Uncategorized

TAKUN SAKA 25

 *_Typing????_**_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

_______________________

*_Chapter Twenty Five_*

………..Hibbah ta haɗiye yawu da ƙyar da ƙoƙarin haɗiye tsoronta ta zuba masa harara. “Dan ka kasheni ai ba abin mamaki bane, mutumin da ya ke gawurtaccen ɗan Homo ne kashe rai zai zama abin damuwa a garesa, wama yasan iya adadin nawa ka kashe ka binne a gidan”.

      A yanda tai maganar cikin tsoro da ƙarfin hali yay matuƙar bashi dariya. Sai dai ya shanye abarsa cikin rai, a zahiri ma sai sake tamke fuska da yay yana yamutseta. Ya janye bindigar a kanta tare da kaita ya ɗan buga a saman laɓɓanta. “Wannan bakin naki shine zai halakaki stupid girl”.  

      Ya faɗa yana sauke ƙafarsa ƙasa da miƙewa da ga ranƙwafowar da yay a kanta yana ƙwafa. Nannauyan numfashi Hibbah ta sauke a ɓoye da lumshe idanunta ganin ya fice a ɗakin ko waiwayenta baiyi ba, tai saurin kai hannu saman ƙirjinta ta dafe saboda yanda yake bugawa da sauri-sauri. Dan harga ALLAH ƙarfin hali kawai tayi da ganin wannan bindigar akanta. Ga shegun idanunsa da ke saka zuciyarta tsargawa tamkar zatai zallo ta fito waje idan ya zuba mata su. A fili tace, “Gashi ɗan iska ɗan homo, amma sai shegen kwarjini.

(Hibbarmu karki sake kiji tsoronsa. Dan karma su o.e ƙannensa suji kansu ya ƙara girma ehe????????????????????.) 

★★★★★★

         

            Dauriya Ummi kawai takeyi na rashin ganin Hibbah bata shigo musu ba har kusan goma na safe. Tanaji a ranta anya su Yaya Muhammad basa ɓoye mata wani abu kuwa? Dan babu yanda za’ai su kwana gida ɗaya da Hibbah ta iya haƙurin kawai yanzu bata nema inda take ba. Musamman anan da take ganin sabon gida tunda ba’a taɓa zuwa da ita ta gani ba sanda ake ginin. Hasalima babu wanda ya taɓa sanar mata ita da Ammar. Sai da ga baya ne Ammar ɗin ya sani, suka kuma gargaɗesa da kar ya faɗama Hibbah.

          Shigowar Isma’il gidan kusan sha ɗaya na safe ne ya ɗan rage mata ƙulafucin son ganin Hibbahn. Bayan sun gaisa cike da girmamawa yay mata bangajiyar biki tare da yima anguna addu’ar zaman lafiya.

       Cike da kulawa a garesa Ummi da ke murmushi ta ce, “Saura kai Isma’il. Ya kamata ka nemo matar aure haka nan, dan shi aure cikar kamalace ta ɗan adam koda ace ya kasance mutumin banza ne. Idan kuma kaima irin nasu Usman ɗin zan maka to”.

       “Ƙayataccen murmushi ya saki da sake duƙar da kansa yana shafa ƙeya. Ummi karki damu kiyimin addu’a kawai”. Ya faɗa murya a tausashe saboda yanda yake jin Ummi matuƙa a rai kodan yana ƙishirwar mahaifiya.

        “Kullum addu’ar nan ita muke muku Isma’il. ALLAH ya cigaba da tsareku a duk inda kuke. Ya baku kariya da ga dukkan abun ƙi. Yay muku albarka ya baku ƴaƴa nagari da zasu kwatanta muku ƙyautatawar da kuke mana da biyayya”.

        Tasowa yay ya durƙusa gaban Ummi hawaye na ciko idanunsa, yay haɗiyesu da ƙyar yana faɗin, “Amin ya rabbi Ummi nagode”. 

       Hannunta ta ɗora saman kansa ta shafa dan tsaf ta fahimci abinda yake buƙata kenan. Tausayi yake bata yaron har cikin rai, dan ta jima da nazartar yana matuƙar bege da ƙishirwar mahaifiya ne.

          “ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai albarka Ummi”.

      “Amin Isma’il”. Ta faɗa tana murmushi da sake shafa kansa har fararen haƙwaranta na bayyana.

           “Uhmm kaga ɗan gatan Ummi, ashe kana nan?”. Su yaya Abubakar da ke shigowa suka haɗa baki wajen faɗa suna kallon Isma’il ɗin. Ƙaramar dariya yayi da miƙewa da ga gaban Ummin ya koma inda ya taso. “Gara nai sauri na kwashi rabona kafin kuzo ai mana raba dai-dai.

