Uncategorized

TAKUN SAKA 42

 *_Chapter Forty Two_*………..Har cikin ransa sai da yaji shock dan bai zaton hakan ba da ga gareta cikin sauƙi. Sai dai idan yayi dubi da tarbiyanta da yanda ta tashi za’a iya mata koda wayone da yaudara ta amince. Idanunsa ya lumshe tare da riƙe hannuwan nata yana murmushi, ya rungumeta da ƙyau shima yana jerama UBANGIJI godiya, dan jinsa yake tamkar ya sauke wasu kaya masu nauyi dake bisa kansa.

         Muhibbat da gaba ɗaya ta kasa tsaida kukanta ta sake yunƙurin barin jikin nasa. 

        “I’m sorry Hibbaty”. 

    Ya faɗa cikin kunnenta yana sake matseta da busa mata iskar numfashinsa cikin kunnen dake tada mata tsigar jiki..

      “Ni ka sakeni, wajen Ummina zanje, karka sake shiga sabgata kuma. Karka sake zuwa mana gida.”

         Cikin gimtse dariyarsa ya ɗagota da riƙe fuskarta cikin tafukan hannunsa. “Buɗe idanun mana ki kalli cikin nawa ki faɗa. Kefa kikace da Isma’il zaki zauna, taya kike tunanin kunnen Isma’il yaji wannan zance yay sakacin barinki kiyi nesa da shi kuma?”.

          Sake matse idanun tayi hawaye na zirarowa. Batare data iya buɗesu ba tace, “To na fasa. Yanzu bazan zauna da kai ba”.

        “Shi kuma babyna kimin yaya da shi? Dan bazaije ko ina ba a gidansu zai tashi”.

         Babu shiri ta buɗe idanun sai dai bata kallesa ba. Cikin motsawar sakarcin nata tace, “Ni yaushe naga wani babyn ka balle na rakitama kaina har yaje gidanmu”.

      Hannunsa ya ɗaura a saman cikinta yana ƙasa da shi a hankali, cikin muryar raɗa ya ce, “Gashi anan insha ALLAH, zaki gansane kema soon”.

             Hanunsa ta ture da faɗin, “ALLAH ya kiyaye”.

      “Na yanzu kam ya faru sai dai ya kiyaye na gaba kuma”. Ya bata amsa yana kwantar da ita shima ya kwanta a gefenta. Duk yanda taso tashi kuma ya hana dole ta haƙura. Sai dai ta masa shiru bata sake tankawa ba. Shima gajiya da suruntunne ya sashi rufe idanunsa da fatan samun barci.

     Koda suka tashi wajen sha ɗaya duk yanda Hibbah taso zillewa hanata yayi tare sukai wanka. Ta gama ƴan koke-kokenta na shagwaɓa ta bari. Breakfast ma tare sukayi, tanason taje gaida baba Saude ya hanata. Dole ta haƙura tanata faman sinne kai dan sam bata buƙatar su haɗa ido. Sai dai dukan motsinsa saita bisa da kallo, har yanzu zuciyarta na kaikawo akan kasancewarsa Isma’il kuma Master. Sarai yana lure da ita amma sai ya basar yanata aikinsa tana gefensa. Lokaci-lokaci yakan sakata tai masa wani aikin. 

      A yau dai komai yinsa take babu musu ko tsiwa, dan idan ka ganta bazaka taɓa ɗauka Hibbahn Ummi da su Yaya Ammar bace. Haka suka kasance har yamma salla ce kawai ke tashinsu. Abinci ma da aka kawo na rana catai ta ƙoshi. Shima kuma baici ba dan bayajin daɗin bakinsa tamkar ita. Har dare bai fita ko inaba yanata aiki, sai bayan sallar isha’i ne Habib ya shigo musu da ledar kayan kwaɗayin da suka fita yawo suka siyo. Koda ya shigo falon Hibbah na kwance a doguwar kujeran da Master ke aiki kanta a saman cinyarsa. Dan ta kwanta tai filo da hanun kujerar ya taso daga inda yake zaune ya ɗagota yasa kan nata saman cinyarsa. Duk yanda taso tashi kuma bai bata fuska ba dole ta haƙura ta kwanta ƙamshin turarensa na mamaye kwanyarta a hankali. Aikinsa yake ita kuma tana kwance idanu a rufe ta lula duniyar tunani.

