TAKUN SAKA 21

Yaya Abubakar da shi kaɗai yasan lissafin da zuciyarsa keyi ya ɗan firzar da numfashi yana ciza lip ɗinsa na ƙasa da duban Ummin tasu cike da kulawa. “Ummi ki kwantar da hankalinki. Babu abinda zai samu Muhibbat da izinin ALLAH…..”
Da sauri Ammar ya amshe zancen da faɗin, “Ummi mugodema ALLAH ma da kafin a kaita gidansa ne komai ya fito. Yanzu kunga ko a kotu ne a raba auren kawai sai a bama Yaya Isma’il dama sunfi dacewa”.
Sosai maganar Ammar ɗin tai tasiri a garesu har Yaya Muhammad ya shafa kansa yana ɗan murmushi.
Yaya Abubakar kam ɗago kai yayi ya kallesa tamkar wanda zancen yayma allura. cikin nazarin furucin na ammar, ya ɗan kaɗa kai yana jujjuyawa, dan baya son faɗar abinda a yanzu zuciyarsa ke hasko masa kai tsaye saboda Ummi. Miƙewa yay yana faɗin, “Komai ma da baƙwa tunani zai iya yi. Sai dai inaji a jikina Muhibbat ce tarkonsa a wannan karon”.
“Yaya Abubakar kana nufin zai cigaba da bibiyar auta?”. Cewar Usman a tsorace yayinda duk suka bisa da kallo har Ummi.
Numfashi Yaya Abubakar ya fesar yana gyaɗa kai dai-dai yana ƙoƙarin kaiwa ƙofar fita. “Bazaka gane lissafinba Umar. Ku dai da ga yanzu dukkanin idanunku su kasance akan Muhibbat ne. Dan duk yanda kuke tunanin wanann shu’umin mutumin yafi ga haka. tabbas bazai taɓa bayyana kansaba bayan bai gama tsara yanda komai zai tafi masa ba.”
Da kallo kawai suka bisa harya fice yana ƙoƙarin kai waya bisa kunnensa. Da alama kira yayi. Kafin Ammar ya miƙe yana faɗin “bara na nemota itama.”
Kai kawai suka iya jinjina masa, dan jikin kowa ya gama sanyi a cikinsu.
★★★★
A ɓangaren su Musbahu kam koda suka iso L.E street. Habib ne ya shiga sanarma ogan nasu isowar tasu, duk da kuwa sarai yasan yaji.
Zaune ya sameshi ƙafa ɗaya kan ɗaya a katafaren falon nasu da yaji kayan more rayuwa yana sarrafa system da ke saman cinyarsa. Duk da yaji shigowar Habib ɗin bai ɗago da ga abinda yake ba, sai dai ya amsa masa sallamar akan laɓɓa.
Habib da ya ɗan kallesa ya risinar da kansa ƙasa da girmamawa yace, “Barka da hutawa Master”.
Uffan baice ba, bai kuma ɗago ya kalli Habib ɗin ba har tsahon wasu sakanni, sai dai ya jinjina kansa alamar amsawa.
Habib da ya fahimci ƴan mulkinne a kusa yau sai kawai ya cigaba da magana. “Aiki ya kammala, itama gata tare da mu”.
Dakatawa yay da ga sarrafa lap-top ɗin, a hankali ya ɗago idanunsa cike da ƙasaitarsa ya saukesu kan Habib ɗin da ya nutsu waje guda saboda tsabar girmamawar da suke bashi.
Kallo daya yay masa ya janye idanunsa ya maida akan system ɗin da faɗin, “Su Salis?”. Yay maganar a taƙaice cikin sigar tambaya”.
“Dukanmu tare muka shigo”. Habib ya bashi amsa.
Lap-top ɗin ya ajiye ya miƙe, batare da ya sake cema Habib ɗin komai ba ya nufi hanyar fita cikin takun da ke nuna cikakkiyar lafiyarsa da nutsuwar da ALLAH ya azurtashi da ita.
Shima Habib bayansa yabi da saurai suka fita a kusan tare. Kallo ɗaya yay ma su Salis da ke ƙoƙarin fitowa a mota ya ɗauke kansa da cigaba da tafiya cikin izza da ƙasaitarsa tamkar wani jinin mulki.
Dai-dai yana isowa inda suke suka haɗa baki wajen faɗin, “Barka da gida Master”.
Hannu kawai ya ɗaga musu yana nufar motar da Habib ya fita da ita. Da sauri Habib ya buɗe masa motar ta sashin da Hibbah ta ke yana matsawa gefe tamkar yanda sauran suka nutsu.
Duk da yasan a sume take hakan bai hanashi sake ɗaure fuska ba kafin ya sauke nutsatstsun idanunsa masu kaifin gani a kanta. Sai kuma ya ɗan kaudasu tare da ƙarasa takawa gaban motar da ƙyau yana yamutse fuska. Dai-dai lokacin da yake ranƙwafawa su Habib suka kalli juna, yana ɗagowa ɗauke da Hibbah suka waro idanu waje da saurin maida kawunansu ƙasa.
Ko kallo basu ishesa ba, sai ma sake tamke fuskar boginsa da yayi ya shiga taku cike da izzarsa da kasaita zuwa cikin gidan ɗauke da Hibbah da batasan wainar da ake toyawa ba.
Idris ya haɗe yatsunsa waje guda alamar love yana wani cije baki. Sauranma idanu suka shiga kashewa da yin alamar nice???????? cike da shaƙiyanci.
Tsaf yaga duk iya shegen nasu ta glasess ɗin windows. Ya ɗan ciji lip ɗinsa na ƙasa da tura ƙofar falon da ƙafa. Hakan ya saka su Khalid saurin mara masa baya gudun yin laifi.
Koda ya shigo falon up stairs ya nufa, anan ma falo ne babba masha ALLAH, wanda babu abinda baijiba na kayan more rayuwa. Sai tashin ƙamshi yake ga sanyin ac mai saka nutsuwa. Kai tsaye ya nufi ɗaya da ga cikin bedroom ɗin da ke a up stairs ɗin. ya shimfiɗeta saman gadon ɗakin yana wani sake ɗaure fuska da yamutseta irin shifa ya gajin nan. Ya ɗan zubamata harara yana janye jikinsa. Wayarsace ta fara tsuwwa alamar shigowar kira.
Sharewa yay tamkar bazai amsa ba. Sai da ta na gab da tsinkewa ya zarota a aljihun wandon baƙin jeans ɗin jikinsa yana jan siririn tsaki da jingina jikin mirror ɗin ɗakin yana kaiwa kunnensa batare da ya ce uffan ba, sai dai shirun nasa na nuna alamun sauraren mai magana ya ke da ga can. Tsawon minti biyu da wasu sakanni ya ce, “Uhmm” da ɗan gyaɗa kai.
Dai-dai nan akai Knocking ƙofar a hankali, kasancewar sun san idan yana a irin wanann yanayin duk wata hayaniya baya buƙatarta.
Cikin ƙosawa da motse-motsen kuwa ya bada izinin shigowa yana janye wayar a kunnensa………..✍
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????
#team ZAFAFA BIYAR????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*
[ad_2]