Uncategorized

TAKUN SAKA 35

     “Duk ku fita!!”.

Ɗaya da ga cikin ƴan sandan ya faɗa cikin daka tsawa. ALLAH ya taimakesu dukansu akwai hijjabai a jikinsu har Ummin, dan basu iya zuwa su zauna mata babu hijjab ko mayafi. kamar yanda itama idan suka shigo bata taɓa zama cikinsu babu mayafi ko hijjab tare da ita. Haka suka fita cikin matsanancin tashin hankalin rashin sanin laifinsu. Da ga su sai wayoyin hannunsu. A cikin mota guda aka zuba su Ummi. suma ƴan sandan suka shiga tasu.

★★★★

      A ɓangaren su Yaya Muhammad ma suna wajen ayyukansu cikin tashin hankalin abinda suka gani a labaran daketa yawo a wayoyin hannu. Zukatansu sun gama basu Hibbah ce ta tonama Isma’il asiri. Duk da suma har yanzu basu san ainahin gaskiyar dalilinsa na aikata waɗan nan abubuwanba hakan bai musu daɗi ba. A daren shekaran jiya yake sanar musu akwai aikin da yake kanyi yanzu haka, yana kammalawa zai kawo Hibbahr ta gaida Ummi. Sai gashi koma ya hargitse tunda gashi suma ta shafesu.

      Dan batare da sun san nasu laifin ba suma dai sai ga ƴan sanda sunzo kamasu suma. Hatta da Yaya Abubakar da ke matsayin jami’in tsaro suna tsaka da kai kawo akan abinda ke faruwar kawai akazo akai arresting ɗinsa. Ƴan sandan dake station ɗinsu sun so ɗaga hankalinsu Yaya Abubakar ɗin ya kwantar musu da hankali yabi jami’an farin kayan da sukazo kamasan. Dan shima a ransa yanason zuwa kodan wani bincike.

★★★★★

         Kusan awa ɗaya kenan da barin su Habib gidan amma babu su babu labarinsu. Gaba ɗaya su Idris sun kasa zaune sun kasa tsaye. Sai kaiwa da kawowa suke a falon hankalinsu nakan wayoyinsu suna ganin abinda ke faruwa ta yanar gizo. Basu kunna tv bane saboda fahimtar gaba ɗaya Master baya buƙatar wata hayaniya. Dan tun korar Hibbah da yay a wajen ya maida idanunsa ya lumshe kai kace barci yakeyi. Koda Khalid ma ya tambayesa ko zaisha tea bai tanka ba dan yayi zurfi matuƙa a tunani.

       “What!!?”

Khalid dake rike da waya a hannu ya ambata yana mikewa tsaye a zabure cikin alamun gigita. Idris dake zaune gefensa yay saurin dubansa da faɗin. “Lafiya?”.

      “Inafa lafiya!, wai kaji mi matsiyacin A.G ɗin nan ke faɗama ƴan jarida kuwa akan alaƙar Master da aunty queen?!”. 

        Hannunsa ya janye a kansa da ke masa tsananin ciyo, tare da buɗe lumsassun idanun ya sauke akan  Khalid da yay maganar. Kafin Idris dake ƙoƙarin buɗe baki yay magana yayi ɗin ya katsesu.

       Cikin muryarsa da ke a shaƙe na mura da tsananin ɓacin rai ya ce, “Television”. 

       Kai Khalid ya jinjina masa da ajiye wayar hannunsa ya ɗauka remote ɗin tv ya kuna. Hakan kuwa yayi dai-dai da hasko A.G da ke bayani ga ƴan jarida, da alama yabar wajen su alhajin Mande ya koma office.

            “Tabbas har yanzu babu wanda yasan fuskarsa. Saboda yana amfani da facemasks iri daban-daban idan zai aikata laifinsa. Misali kamar yau an samu fuska biyu da yaje banki da ita, inda mutane da yawa suka tabbatar da sun gansa a matsayin alhajin ƙauye daya shigo bankin tankar baisan komai ba. Sai a yanzu ne kowa ya fahimci shine yay shigar ɓurtu tamkar yanda ya saba. Tabbas mun bibiyesa adalilin yarinyarsa kuma har mun sami nasarar harbinsa. Sai dai yanzu-yanzun nan muke samun labari a majiya mai ƙarfi dangane da ita yarinyar da tai kiran ta sanar da inda yake. matarsa ce, soyayya sukai kuma kafin aure. Hakan na nufin ahalinta sun san wanene shi suka ɗauketa suka bashi. Dan a yanzu haka zancen da nake muku harda ƙanin mahaifin ita yarinyar dake dauke da ɗawainiyarsu tun suna kanana saboda mahaifinsu ya rasu suka yashema asusu. Kenan hakan na nufin harda ita a cikin tawagar tasa…….”

