LabaraiTurji

babu wata alaƙa tsakanimu da Boko Haram Na dauki Bindiga don kare hakkin Fulani ‘yan uwana da aka takura mawa Bello Turji

Daga | Ahmad Aminu Kado,

Bello Turji Yace , Sam su basu da wata aƙida ko ra’ayiin siyasa.

Kawai sun ɗauki makami ne don kare kawunansu. A cewarsa: “Bamu da ra’ayin kafa wata kungiyar addini.

Bamu da niyyar yanke wata ƙasa, kuma babu ruwanmu da siyasa., Cewar Bello Turji kamar Yadda Jaridar Turst TV ta Wallafa shi a faifan Bidiyo.

Kamar Yadda na faɗa Mun ɗau makami ne don kare rayukan al’ummarmu da ake kashewa.” “Ba wai bamu da imani bane ko bamu da tsoron Allah ba.” Mutane sun yi mamakin yadda na zama dan bindiga, a Matsayina na makiyayi ne.

Bello Turji Turji, wanda dan asalin garin Fakai a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara ne, ya bayyana cewa wadanda suka san shi sun yi mamakin yadda ya fara sata da kashe-kashe.

Turji ya kara da cewa a rana guda aka kashe masa yan uwa shida bayan sacewa iyayensa Shanu sama da dubu. Haka yasa ya dau bindiga don kare hakkin Fulani yan uwansa da aka takurawa a karamar hukumar Shinkafi ta jihar.

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button