Uncategorized

TAKUN SAKA 43

        Murmushi Hibbah tai da kaiwa zaune a kujerar da ke kusa da ita. Cikin girmamawa ta shiga gaida shi. Shima amsa mata yay da kulawa yana kallon Master da ya cigaba da shan coffee ɗinsa yana saurarensu. 

      “Amarya yaya kina kulamin da bestie na sosai ko?”.

      Murmushi tayi, dan gaba ɗaya jitai kunya ta dabaibayeta. Sai take ganin kamar kowa zai iya fahimtar halin da take ciki tsakaninta da Master yanzun. Shi dai Abdull ya cigaba da tsokanarta ne. Yayinda ita kuma ta kasa amsawa dan kunya. Sai da ya gaji dan kansa ya barta. Master dai bai tanka musu ba har sai da Abdull ɗin yay shiru sannan ya duba Hibbahn, saboda nutsuwar tata yay masa daɗi. 

      “Muhibbah!”.

Ya kira sunanta a hankali. Ɗan ɗagowa tai ta dubesa da amsa masa. Ganin ita yake kallo ya sata sake maida kanta ƙasan.

     Ya ɗan sake kwantar da bayansa jikin kujera yana kallon nata. “Wannan sunansa Abdul-Hakim. Aminina ne kuma ɗan uwana. Likita ne a yanzu haka yana zaune a canada tare da iyalinsa da yaransa biyu”.

       Jin yayi shiru ne yasa Hibbah jinjina masa kanta. Tace, “Masha ALLAH Yaya sannu da zuwa. Ka baro su lafiya?”.

           Abdull da Hibbahr ta birge ba kamar yanda yake tunanin ganintaba yay murmushi, “A lallai na samu ƙanwa kenan. To ina godiya sosai Muhibbat. Suna lafiya, suna kuma gaisheki”.

      “Nagode ina amsawa”.

  “Nima nagode sosai da samun tarba daga gareki”.

        Kanta kawai ta jinjina masa tana miƙewa. Rasa madafar ina zata dosa ya sakata nufar kitchen, a yanda ta samu kitchen ɗin sai kawai ya birgeta taji sha’awar yin abinci a ciki. Ƙofar baya ta fita ta kitchen ɗin, wadda daga nan babu nisa da sashen su Habib. Babu wani tunani ta nufi can. Sai dai bata samu kowa ba sai baba Saude da taji daɗin ganinta. Dan sai tambayoyi take mata akan yaya take? Ina ta shiga? Yaya jikinta?.

     Hibbah da itama tai kewarta harsu Habib ɗin ma da Sharifat ta amsa mata cike da girmamawa. Daga nanne suka ɗan taɓa hira har Hibbah ta sakko zancen sonyin girkin amma ta duba a can sashen babu kayan abinci.

     Karan farko da baba Saude taji aranta kodai akwai alaƙa ta aure tsakanin Master da Hibbah ne? Kamar zata tambaya dai sai tai shiru. Sai ma sanar mata da tai cewar gama breakfast ɗinsu nan tun ɗazun take jiran shigowar su Salis sukai amma babu wanda ya shigo tun fitar safe da sukayi.

       A nutse Hibbah ta amsa mata har baba Saude na mamakin yanda ta canja mata a ƙanƙanin lokaci. Sai dai ta danne a ranta ta bita da kallo harta fice.

     Koda ta dawo sashen nasu a yanda ta fito ta kitchen da babban tray ɗin sai Abdull yay tunanin ita ta haɗo musu abincin, Master dai da kallon mamaki ya bita amma sai baiyi magana ba harta kai trayn ajiye saman centre table. Ɗan ɗagowa tai ta dubesa. “Ko akai muku dining?”.

       Tsabar mamakin daya rufesa da ƙyar ya iya kaɗa mata Kansa. Kafin ya iya motsa laɓɓa da ƙyar yace, “Nan ma yayi sannu da ƙoƙari”.

      Kanta kawai ta kaɗa masa tabar wajen, kitchen ta koma ta haɗo duk abinda zasu iya buƙata ta ɗauraye ta sake kawowa, kafin ta koma ta ɗauka ledan jiya data gani cikin fridge. Chocolates ne a ciki sai naman da ko taɓashi basuyi ba. Sai roban ice-cream guda ɗaya data rage. Chocolates ɗin ta ɗiba guda uku ta ɗauka naman ta koma sashen su Habib.

