TAKUN SAKA 36

“Yaron waye?”.
Master ya tambaya yana kafe Musbahu da ido. Adam ne ya bashi amsa da cewar, “Kamar dai yaron Engineer ne”.
Komai Master bai sake cewa ba, sai hannu da ya miƙama Habib da ke riƙe da lap-top ɗinsa. Cikin sauri Habib ya buɗe lap-top ɗin ya kunna ya miƙa masa. Filo ya sa a cinyarsa sannan ya ɗaura system ɗin. Sai kuma yay ma Adam nuni da jakkar da sukazo da ita na wayoyi. Jakar ya zuge ya zazzage wayoyin a saman table ɗin. Komai Master bai ce ba ya miƙa hannu ya ɗauka ɗaya da ga cikin wayoyin ya jujjuya a hannunsa. Kamar zai kunna sai kuma ya fasa ya ajiyeta. Wayarsa da ke a gefen damarsa ya ɗauka, ya ɗanyi danne-danne tare da kaiwa kunnensa ya lumshe ido da kwantar da bayansa jikin kujera jin ta shiga.
Duk sake nutsiwa su Habib sukai da tunanin wa yake kira a cikin wannan ruguntsumin kuma?. Rashin samun amsa ya sakasu nutsuwa a saurarensa.
Wayar na gab da tsinkewa aka daga. Shiru baice komaiba. Takaici ya saka A.G dake can faɗin, “Waye ke magana?”.
Wani lalataccen murmushin gefen baki ya saki, cike da izzarsa da ƙasaita yace, “Master!!”.
Duk da sunan ya daki zuciyar A.G sai ya dake, harda saki wata dariyar gatsatsa wadda tafi kuka ciwo. “Hhhh karen farauta! kai har kana da zarrar ɗaga waya ka kira wani a cikinmu a wannan lokacin kenan? Kako san su wanene mu kuwa?”.
Master ya sake sakin murmushi a karo na biyu da gyara zamansa. “Sai da na sanku ma sannan na fara wasan kaima kasan wannan”.
A.G da kejin zuciyarsa tamkar zata faso ƙirjinta ta fito ya rumtse idanu da ƙarfi batare da ya tuna a tsakkiyar jami’an tsaro yake ba, dan meeting sukeyi akan Master ɗin ya ce, “Kai kare! Idan damar da ka samu a baya kake tunanin tana hannunka har yanzu to ka sani rayuwarka ta ƙare a wannan gaɓar.”
A bazata su Habib sukaga Master ya ƙyalƙyale da dariya, sai kuma ya haɗe fuskar cikin kaushi da barazanarsa ya cigaba da magana.
“A.G! A.G! Na master. Shin ba kune kukace ɓoyayyen wasa bane ba babban jami’i mai gaskiya?. Ya da tada jijiyar wuya tun a farkon karo haka?………”
A fusace A.G ya miƙe yana buga table ɗin batare da ya tuna a inda yake ba. “Kai tsinanne, ka sani duk randa kazo hannu ni ɗin nan da hannuna zanyi gunduwa-gunduwa da namanka na bama karnukan farauta da suka fika giyata su cinye namanka a tsakkiyar kasuwa!!”.
“Tofa babbar magana, wai da wuri haka har ka fara fusata?. Nifa ta ɓangare ɗaya kawai na fara buga wasan a yanzu, amm har kake tada jijiyar wuya da ɗaukar alwashi kamar haka. To kwantar da hankalinka dan bamma fara komai ba, yanzu ma na kiraka ne danna sanar maka tarkacenku na hannuna, a kuma daren yau wasu a ciki zasu iya tsallakawa barzahu, gawawwakinsu kuma zasu iya zuwa maku ƙarfe biyar ɗin asubahi. Ku shirya dakatar da hakan ta dawo min da ahalin MATATA. Sannan ku tabbatar kun lashe aman da kukai na kalamaku daga nan zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu, daga nanne sai ai wasan fili ba TAKUN SAƘA ba. Umarnine ba shawara ko neman alfarma ba..”
Ya katse kiran da jefar da wayar gefensa yana cija lebensa na ƙasa da haƙori tamkar zai huda shi. Sai kuma ya buɗe jajayen idanunsa dake fusace ya dubi su Salis da sukai tsuru-tsuru.
“Kuje ku huta, zuwa dare ku tattara min dukan bayanai akan maganganun su A.G da duk wani mai faɗa aji da ya fito yay magana. Salis ka turama Faisal cewar ya kawo saƙon nan, sannan ya faɗama *_WALƘIYA yayi barci a farkon dare, ya farka a farar asubahi. Kar yay baƙin ciki akan rubutacciyar ƙaddara, farautar *MASTER* ba wawaso akan naman shanu bane. Masu tambari a bayan ƙeya sun tabbatar da shiryawarsu tunda suka bayyana wasan a fili. Ya shirya dan yanzune TAKUN SAƘA zai fara”_*.
