ita sosai kar naji wani abu mara dadi, karka kuma taba yarda mahaifiyar ta ko wani yace zai taka ka akan matar ka.”

” In Sha Allah ranka ya dade, hakan ba zata faru ba.”

“Yayi kyau, sakon ka na wajen Musaddik.”

Godiya ya hau yi dan dama abinda ya saka kiran kenan. Cilla wayar yayi a aljihu sanda ya isa sashen Takawan da ya zata ya jima da isa a adamawa.

***A tsorace take tun bayan da mutane suka yaye, yan matan biyu da aka barta dasu suma basu wani jima ba suka cikawa wandon su iska dan ba zasu iya zaman ba, babu kalar ma da bata yi musu ba akan su zauna amma suka ki, a cewar su idan suka zauna basu san uban da zai maida su gida ba su ba samari masu mota ba ga unguwar da shegen nisa kafin kaje titi. Haka tana ji tana gani suka yi tafiyar su suka barta. Tasha kuka kuwa kamar ba zata mutu, ta dinga tsinewa Bashir albarka taji kamar ta gudu ta bar garin ma baki daya.

   Tana nan a zaune cikin duhu taji ana saka mukulli a kofar gidan, tashi tayi da sauri tana zaro ido,a duhu take dan dama da wayar ta, ta haska kuma babu charge ta mutu tun dazu.

   Shigowa yayi yana haske gidan da wayar sa, ya shigo ciki ya dalle ta, tayi saurin kare fuskar ta tana cewa 

“Waye!” A tsorace

“Amarsu ta ango.”

Wani abu ne ya tokare mata a makoshi jin muryar sa, tayi kansa da sauri ta hau kai masa duka tana kuka

“Allah ya isa ban yafe maka ba, Allah ya isa.”

Rik’e hannun nata yayi da karfi ya juyar da ita ta dawo tana jingina da bayan sa

“Ni kike wa Allah ya isa? Lallai ma yarinyar nan.”

“Allah ya isa na fad’a mugu, macuci maha’inci.”

Juyo da ita yayi ransa na soyuwa amma ya danne kamar be ji komai ba, ya dalle mata baki da bayan hannun sa, yayi murmushi yana sake haske ta

“Duk abinda ma zaki ce ki fad’a amaryata.”

Kuka ta shiga rusa wa da karfi, ganin zata iya jawowa a jiyo su a makota ya sakashi jawota ya shiga sumbatar ta, ta dinga dukansa tana harbin sa a kafa amma ko a jikin sa, sai da ya gajiyar da ita sosai sannan ya saketa yana murmushin, a kalla ya rage zafi dan yasan ba lallai Hajjaju ta yarda ta barshi ba. 

   A wajen ta duk’a tana kuka, ta dinga jin kamar ta mutu ta huta da abinda take ji, tana jinshi yana waya har ya gama kafin ya dagata tsaye ya rik’e hannun ta a cikin nasa su shiga barin gidan.

   Mota ce a kofar gidan irin wadda yake zuwa wajen ta zance, bud’e mata gaba yayi ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver ya tada motar suka bar unguwar.

   Tafiya sukayi da dan nisa har suka iso unguwa, gangarawa taga yayi zuwa wata doguwar hanya suka dinga tafiya kafin su isa kofar wani babban gida, horn taga yayi da sauri me gadin ya bud’e gidan ya shiga da motar ciki. Tunanin ta ne ya tafi wani waje daban, ko dai Bashir gwada ta yake yana so yaga yadda zatayi idan ya kaita wanchan gidan shiyasa ya kai ta? Ko kuma dai duk shiri ne. Murmushi ya sakar mata ta cikin hasken da ya hasko cikin motar bayan ya tsaya a gaban ginin gidan. 