       Usman da ke dariya ya ce, “Gaskiya Yaya Isma’il i’m jealous”.

       Dariya suka sanya gaba ɗayansu harda Ummi. Kafin su ƙaraso cikin ɗaki su mimmiƙa masa hannu har Yaya Muhammad. Da ga haka suka zauna aka dasa sabuwar hirar da ta sake ɗauke hankalin Ummi duk da kuwa zuciyar tata naga son ganin Hibbah ta shigo. Dan a cikin firarma sunayi suna sakko sunanta da rashin jinta suna dariya. Basu taso gaban Ummi ba sai ƙarfe ɗaya suka fita massallaci. Da ga nan Isma’il yay gaba su kuma suka koma cikin gidan da yake ya ƙara cika da dangin amare ƴan buɗar kai dan yau anguna zasu shiga ɗakunansu.

★★★★★

          A ɓangaren Abba kam barazanar rashin barci da ya fuskanta a daren jiya ce ta kaisa ga makara sai kusan takwas ya farka. Farkawar ma ba kaitsaye yayita ba masifar Momy ce da ta dawo asibiti ta gansa yana barci ta farkar da shi.

       “Yanzu wannan wane kalar rashin mutunci ne haka Hadiza? Ina tsaka da barci kizo ki tadani saboda rashin mutunci”.

        “Ni da kai a tantance mara mutuncin Abban Junaid. Yanzu dan ALLAH ko kunya bakaji ba ɗan ka namiji tilo na asibiti rai a hannun ALLAH amma kai kana nan kana barci hankali kwance. Bakaje kaga halin da yake a ciki ba baka ɗauki wani matakiba kuma ga wanda ya aikata masa. To sai ka miƙe dan Asiya da yaranta duk basa gidan nan. Yanda alamu ma suka nuna basu kwana ba a cikinsa”.

       “What?!”

Ya faɗa yana wantsalowa da ga gadon ƙirjinsa na wani irin bugawa. “Hadiza wace maganar banza ce wannan. Ita Asiyan idan ta fita anan gidan ubanwa zataje tunda bata ajiye kowa ba bayanan nan ɗin?”.

       “To waya san ko tana da wajen zuwan abu a duhu. Ga dai Hajiya mama can ta gama bincike ko ina na gidan nan ita da su Garba amma babu komai kama da su. Alamuma sun nuna dama da shirin hakan tare da su dan duk sun tattare kayansu masu muhimmanci da ga sashen”.

      “Kutuman bura’uban nan kayyasa”. Abba ya danna ashariya tamkar ɗan gidan maguzawa. Ita kanta Momy jin ashariyar tasa sai da ta zaro idanu waje. Hannu yasa ya ingijeta tare da fisgar sandarsa ya yo waje. Tun daga sama yake hango su kawu bello tsaye cirko-cirko a falo cike da tararrabi.

       Bai iya tanka musu ba tsabar rikicewar da yay ya fice da sassarfa duk da azabar da yakeji sabuwa ƙafarsa na masa.

      Tabbas babu alamar Ummi da ƴaƴanta a gidan. Wannan al’amari ya matuƙar hautsina kan Abba. Babu shiri ya shiga bige-bigen waya. Kafin ya tattara yabar gidan batare da ya tuna da ƙarin sallar asuba da ke a kansa ba bayan sallolin jiya da bai sauke ba har yanzun.

       Yayinda ya bar ƴan biki nata kace nace akan wannan al’amari. Harda masu yima ƴaƴan Ummi da ita kanta addu’ar tsiya suna mai goranta mata asalinta. Oho bama tasan sunai ba, su aiki ya sama????????????.

★★★★★

        A ɓangaren Hibbah kam Master na fita babu jimawa taji sallama a ƙofar ɗakin tare da knocking. Sam jikinta babu wani ƙarfi dan yunwa takeji matuƙa ga rashin ƙarfi. Hakan yasa tun bayan fitarsa bata motsa da ga inda take ba. Tunanin shine ya sake dawowa ya sakata harar ƙofar tamkar idanunta zasu faɗo. Ta kuma ƙiyin magana.

    Baba Saude dake tsaye ta sake ɗan buga ƙofar da ɗaga murya sosai wajen sallamar. Ɗan zabura Hibbah tayi jin muryar mace. Ta amsa da ƙoƙarin son tashi, sai dai kafinma ta tashin Baba Saude da taji an amsa mata harta shigo abinta ɗauke da tray.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button