Uncategorized

TAKUN SAKA 30

    Wani irin ɗaci da jin zafinsa ne ya soki zuciyar Hibbah. Ta cije lips ɗinta da ƙarfi tana matso hawayen da suka sake ciko mata idanu. Cigaba tai da tafiyarta wani duhu-duhu na mamaye idanunta.

       Da ƙyar ta ƙarasa saman gadon kuka na sake kufce mata. Tana tsoron rasa Ummi da yayunta, tana takaicin fasiƙi azzalumi irin Abba ya samu galaba akansu. Sai a yanzunne take jin matuƙar takaicin biye masa tun farko harta maida murtani. Dan zuwa yanzu ta fahimci irin wannan mutumin ba’a cinsu da yaƙi ta ƙuru-ƙuru sai ta siyasa da taku. Hakan na nufin kuma sai ka kwantar da kai wajen fara fahimtar su ɗin su wanene kafin ka samu damar kutse a lamuransu. Inama ɗazu shiru tai masa har yayi ya gama. (Dole ne yanzu ta sake sabon shiri), ta ayyana a ranta tana miƙewa zaune. Mamaki ya kamata ganin bai fita ba. Ya saki ƙofar ya juyo hannayensa harɗe a ƙirjinsa ya tokare ƙafarsa ɗaya jikin ƙofar daya jingina bayansa. Sai idanunsa da ke matuƙar hanata sukuni da tsiwa da ya zuba mata yana wani kallonta tamkar a ɗage.

     Kanta ta maida ta duƙar tana share hawayen. Lumshe idanun yay ya buɗe yana ɗaukesu da ga kanta ya maida kansa ga ƙofar ya jingina. Ta ƙasan ido ya koma kallonta batare da tasan yana cigaba da kallon nata ba duk da tanajinta a takure har yanzun.

      “Zan iya baki dama bisa sharaɗi”.

Da sauri ta dubesa jin abinda ya faɗa. Tai saurin miƙewa ta nufosa cikin sassarfa. “Dan ALLAH Yaya kana nufin zaka barni in tafi wajen Ummi na?”.

       Ta faɗa tana matsoshi gab batare da tasan tayi hakan ba saboda zumuɗi. Idanunsa ya buɗe da ƙyau a kanta jin yanda ta kusanta kanta da shi. Yanda ya zuba mata idanun ya sata tura baki tai ƙasa da kanta.

       Warware hannayensa yayi yana miƙewa da ƙyau ya tsaya kan ƙafafunsa. Hakan sai ya sake kusancin nasu matuƙa. Baya ta ɗan ja tana sake ɓata fuska. Takowa yay ya sake matsawa suka koma yanda suke, bayan ta shiga jan ƙafafunta. Shi kuma ya cigaba da takawa yana binta har suka dangane da mirror. Hannayenta duka biyu ta dafe mirror ɗin da su tai ɗan baya saboda yanda ya tsaya mata ƙiƙam tamkar soja. Bakinta ne ya shiga motsawa alamar akwai magana amma babu damar faɗa.

       Fahimtar hakan ya sakashi fara magana a daƙile yana bin fuskarta da kallo. “Zakiyi aiki na wata guda tare da mu….”

       Zabura tai babu shiri, hakan ya sata faɗawa jikinsa saboda kusancinsu. Bai riƙeta ba, dan haka ta sake komawa baya jikin mirror ɗin tana faɗin, “Kana nufin nima na fara sata?”.

       “Itama sana’ace ai”.

Yay maganar yana tura duka hannayensa a aljihu da lumshe ido ya buɗe lokaci guda. 

      “Tab wlhy ban yarda ba. Ƴar yahoo fa kenan mai datsan accaunt ɗin mutane, zamb…….?”

      Tai saurin rumtse idanun da bakinta batare da ta ƙarasa ba saboda ganin ya ɗora hannayensa saman mirror ɗin yayo kanta. Saurin maida lips ɗinta tai cikin baki ta matse tana ƙwaɓe fuska tamkar zatai kuka, dan yanda ya kusanto da fuskarsa da tata har yana busa mata numfashinsa sai ka ɗauka wani abu zai mata. Janye fuskar tasa yay ya maida saitin kunnenta yana sake tsuke fuska. Cikin wani irin Slowly voice da ke nuna gajiyarsa matuƙa ya fara magana yana shaƙar ƙamshin da gyararren gashinta keyi duk da ya ɗan mimmiƙe ta gaba dan tun gyaran ranar ɗaurin aure. “Ashe zaki dawwama tare da Master har tsufanki babu ganin Ummi”.

      “ALLAH ya kiyaye na zauna da mai homo, wlhy kota katanga sai na haura”.

       Baki ya taɓe da ɗage kafaɗa irin I don’t care ɗinnan. Batare da ya sake ko kallonta ba ya nufi ƙofa abinsa cike da takun ƙasaitarsa da izza. Kukan ƙarya Hibbah ta fashe da shi duk da dai har cikin ranta tanajin raɗaɗi da takaicinsa. Baiko nuna yasan tanai ba ya buɗe ƙofar ya fice abinsa.

