TAKUN SAKA 36

Rawa jikin Abba ya kamayi, sai kuma ya fashe da sabon kuka yana jeroma Master tagwayen ALLAH ya isa da tsinuwar alkaba’i kala-kala. Takaici yasa Momy fisgar wayar a hannunsa ta fara dubawa. Dan yaki musu bayanin da zasu fahimta gashi yana rusar kuka tamkar wani ƙaramin yaro.
Komai bata fahimta ba, dan haka ta dangwarar masa da wayar tana jan tsaki tabar wajen, hakan yasa suma su Ameera bin bayan uwarsu suma cikin takaici suka bar Hajiya mama ita kaɗai tsaye akan Abba.
Sai daga baya suka fahimci abinda ke faruwa ta hanyar kunna tv. Hankalinsu ya tashi suma matuƙa. Dan a take momy ma tai zaman ƴan bori da ƙwala ihu. “Na shiga Uku dadyn Junaid kai ko miya haɗaka da Master har ka shiga lissafinsa?”.
“Tsautsayi!. Wlhy Tsautsayi ne ni Halilu na shiga uku. A.G ka gama da rayuwata. Nayi dana sanin sanin matsiyacin yaron nan mai kama da bokan tsauni”.
*_________________________*
Har zuwa yammaci abu ɗaya ke maimaita kansa a kowacce kafa ta yanar gizo da kafafen yaɗa labarai. Manyan masu fashin baƙi nata famanyi tare da jami’an tsaro da jama’ar gari ƴan bani na iya. Babu wanda yasan da ga ina hoton Hibbah da ahalinta ya fito sai gashi yana yawo. Master dai babu ma wanda ya sansa balle ya fidda hoton nashi. Sai dai hotunansa na ɓadda kama da keta yawo wanda yake a cikin fuskoki kala-kala da ko yatsansa ba’a gani.
Ana tsaka da wannan kace nace kuma sai ga sabon zance ya fito da ga su A.G cewa anyi kidnapping ahalinsu har gida. Hatta da ma’aikatan gidansu ba’a bari ba sai masu gadi kawai.. Dan shi A.G ma securitys ɗin da ke a gidansa suna bada tsaro saboda kasancewarsa babban jami’i kansu an kwashe harda su.
Komai ya sake tashi sabo anata kace nace na hasashen dalilin yin hakan da Master yayi, sai dai abinda ke ba mutane mamaki a wannan gaɓar miyasa Master ɗin zaiyi hakan? Tunda kowa yasan a baya iyakarsa satar kuɗi ba’a taɓa jinsa da yin garkuwa da mutane ba.
A gefe kuma na manya irinsu A.G da wasu kasashen ƙetare na ƴan bani na iya har wasu na iƙirarin saka sunan Master ɗin a jeren ƴan ta’adda na duniya. Sun kawo hujjoji da dama na cewar hakan da hasashensu ya basu. Musamman da a wannan karon al’amarin nasa ya fito fili da kuma sabon salo. Sai kuma hasashen yana da yara masu masa aiki a wajeje daban-daban.
Har zuwa dare dai Master bai sake cewa komai ba tun wayarsa da A.G. Duk da kuwa yana ta bibiyar shafukan sada zumunta da ganin dukkan labaran da ke yawo duk da tsananin buƙatar son hutu da yake a ciki. Ga mura da ke nuƙurkusar rayuwarsa har yanzu. Ya jima zaune a falon salla kawai ke tashinsa har isha’i. Sai da su Zaidu suka fito suna masa shagwaɓar yunwa sukeji sannan.
Da farko bai kulasu ba. Sai da yaga zasu addabi rayuwarsa dan su a ɓangaren ci babu wasa ne, sannan ya ɗauka waya yay musu order ɗin abinci yana hararsu. Tattare kayansa yay ya barsu a falon. Duk da baice musu komai ba sun san za’a kawo abincin.
Koda ya koma ɗakin kwance ya tadda Hibbah a tsakiyar gadon ta ƙudindine. Sai dai da alama ta tashi tayi dukkan salloli. Daga tsayen da yake ya kai hannunsa mai ciyo ya ɗan janye bargon data lulluɓa har akan fuska. Barci takeyi. sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci bana jin daɗi bane. dan ta wani nannaɗe kanta a waje guda kamar wadda take a firgice. Kusan kallon mintuna huɗu yay mata kafin ya janye idanunsa yana furzar da iska mai ɗaci.
Toilet ya shiga yay abinda zaiyi ya fito yai shirin barci. Zama yay a gefen gadon kusan mintuna goma yana kallon Hibbah da sauraren hayaniyar su Idris da alamu ya nuna an kawo musu abincin. Sai kuma ya zame a hankali ya kwanta yana matse fuska alamar dai bayajin daɗi sosai. Kwanciya yay a rigingine ya lumshe idanunsa, tare da harɗe hannayensa a ƙirji ya lula duniyar tunani.
A yanda yake ɗin sai ka ɗauka barci yake, sai dai yanda yake murza babban yatsan kafarsa dana kusa da shi zaisa kasan ido biyu yake ran mazane a wuya kawai. Shi mutum ne mai matuƙar fushi da zafi idan aka ɓata masa rai. Shiyya su Habib kanyi matuƙar taka tsantsan da shi idan yana a cikin irin wannan halin. Ya jima a haka yana ƙullawa da kwancewa akan shirinsa na safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu kafin barci ɓarawo ya sace sa.
*_WASHE GARI_*
A safiyar yau tamkar yanda ya tsara ya fidda video a karon farko na tarihin rayuwarsa. Video ne da ya ƙunshi abubuwa da yawa da suka danganci jerarrun tambayoyi da ga kalaman su A.G ɗaya bayan ɗaya. Dama duk wani babba da ya fito ya tofa albarkacin bakinsa dan gane da abinda ya faru jiya.
Da ga ƙarshe ya rufe da faɗin, “Ina da abin cewa da yawa, amma bazan ce ba, saboda lokacin cewar baiyi ba. Sai dai inason kamar yanda nai tambayoyin nan ga duk waɗan da na ambata su amsa min su. Da ga ƙarshe ina mai tuna muku acikin awa ashirin da huɗu saura awanni goma sha ɗaya suka rage muku akan ahalinku, Idan har kuna buƙatarsu ku sakarmin nawa nima na baku naku, dan ko ƙwarzane ya samu ɗaya daga cikinsu babu fashi sai na rama. Dan Master baya yafiya wa abokin gaba koda akan harara ne…………????
(Tofa turƙashi, bara mu kama kanmu kenan master).
*_Ku sani a addu’a na bar posting dare ɗin nan????????????????????_*
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????
#team ZAFAFA BIYAR????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*
[ad_2]