TAKUN SAKA 30

*_WASHE GARI_*
Kamar yanda ya saba shine ya tashesu suka wuce massallaci duk da kuwa bayajin daɗi, dan ciwon kan har yanzu bai sakesa ba duk da yayi barci. Koda suka dawo su kaɗai suka shiga ɗakin motsa jiki shi sama ya dawo. Bai ko kalli ɗakin da Hibbah take ba. baima nuna ya tuna tana gidan ba ya shige abinsa.
A ɓangaren Hibbah ma ta farka dan ta saba. Sai dai tana idar da salla ko azkar batai ba ta haye gado ta koma barci. Barci sosai ta sha har kusan goma saura. Tana buɗe ido da ledoji taci karo manya-manya guda uku. Fahimtar kallo daga nesa bazai mataba ya sata sakkowa taje garesu. Ɗan bubbuɗewa tai sai taci karo da kayan datai shopping jiya da dare ta online. Babu shiri ta shiga sungumar ledojin duk da akwai nauyi tana kaiwa saman gado ta dinga ɗagasu tana zazzagewa.
Mamakine ya bayyana a saman fuskarta ƙarara. Dan duk abinda ta zaɓa ɗin an sako mata. Harma da wanda bata zaɓa ba na fanin kayan shafa, sabulai, kayan gyaran gashi, da kayan yan kunne sai takalma. total na kuɗaɗen da aka sakko ta shiga dubawa mamaki na neman halakata. “Anya mutumin nan yana da man kai kuwa? Koda yake ina ɗan yahoo ma yasan zafin kuɗi tunda wasu suka tara ya wawasa. ALLAH ya gani naidai tunda badani ya sato ba ko naci banda zunubi”. Ta faɗa cike da yarda da kai.
Dama azababben ƙamshin turaren kayansa ya isheta, dan haka ta faɗa wanka. Bata wani jimaba ta fito dan dama bata daɗewa a wanka, da sabbin kayan shafanta tai amfani, dan tana son fara aiwatar da shirinta na yanda zata kuɓuta a gidan nan. Tai kwaliyarta gwargwado ta shirya cikin wata doguwar riga maroon mai laushi da tabi jikinta kasancewar kamar roba take. Sai dai bata fidda mata jiki ba. Dan daga sama an mata wani ado da yay tamkar mayafi ya rufe ƙirjinta duka hakama ya sauka bayanta har kasan mazaunai. Ita kanta tasan tayi kyau gwargwado. Dan haka ta tattare sauran kayan tasa a Wadrobe ɗin ɗakin ta ɗauka gyale karami dake cikin kayan ta yana a kanta. Tab ɗinsa da plate ɗin da taci abinci jiya ta ɗauka ta fito, dan yanzun ma yunwar takeji.
Babu kowa a falon saman sai ƙamshin air Fresheners da mayataccen ƙamahin turarensa alamar ya gitta falon. Baki ta tabe da nufar ƙasa. Kasancewar hankalinta na kan tab ɗin yasa bata kallon gabanta, so take ta fito a shop ɗin jiya amma har yau yaki, da alama shi yay hakan dan karta samu damar shiga ko ina.
“Good morning Aunty Queen!!”.
Su Zaidu dake kan dining suna karyawa suka haɗa baki wajen faɗa dai-dai Hibbah na taka step ɗin ƙarshe zata dire ƙafarta ƙasa tamkar wasu ɗaliban makaranta. Fasa saukar da kafar tai ta ɗago aɗan razane ta dubesu. Kawunansu sukai saurin maidawa ƙasa suka duƙar saboda harar da boss ya gallaro musu da ga inda yake zaune can gefen falon saman ɗaya daga cikin kujeru biyun da aka ajiye dan hutawa ta musamman yana ta faman sarrafa lap-top.
Fuska Hibba ta ƙwaɓe itama tana hararar su, dan sam bata lura da Master ba. “ALLAH idan baku daina cemin auntyn nan ba sai na haɗaku da jarababben uban gidankun nan da wata ɗaurarren face ɗinsa kamar mala’ikan ɗaukar rai.”
Idanu suka waro waje tare da saka hannu sukai saurin ɗorawa a saman bakunansu, saboda dariya dake neman kufce musu babu shiri. Yayinda ita kuma ta kaɗa kanta ta cigaba da tafiya fuska a kumbure. Turus taja ta tsaya saboda cin karo da wanda batai tunanin gani ba zaune a falon, duk da yayi tamkar baya jinsu sarai tasan duk abinda tace masa akan kunnensa ne. Ita kanta baba Saude dake daga kitchen dariya ta shigayi, yayinda wani sashe na zuciyarta ke ayyana mata (inama ace….)
Hibbah ta ɗan saci kallon fuskarsa da ke a tsuke ta ganta babu alamar rahama, wani irin sake tsargawa cikinta yayi, dan ta tabbatar zai iya mata walmakalifatu. Dabara ce tazo mata, dan haka cikin ɗan raunana murya da langaɓe kai gefe ita a dole kalar tausayi tace, “Yaya Master dama tab ɗinka ce na kawo maka ko zaka nema. Kuma na……”
Wani shegen kallo daya watso matane ya sakata saurin duƙewa ta riƙe ciki da faɗin, “Wayyo Ummi na cikina. Yaya Muhammad!!…”
Da sauri baba saude ta fito a kitchen, hakama su Khalid duk mikewa sukai duk zatonsu gaske takeyi tunda kansu a duƙe yake basuga harar da yay mata ba. Amma sunji mitace akan tab. Baba saude data ƙaraso ta kamata ta tayar tana jera mata sannu. saman doguwar kujera ta kaita duk ta rikice. Hakama su Habib falon suka nufo a rikice suna tambayarta dama bata da lafiya ne?.
Murƙususun ƙaryar da takeyine ya hanata basu amsa. Baba Saude dake a rikice ta dubi Master da yay kunnen uwar shegu da su kamarma baisan sunai ba. “Babana ko akwai wani maganine da zata sha a cikin maganinta?”.
Idanunsa ya ɗago a hankali ya dubi baba Sauden, kafin ya janye ya maida kan Hibbah data haƙiƙance ita ciwo cikinta ke mata da gaske. Lip ɗinsa yaɗan ciza ta gefe yana mikewa da ajiye lap-top ɗin saman table ɗin kujerun. Cikin halin ko in kula ya nufa inda suke cike da ƙasaita. Musbahu ya kalla a ƙasan maƙoshi yace, “Ɗakko min maganin feshin flowers ɗin nan a bata yana maganin ciwon ciki….”
“Kaji mugunta”.
Hibbah ta faɗa tana mikewa zaune dingangan. Ta dubi baba saude data wangame baki tana kallonta. “Baba wlhy so yake ya kasheni kawai mutumin nan dama ba ƙaunata yake ba”.
Babu shiri su Habib suka kwashe da dariya. Sai kuma sukai saurin gimtsewa saboda kallon da yay musu. Hibbah ta mike zumbur ganin ya nufota. Bayan baba Saude ta koma ta maƙale.
“Wayyo baba!, wayyo baba saude!!”…………✍
*_fajin he tsaho ike????????????????????_*
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????
#team ZAFAFA BIYAR????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*
[ad_2]