Uncategorized

TAKUN SAKA 29

     Har ƙofar gida su Yaya Umar suka rakoshi zukatansu sakayau bakamar yini da kwanan jiya ba da suka kasance a damuwar rasa Hibbah. Yana tafiya suka rufe gidan suka dawo ciki, zukatansu kuma fal tunanin miyasa yake aikata yahoo? Dan suna buƙatar sanin hakan kodan ƙanwarsu da ke a hannunsa matsayin mata. Bazasu so ta kasance a gararin rayuwa ba, ba kuma zasu so ta kasance da mijin da zai ciyar da ita ta hanyar haram ba.

       Sun so zama su tattauna maganar Ummi ta korasu suje ga matansu da safe zatai magana da su. 

      

★★★★

     Tunda yabar gidan su Ummi ajiyar zuciya yaketa faman saukewa da dafe kai saboda ciwon da yake masa na rashin sabon dogon surutun daya zuba a yau. Sai dai kuma yanajin zuciyarsa sakayau tamkar ya sauke wasu kaya masu azabar nauyi dake a kansa ne. Sai da ya biya ta gidan A.G ya amshi takardun aikin Abba sannan ya wuce gida.

       Koda ya isa gidan a falo ya samu su Habib sun baje kowa da hidimar da yakeyi, ga kayan ciye-ciye sun baje tamkar wata sabuwar bola. Shigowar tasa ce ta saka falon ɗaukar shiru kowa ya nutsu. Cike da girmamawa a garesa tamkar yanda suka saba suka shiga masa barka da zuwa. Hannu ya ɗan ɗaga musu yana bin falon da kallo fuska a tamke da binsu da harara. Sun san laifinsu dan haka suka shiga sosa ƙeya kowa na kai hannu a sace yana ɗauke ledar gabansa da su gwangwanaye.

    Komai baice musu ba ya nufi upstairs ɗin yana hawa steps ɗin a kasalance da izzar data zamewa gaɓansa jiki. A dai-dai nan Hibbah da yunwa da damuwa ke neman halakawa ta fito daga cikin ɗaki itama cikin ɗan layin barcin data fara tun bayan idar da salar isha’i. Abincin data hanga a shirye a dining ɗin falon saman ya sata nufar can duk da ta fahimci mai faɗa ajin gidan aka shirya mawa. Kujera taja ta zauna a fili take faɗin, “Daga gani shegen ci ne da wannan mutumin, tunda kuwa ya sakani kuka ɗazun na rantse da yunwa zai kwana shima mugu dangin su Halilu mtsoww ”.

       Karaf kuwa wannan zance a kunnen Master da ke hauro step ɗin ƙarshe. Cije lip ɗinsa na ƙasa yayi tare da kai dubansa gareta da lumsassun idanunsa da tsantsar gajiya da ciwon kai ya kanainaye. Ya ɗan sake tsuke fuska da nufar inda take batare da ita kuma tasan da shigowar tasa ba. Hidimar ma zuba lafiyayyen abincinsa da baba saude ta haɗa masa na musamman takeyi cike da mugunta. Ta ɗiba gasashen hantar da yaji kayan haɗin salad zata kai baki ya riƙe hannun…………..✍

*_Gashi nan harda na gobe idan ALLAH ya kaimu????????????_*

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????

#team ZAFAFA BIYAR????????????????????

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button