TAKUN SAKA 29

Master ya cigaba da faɗin, “Na shigo rayuwarku ne a dalilin Muhibbat, sai dai labarin ya sauya adalilin karamcin Ummi da ku kanku. Sai kuma randa na jima Halilu ciwo saboda ranar na fara ganinsa a gidanku, na kuma sansa a matsayin yaron su Alhajin Mande. Wannan dalilin ne ya sani yin bincike akanku sosai harna gano mummunar manufar da yake da ita a kanku. Cikin sa’a kuma abinda yake shiryawa a kankun sai aikinsa ya faɗo hannuna duk da dai nina saka A.G yay hakan batare da shima ya sani ba. Shiyyasa na koma ta bayan fage nazo ma Muhibbat matsayin Muhammad Shuraim. A lokacin da naita bibiyarta nine da kaina. Sai dai kuma ƙanina Musbahu shine yake zuwa gareku da fuskar Shuraim. Yayinda shima kansa baisan niɗin nine Isma’il ba, na kuma cigaba da ɓoye musu zahirina saboda wani dalili nawa daban. Dan basu taɓa sanin ainahin fuskata ba duk da kuwa tun suna ƙanana suke tare dani. Sannan basu taɓa sanin aikin dana tsundumasu a ciki munayi tare ni miye dalilinsa ba. Tsabar biyayya da soyayyar da sukemin ce kawai tasa basu taɓa min musu ba akan komai da nace suyi. Domin gaba ɗayansu na horar da su akan harkar Computer.”
“Kune mutane na uku da kuka san ainahin fuskar Isma’il bayan iyayena da baba. Wanda da farko naje asibiti da wata fuska ne daban, a dalilin Ummi naji bazan iya zuwa mata a baɗinina ba shiyyasa na sake komawa na biya kaso ɗaya bisa ukun kuɗin aikinta bayan na biya duka a farko. A yau kuma na zaɓi bayyana muku zahirin gaskiya ne a dalilin Ummi. Banason ta shiga wani hali akan rashin Muhibbat, sannan ya kamata kusan wane ƙudirine a zuciyar Halilu kar yabi ta wata hanyar ya cutar da ku idan yaga ban masa aikinsa yanda yake so ba. Dan na tabbata zai binciko gidan nan yanzu hakama dan a rikice yake kuma shi mutum ne kamar sauna idan ya ƙwallafa rai akan abu.”
“Na ɗauke Muhibbat ne saboda bin bayan Halilu da tai ranar ɗaurin aure batare da kun sani ba, yayinda ta jiyo sirrikansa masu yawa. A ranar ɗaurin aure yawan mutane yasa bazaku fahimci bana tare da ku ba. Amma kuma nazo, sai dai ganin fitowar Muhibbat da duk da ta saka hijjab da Niƙab na ganeta ya sani fasa bin ƴan ɗaurin aure nabi bayanta. Sai da na tabbatar da inda ta nufa sannan na koma gida a hanzarce, amma tunkan na ƙarasa na kira Habib ya sameta a wajen, hakama maigadin gidan halilun, saboda duk gidajensu na sirri da suke aikata tsiyatakunsu akwai yarana a ciki, amma ba cikin su Habib ba. wasu masu gadi, wasu masu musu aikin gidan batare da sun sani ba. Aurenku kuwa da yaransa dama can na shirya wargazashi tsaf. Dama na tsara sai an kai Muhibbat gidana zaku san nine master, a gefe kuma na cigaba da kasancewa daku matsayin Isma’il. To sai akai rashin sa’a autar Ummi ta buɗemin aiki saboda rashin jinta”.
Murmushi Ummi tayi da kai hannu ta share hawayenta. Suma su yaya Muhammad duk murmushin suke da sauke ajiyar zuciyoyi.
“Kuyi haƙuri da fuskokin yaudara dana zo muku daban-daban. Ni kaina inaji haushin yaudarar Ummi, shiyyasa na zaɓi zuwa na bayyana muku kaina dan ku kanku ku sami nutsuwar shiga sabuwar rayuwa a yau. Hakama Ummi hankalinta ya kwanta kar garin neman gira a rasa ido dan bazan yafema kaina ba idan wani abu ya sameta adalilina. Auta na tare dani tana zubamin tsiwa da tsaurin ido Ummi, sai dai banason ta san niɗin wanene yanzu har sai nan gaba. Aiki akan Halilu kuwa ita daya raina itace zatayi komai da kanta insha ALLAH”.
Dariya duk sukayi, Yaya Abubakar da gaba ɗaya ya tsunduma tunani da nazartar labarin Isma’il Master yay ɗan murmushi, “Ai ni auta kamar ba’a gasa mata baki wajen wankan jego ba. Dan wannan bakin natane ya jefata a tarkon jami’an tsaro su A.G sukaso yin amfani da ita. To ashe wanda suke bulayin neman shi tuni ya gama neme su”.