A tare suka ƙame jikinsu da salute nasa. Fuskokinsu washe da fara’a suka hada baki wajen faɗin, “Yes master!!”.
Wani shegen lalataccen shu’umin murmushi ya saki a karon farko da ɗaga lumsassun idanunsa ya dubesu. Tausayin ƙannen nasa kuma ahalinsa a halin yanzu na ratsashi, a hankali ya buɗe hannayensa ya mika musu alamar suzo garesa saboda yanda duk suka koma kalar tausayi a dalilin halin da yake ciki, baya son ganinsu cikin damuwa sam. Cikin ɗoki da zumuɗi suka nufo jikinsa batare da sun yarda sun fama masa ciwukansaba saboda tsabar taka tsantsan ɗinsu garesa. Ya haɗiye hawayen da suka ciko masa idanu cikin muryarsa da ke bayyana kaushinsa da ƙaunarsu ya furta, “I love you so much my sweet Brothers. ALLAH yay muku albarka.”
Hawayen dake bin fuskokinsu suka shiga sharewa kamar yanda suka saba a duk lokacin da ya furta tsananin kaunar da yake a garesu. Cikin haɗa baki suma suka shiga sanar masa da ɗunbin ƙauna da soyayyar da suke masa har cikin ruhi da ɓargo. Irin wadda gaba ɗayansu suke jinsa a ransu tamkar mahaifi. Dan ya ɗaukesu lokacin da nasu iyayen suka jefar da su. Ya raineso lokacin da iyayensu suka nisancesu. Ya kaunacesu lokacin da iyayensu suka manta da su. Ya basu tarbiyya lokacin da iyayensu suka toshe idanunsu da kunnuwansu. Ya inganta rayuwarsu lokacin da iyayensu suka nuna gazawa da su. Ya yalwata farin cikinsu tamkar yanda kowaɗannen iyayen ƙwarai suke yalwata na ƴaƴayensu da basu gata. Bai taɓa banbantasu da Habib ba balle nuna ya fisu a gareshi.
“Bana son kuka”.
Ya faɗa a hankali yana shafa kawunansu da hanunsa mara ciwo tare da ɗan jan kunen Salis dake gefen damarsa cikin salon da yake musu punishment tun suna yara idan sun masa laifi. Dariya suka sanya dukansu suna share hawayen. Kafin su miƙe kowanne ya manna masa kiss a gefen kumatunsa, dan wannan itace fuskar da suke ɗauka real face ɗinsa saboda ita suka taso suka sanshi da ita. Hakan ya sakashi sakin murmushi ƙarfin hali. Tausayinsu na ratsashi da tarin ƙaunarsu. Sune ahalinsa, sune farin cikinsa, sune raunin sa, sune… Sune… Sunee…. Da yawan da babu adadin kididdiga.
★★★
Gaba ɗaya A.G ya birkice, jiya yake tamkar ya jawo Master ta cikin wayar. Su kansu sauran jami’an kallon mamakin rikicewar tasa suke duk da sun san cewa mastern yay masa illa. Cikin gaggawa aka fara bibiyar lambar da yay kiran. Sai dai kash babu wata hanyar da za’a iya samun sa.
A.G da gaba ɗaya jikinsa ke matukar rawa ya fice tare da wasu jami’an domin tabbatar da zancen master ɗin. Cikin lokaci ƙanƙani hukumar ƴan sandan ta sake rikicewa. Suma su Alhajin Mande aka fara kiran wayoyinsu domin ji da ga garesu….
★★
A ɓangaren Abba kam sai da suka zuba masa ruwa sosai ya farfaɗo. Koda ya buɗe ido ya kallesu tsaitsaye a kansa sai ya fashe da kuka. Cikin mamaki da tsoro suke dubansa. Hajiya mama da zuciyarta ke tsitstsinkewa da tunanin waye kuma ya rasu tace, “Halilu kabar mana wannan kukan ka sanar min wanene ya rasu ne?”.
Sake fashewa yay da wani sabon kuka saboda jin abinda hajiya mama ta faɗa. Sai kuma ya rarumo wayarsa batare da ya bata amsa ba. Number A.G ya shiga nema amma kuma ya gagara samu. Sai busy take nuna masa. Ya maida akalar kiran kan Alhaji Balele. Sai da tana gab da tsinkewa ya ɗaga. Ɗan gidan Alhaji Balele da ya ɗaga wayar cikin kuka da ga can yake sanarma Abba ai suna asibiti, tunda yaga yasar da Master yay masa shima ya yanke jiki ya faɗi. A yanzu haka ma likita ya sanar musu paralysis ta kama shi.