       “Mugu danginsu Halilu. Na rantse sai kayi dana sanin satoni wannan gidan naka, dan saina addabi kowa. Da wani idanunsa abin tsoro”.

     Oho shi baima san tanai ba. Dan tuni ya kai downstairs. Kamar yanda ya saba a duk dare sai da ya leƙa ɗakunan su Salis ya tabbatar suna lafiya. Waɗanda basu kashe fitila ba ya kashe musu. Wasu ma har barguna ya gyara musu a ransa yana ɗan mamakin kwanciyar tasu da wuri yau, sai da ya ƙara musu addu’ar barci kamar yanda ya saba sannan. Compound ya fito ya dudduba. Sai da ya tabbatar komai normal ma anan sannan ya dawo ciki ya kashe sauran fitulun ya haura sama. Ƙarasa shirin barcinsa yay ya haye gado yana godema UBANGIJI da ya kaisa wanann lokaci da rai da lafiya bayan wasu na asibiti wasu ko na gida cikin jiyya matsanciya. Cikin ƙanƙanin lokaci barci yay awon gaba da shi dan yayi matuƙar gajiya. Gashi dama yasha maganin ciwon kan.

     A ɓangaren Hibbah kam sai da ta gama sharce-sharcen ƙwallarta ta cire hijjab ɗin bayan taje ta murzama ƙofar key. Kayan daya ajiye ta warware. T-shirt ɗinsa ce mai gajeren hannu da three quarter wando sai mayen ƙamshinsa sukeyi. Ta ɓata fuska tana cillar da kayan. “Ni bazansa kayan ƴan homo da yahoo ba”. Tai maganar tamkar zatai kuka.

     Abincin da ya ajiye ta ɗauka da bottle water ɗin da suma ya ajiye ta zauna a bakin gado ta fara ci dan da gaske yunwa takeji. Taci sosai tasha ruwan sannan ta miƙe. Kayan ta sake harara dan harga ALLAH tana buƙatar saka sutura a jikinta. Bazata taɓa iya barci da guntun ɗankwalin dake ɗaure a jikin nata ba. Hakama kayan data cire ƙyanƙyaminsu take bazata iya maidasu jikinta ba. Wando da rigar data gama mita a kansu ta ɗauka ta saka. Sai ga three quarter ita ya zamar mata dogo, dan kaɗan ya rage ya rufe idon sawun ƙafarta. Hakama rigar tai mata burun-burun tamkar kaita mata dariya. Baki ta taɓe da yamutsa fuska tana duban kanta a mirror, dan ba karamin addabarta ƙamshin turaren nasa yayi ba.

   Idonta ne ya sauka akan tab ɗin daya ajiye mata. Ita sam tama manta da ita. Ɗauka tai da saurin tana faɗin, “Stupid me. Wai mima ya kaini masa magana bayan ga maganin kukana anan”. Ta ƙare maganar da ƙyalƙyalewa da dariya. Ta dira tsalle ta ɗane gado ranta fal farin ciki. Babu lock a tab ɗin, hakan ya bata damar sauke idanunta akan hoton su Habib su bakwai sai shi na takwas a tsakkiyarsu, duk sun wani kanannaɗe masa jiki tamkar tata. Shima ya shafo fuskar Adam da Khalid dake gefe da gefensa yana ɗan murmushi. Daga ƙasa Habib da Idris suna zaune sun ɗaura kawunansu bisa ƙafarsa ɗai-ɗai sun kwantar. Sai bayansa Musbahu, Zaidu, Salis suna akan kafaɗarsa suma. A kallo ɗaya zaka fahimci tsantsar ƙaunar da sukema juna. Ta ɗan taɓe baki da faɗin, “A haka dai kamar mutanen kirki, sai dai ALLAH kaɗai yasan tsiyatakun da kuke aikatawa.”

       Kauda hoton tai da nufin shiga inda applications suke taci karenta babu babbaka sai taga saɓanin haka. Dan kai tsaye ga shagon da zatai sayayya ya kaita. Cikin takaici tai ƙoƙarin fitowa amma hakan ya gagara. Tamkar zata fasa kuka dan haushi. Har tayi niyyar ajiye tab ɗin sai kuma ta tuna bata da sutura kota yin salla. Da bai taimaketa ya bata waɗan nan ba ma da batasan yaya zatai ba. Kaya ta fara zaɓa harda underwears tanata faman ƙunƙuni. Yanda taketa zaɓar abubuwa zaka fahimci harda mugunta a ciki. Dan sai faman taune lip take tana murmushi. Sai da ta gama yayar kaya san ranta sannan ta dangwarar da tab ɗin tana hararta ta koma ta kwanta duk da bata tunanin zata iya yin barci saboda kewa da damuwar rashin ahalinta a tare da ita.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button