        “Amma yallaɓai idan harda ita mi zaisa ta tona masa asiri?”.

    Wani yayma A.G tambayar cikin katsalandan na ƴan jarida.

        A.G yaja numfashi, “Muma wannan itace tambayar da muke nemawa amsa. Sai dai a ganina kawai sun shirya mana wasa da hankaline kawai sai suka rufta..” 

       “Kenan dama kuna bibiyar al’amuransa a koda yaushe?”.

     “Sosai ma kuwa. Dan bamu da burin daya wuce mu kamashi. Shiyyasa dare da rana muke tsaye tuƙuru akan dukkan motsinsa…”

       “Amma yaya akai duk da jajircewar nan taku harya samu nasarar yashe asusan bankunanku kuma a yau?”.

      A.G ya kafe ɗan jaridan da yay tambayar da ido har saurayin ya tsargu. Ganin sauran ƴan jaridar na juyawa suna kallon saurayin saboda kallon da yake masa ya sashi basarwa yana sakin murmushi. “Tambaya mai ƙyau. Sai dai zan bada amsartane anan gaba bawai yanzu ba…”

       “Tabbas zaka amsata kuwa! Koda su sun manta ni Isma’il Aliyu Hikima zan sakaka ka amsata!!”.

      Master ya faɗa cikin wani irin kaushin murya da ɗaci yana sake maida idanunsa ya rufe. A haka ya cigaba da sauraren A.G daya ke tabbatarma da duniya a yanzu haka sun sami nasarar tattaro ahalin Hibbah, dan sune kaɗai zasu iya faɗama duniya a inda master yake a yanzu.

       Cikin tashin hankali su Khalid ke duban Master daya maida idanunsa ya rufe. Sun san sarai yana jin A.G ɗin shima. “Innalillahi…. Boss akwai matsala kenan”.

     Bai motsaba, bai kuma tanka ba duk da yaji abinda Idris ɗin yace. sai dai faman taunar lip ɗinsa yake na kasa alamar zuciyarsa na masa zafi da ciwo. Dan tsabar yanda yake taunar lip ɗin har ya koma jaa sosai.

         Shigowar baba saude da ke faɗa musu Hibbah fa babu lafiya jikinta sai rawa yake ga kuma zazzaɓi ya sakashi buɗe idanu a hankali. Kallon baba Sauden kawai yakeyi yana cizar lip. Su Idris kam duk sun zabura kan baba saude suna tambayarta miya sameta? ba yanzu ta shigaba lafiya lau.

     “Gaskiya inaga firgici ne. Da alama bata taɓa gamo da makamancin wannan tashin hankalin ba. Tunda ta shiga fa sai surutai takeyi. Maida idanun yay ya lumshe, gaba ɗaya kansa ciwo yake masa tamkar zai buga.

       Jin yaƙi cewa komai yasa sukai tsuru-tsuru suna kallonsa. Musamman ma su Khalid. Ganin haka yada Baba Saude takowa ta ƙaraso inda yake. Cikin taushin murya tace, “Babana ko jikin ne?”.

     Idanunsa ya sake buɗewa, yanda suka sake kaɗawa sukai ja har kamar suna ƙyallin ruwa sai ka ɗauka kuka yake. Yay ɗan murmushi mai ciwo yana girgizama baba sauden kansa. 

       “Naji sauƙi baba, kice mata tazo nan”. Yay maganar acan ƙasan maƙoshi cikin rauni da ɗacin dake addabar zuciyarsa da maƙoshinsa.

        Baba saude da gaba ɗaya itama zuciyarta ta ƙara raunana. Ta kaɗa masa kai da juyawa ta koma. Babu jimawa kuwa sai gata ta fito riƙe da hannun Hibbah da kallo ɗaya zakai mata ta baka matuƙar tausayi. Duk ta susuce ta firgice. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunta sun kumburo matuƙa, jijiyoyin kanta duk sun miƙe ruɗu-ruɗu. Duk da haushinta da su Khalid ke ji sai wani irin tausayinta ya kamasu. Suka shiga jera mata sannu cike da damuwa. Bata iya ta amsa musu ba, dan gaba ɗaya a yanda Hibbahn take ta fita hayyacinta ba lallaine ma tana fahimtarsu ba.

      Shi kansa master tunda baba Saude ta zaunar da ita gefensa ya buɗe idanu ya kalleta sai da tsigar jikinsa ya tashi. Yaja numfashi batare da ya ce komai ba ya maida dubansa ga baba Saude. “Baba kije abinki kawai”.

      “To babana, amma babu wani abinda kuke buƙata?”.

     Kansa ya jinjina mata kawai. Sai kuma ya maida dubansa ga su Khalid.  “Tea da bargo”. Ya faɗa a taƙaice dan baya son yawan maganar. 

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button