         Yanzun kam ta iske sun dawo, dan tana shiga suka haɗa baki wajen gaisheta da kiranta aunty Queen kamar yanda suka saba. Harararsu tayi itama kamar yanda ta saba ɗin, kafin takai zaune kusa da baba Saude tana ɓare ledan chocolate ɗaya ta kai baki. Koda suka cigaba da hira sunsha matuƙar mamakin yanda take amsa musu a nutse tamkar ba ita ba, hakan yasasu fahimtar dama tsiwa ce ke damun bakinta kawai badan batasan komaiba ko bata da nutsuwa ne. Habib ma tun yana ɗan basar da ita harya saki jikinsa kuma. Itako tayi mirsisi tamkar ma bataga yana fushin ba.

       

          Har akai sallar azhar Hibbah na nan tare da su Musbahu. Sallar ma a ɗakin baba Saude tayi abinta. Bayan sun idar kuma ta bita suka shiga kitchen tare sukai girki mai sauƙi. Baba Saude ta haɗa na master tamkar yanda ta saba.

      “Ɗiyata ga abincin mijinki ko”.

Tai maganar cike da son bugar cikin Hibbahr. Har ko cikin rai Hibbah taji kunyar kalmar mijin nan. Tai ƙasa da kanta cikin sabon sanyin daya saukar mata ta ce, “To baba”.

      Kafeta da idanu kawai baba Saude tai cike da mamaki fal ranta. Kenan dai hasashenta ya zama gaskiya aure ne tsakanin Master da Hibbahn. Sai taji wani farin ciki ya baibaye zuciyarta harta kasa ɓoyewa sai da ta tanka. “Oh ni ƴar nan, dama babana mijinki ne amma kuketa ɓoye-ɓoye?”.

        Da sauri Hibbah ta ɗauka trayn abincin ta fice tana murmushi. Baba Saude ta ɗaga hannu sama tana ma ALLAH godiya da wannan haɗi, dan ɗari bisa ɗari taga dacewar wannan ma’aurata. Ta kumayi farin ciki matuƙa.

         Hibbah ko data koma sashensu ta iske su Master basu dawo ba da ga salla da suka fita. A dining ta ajiye musu abincin yanzu kam, ta tattare falon da kwanikan da sukai amfani na ɗazun. Kitchen ta kai ta wanke. Tana tsaka da goge inda tai wanke-wanken taji ƙamshin turarensa.

    Jiyowa tai ta duba ƙofan dan bataji takunsa ba. Ido suka haɗa yana tsaye jikin ƙofa ya harɗe hannaye a ƙirjinsa yana kallonta. Hararar sa tai kaɗan da ɗauke kanta. “Ni dai abar kallona gaskiya”.

        “Ai sadaki na na kalla”.

Ya bata amsa da ɗage gira sama duk da ba kallonsa take ba. Hibbah dake cigaba da aikinta tai murmushi kawai. Cikin son kauda zancen nasa da idanunsa dake binta da mayataccen kallo ta ce, “Ga abinci can a dining kai da baƙo”.

     Hannayensa ya warware daga ƙirjinsa ya ƙarasa takowa cikin kitchen ɗin, ta ɗan gefenta kaɗan ya tsaya tare da jingina da jikin kitchen cabinet ɗin yana kallonta. “Da gaske autar Ummi tayi hankali irin na kowace mata a gidan miji, nagode sosai da kika fiddani kunya Hibbaty”.

        Hibbah dai bata yarda ta kallesa ba, amma taji daɗin ganin yanda ya nuna jin daɗinsa akan abinda tayi badan tayi tunanin tayi dai-dai ba…..

        Katse mata tunani yay da faɗin, “Ki shirya idan mun kammala zamuje anguwa”.

        Ɗagowa tai ta dubesa cikin wani irin shauƙi da zumuɗi. “Dan ALLAH da gaske Yaya?”.

       Kansa ya jinjina mata, “Sosai ma kuwa. Ai na cancanci bada tukuyci bisa ƙyautar dana samu mai ɗunbin daraja baby luv”.

             Kafimma ya rufe baki ta nufi ƙofa da sauri zata fice. Yay azamar riƙota ganin tana neman kaiwa ƙasa dan zumuɗi.

       “oh-ouh nifa a dinga kula saboda ɗan tayina bai gama zama da ƙyau ba”.

     Ba wani fahimtar zancen ɗan tayin nan take ba, dan haka ta amsa masa da “to”, dan so take ya saketa ta tafi tai shiri. Fahimtar hakan da yay ne shima ya sashi sakin nata kawai. Amma yayi gaba ta bisa a baya. Waya suka iske Abdull nayi, dan haka Hibbah tai bedroom harda haɗawa da ɗan gudinta…………✍

*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button