   Sauri taga yayi ya bud’e motar sanda wata babbar mata hamshakiya ta nufo su cikin wata irin kwalliya, ta sha ado sosai tana walwali, katuwar gaske ce dan zatayi biyu ko ma ukun Bashir din idaan aka hade shi da Zeenat din waje daya.

    Kafin ta kai ga garasowa Bashir din ya isa wajenta. Yayi kamar zai zube a k’asa a gabanta, ta riko shi tana masa murmushi, ware ido sosai Zeenat tayi tana tunani toh ko Maman shi ce? Karasowa tayi daidai kofar da Zeenat din take ciki ta bud’e mata tana sakar mata murmushi

“Amarya.” 

Ta kira ta tana sakin hannun Bashir din ta kama na Zeenat din tana jawo ta daga ciki.

“Sannu da zuwa kanwata, sannu sannu.”

“Kanwata?” 

Zeenat ta maimaita sunan tana bin Bashir da kallon neman karin bayani amma sai taga ya fuske kamar be ganta ba. Takawa suka shiga yi har zuwa cikin gidan wani babban falo da yasha kawa sosai. Wasu mata ne hamshakai suma kamar matar farkon suka tarbi Zeenat din suna tafi, ita dai Zeenat gaba daya kanta ya kulle jira take su samu kebewa da Bashir ta tambaye shi me yake faruwa. Zaunar da ita matar tayi ta ja hannun Bashir din sauran mstan suka hau shewa da dariya, bin su Zeenat tayi da ido har suka haura sama, zuwa anjima kad’an sai gata ta sakko ita kadai babu Bashir din cikin shigar kayan bacci ta karaso falon ta kalli sauran matan tace

“A rakata dakin ta ko?”

“An gama Lay, an gama.”

Suka tashi gaba daya, daya ta kama Zeenat din suka nufi wata hanya da take a bayan kafar benen dake falon, wani dogon corridor ne suka bishi har zuwa bayan dakunan gidan, sai wani daki guda daya a wajen da kofar sa tana kallon kofar da suka fito, nan taga an bud’e, sannan sun shiga gaba daya ciki.

   Katifa ce a k’asa karama kamar ta yan boarding sai wata karamar kujerar roba fara, suna shiga kamar jira dama suke matar da ta shigo da ita ta wurgar da ita a saman kujerar har sai da kanta ya bugu da bango, tayi kara saboda zafin da taji kafin wadda suke kira da Hajiya Lay (Layuza) ta rankwafo akanta tana mata kallon tsana tace

“Ke dan yar iska ce ke, har kin isa mu hada miji daya? Kin isa nayi sharing dake? Karamar yarinya da bata fi sa’ar yata karama ba, kece kishiyata ko? Toh ni ko a zamanin kuruciya ban zauna da kishiya ba balle yanzu da nasan ciwon kaina nasan abinda nake so, dan haka nan dakin da nake ajiye masu aiki nane kuma na sallame su dan yanzu basu da amfani, sai ki cigaba daga in da suka tsaya, shara wanke wanke, wankin undies dina da girki, komai ma dai da kika sani.”

Gaba daya kwakwalwar Zeenat ta gaza gane me matar take cewa, ji tayi kamar wani yare take mata na daban da bata sanshi ba, ta dinga jujjuya kanta tana son gasgata abinda taji akan Bashir din, yana da mata dama? Mata babba kamar wanna da ta yi sa’ar uwarsa? Abba ne ya fado mata, sanda ya kirata yake mata magiya kamar ba Mahaifin ta ba, ya kaskantar da kansa yana rokon ta akan ta rufa masa asiri ta hakura da Bashir amma ta shafawa idon ta toka, ta kekeshe kasa tace taji ta gani, yanzu ta yaya hakkin Abban ta zai barta? Tun a ranar farko ta fara fuskantar wannan tashin hankalin.

   Firgigit tayi sanda taji saukar abu kamar ruwa asaman fuskar ta, ta saka hannu ta shafa da sauri tana daga kanta

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button