Nanma dariyar suka sanya. Yaya Umar ya karɓe da faɗin, “Ai bakin auta ya mana rana. Tunda gashi ya jawo mana Master har cikin gida batare da mun saniba. Sai dai muna son sanin ƙyaƙyƙyawar manufarsa kodan mu cirema ranmu zarginsa a jerin na ɗan ta’adda ɓarawo da kowa ke kallonsa da shi.”
“Wannan gaskiya ne yaya Umar. ALLAH ya jikan su Mamy yay musu rahama ya saka musu, amma ya kamata musani kam”.
Cewar Yaya Usman da hawaye suka ziraro masa na tausayin Master ɗin. Gaba ɗaya suka amsa da amin, sannan suka shiga ƙara jero sabuwar addu’a ga mahaifansa. Ummi kam tama gaza cewa komai. Dan zuciyarta a matuƙar raunane take da tausayinsa. Yayinda a gefe takejin matuƙar nutsuwa da kasancewar sa miji ga ɗiyarta ɗaya mace tilo marainiya duk da yaƙi faɗar dalilin nasa na shiga wannan harkar, sai dai tana masa ƙyaƙyƙyawan zato. Sai ɗunbin al’ajab na son zuciya da shahara a zalunci na Halilu wanda suma su Yaya Muhammad ɗin duk yake cin zukatansu……
Master ya katse tunanin Ummi da faɗin, “Ƴan uwana kuyi haƙuri wannan sirri ne mai matuƙar daraja a gareni, badan ban yarda daku ba kuma na ɓoyesa. Insha ALLAH zaku san dalilina wataran. Na yarda ku san niɗin wanene saboda kuma kun sanar dani sirrinku a lokacin da baku gama sanin niɗin wanene ba. Kun kuma yarda dani duk banzo muku a yanda kukai tsammanina ba. Dan ALLAH ina roƙonku ku bizne wannan sirrin a wannan falon har sai ranar da ya kamata gaskiya ta bayyana kanta ga kowa”.
“Tabbas ita amana abuce mai nauyi Isma’il. Kuma ka cancanci muriƙe maka ita dan kaima ka riƙe tamu, yayinda kaketa hidima da gwagwarmaya a kanmu batare da mun sani ba. ALLAH ya saka maka da alkairi, ya cigaba da baka kariya akan ayyukanka. Ya kuma baka ikon sanar mana dalilin naka wataran. Bani da haufi game da sauran ƴan uwana akan riƙe maka wannan sirrin, dan nasan mahaifiyarmu ta mana horo akan hakan tunba yanzuba. Ballema wannan sirin riƙesa a garemu tamkar rike namu sirrine. Fita da shi kuwa tamkar tozarta kammune.”
Yaya Abubakar ya amshe da faɗin, “Wannan gaskiyane Yaya Muhammad. Insha ALLAHU bazakai baƙin ciki akanmu ba Isma’il. A matsayina na jimi’in tsaro kuma zan cigaba da baka gudunmawa insha ALLAH a duk sanda kake buƙata, sai dai ina roƙonka ka tabbatar duk abinda kake aikatawar nan kanada hujja ta gaskiya aranar kare kai, dan idan naci karo da saɓanin hakan komai zai iya faruwa”.
Murmushi yayi na ƙasaita yana jinjina kansa, “Nagode matuka yan uwana da Ummin mu. Abubakar karka damu kaima insha ALLAH, dan na jima da saninka da kuma gaskiyarka da ƙwazon aiki.
“Shiyyasa kazo kaketa min ƙafar angulu akan auta ko?”. Yaya Abubakar ya faɗa cikin barkwanci.
Dariya suka sanya baki ɗaya. Banda Master da murmushi ne kawai nasa dan dama can yawan fara’a ba ɗabi’arsa bace. Sunema yake sakewa da su matuƙa fiye da zato da hasashe. Duk da dai lokacin baya yana zuwa musu ne da fuskar mutane masu sanyin hali saboda salon acting daya ƙware akai like wani ɗan film. Miƙewa yay yana duban agogo ganin dare yaja. “Kai kai bara na barku kuje ga amare fa Yaya Muhammad kar mu take shari’a. Ummi samin albarka na gudu nima”.
Kansa Ummi ta dafa tana murmushi dan ita kallon ɗa take masa bawai suruki ba. Tai masa addu’a da sanya albarka saboda har yanzu zuciyarta bata gama dai-daita da sheɗancin da Halilu ke shiri akansu ba. Dan ma bataji yana aikata ƙazantar luwaɗi ba kenan. Sallama yay musu ya fita akan zai dawo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu dan zai zama busy a satin nan.