      Koda Habib ɗin ya shigo bayan ya amsa masa sallamar da bashi iznin shiga kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa zuciyarsa na masa wani fari fat. Kayan ya ajiye yana masa sannu da aiki.

          Amsawa yay yana ɗago idanu ya kalli ledar, sai kuma ya maida dubansa ga Habib ɗin. 

         Da sauri Habib yace, “Na aunty Queen ne, sai da safe”.

       Kafin ma master yace wani abu tuni ya fice. Kansa ya ɗan girgiza da maida dubansa ga Hibbah da duk take jinsu amma tayi luf. Ganin bata motsaba komai baice ba ya cigaba da aikinsa. Sai zuwa can da yaga barci na meman dibarta ne ya ajiye aikin yana buɗe ledan. Gasashshen namane mai romo da ice-cream. Sai Haɗaɗɗun chocolates masu daɗi. Roban ice-cream ɗin ya ɗauka ya buɗe. Dan shima ma’abocin sonshi ne. Batare da yayi magana ba ya ɗiba yakai baki. 

       Hibbah dake sauraren taji yace ta tashi ta hadiye yawu da ƙyar. Jin alamar ya ƙara kaiwa baki yasata buɗe idanunta da miƙewa zaune. Hannu tasa ta warce roban tana ɗan hararsa ƙasa-ƙasa da ƙunkuni.

      “Ai nidai banji ance nakaba amma ka hau kai da sha”.

         Gira ɗaya ya ɗauke yana sauke mata wani shu’umin kallo. “Naga kamar baki da ra’ayine shiyyasa nace bara na maida jinina da kika tsotse jiya da wanda kikasa bindiga ta zubarmin”.

        Baki taɗan murguɗa gefe da kai cokalin ice-cream ɗin zata sha ya kai hannu zai riƙe ta tura da sauri. 

     “Humm rowa ko?”.

  Kumburarrun idanunta ta ɗan juya masa “Kai da baka da rowar ka taɓa siyamin ne?”.

       Master daya shagala a kallonta har tana saka tsigar jikinsa tashi ya ɗan waro idanu kaɗan. “Aunty Queen kiji tsoron ALLAH ban sayo miki kazan first night ba randa aka kawoki?”.

          “Kadai satoni! Kuma ni babu wata kaza daka sayamin”.

        Dariya ta bashi, amma sai ya gimtse yay murmushi kawai. “Ai ke amaryace ta musamman, shiyyasa kaiki gidan mijinki ma ya zama na musamman.”.

      Yay maganar da ɗan kwantowa jikin kafaɗarta yana wani sassanyan murmushi idanunsa akanta. Matsawa taso yi ya tura hanunsa ta bayanta ya riƙo ƙugunta. Cikin marairaicewa yace, “Ki sammin ko kaɗan mana, inba hakaba kuma a daren nan na ɗiba rabona a can”.

        Sam Hibbah bata fahimci a ina zai ɗiba rabon nasa ba. Dan haka ta sake juya kanta gefe tana kaiwa baki da faɗin, “Gara kaje ka ɗiba rabon naka a can amma ba nan ba”.

       Wata ƴar dariyar ƙeta yay da ɗaura hanunsa saman ƙirjinta, “Ina godiya sarauniyar gidanmu”.

     Da sauri ta ture hannunsa har tana neman sakin robar ice-cream ɗin ya riƙo da sauri. Kafin tayi wani yunkuri ya miƙe zaune sosai da fige ɗan spoon ɗin ya juya mata baya. Shaf ta manta da wanda take tare, ta ɗane bayansa cikin shagwaɓa tace, “Ummi kin gansa ko”.

       Ice-cream ɗin ya dinga ɗiba yana kaiwa baki da kakkauce mata. Itako ta maƙalƙalesa ta baya da daura kanta a saman wuyansa tana son amsa amma ta kasa. Master da ke sha da sauri-sauri ya fara ƴar dariya mara sauti da batai zaton ya iya ba. Ganin yasha kusan rabi yasata barin bayansa ta sakko da sauri a kujerar taje gabansa zata warce ya kauce ta faɗa jikinsa. Zaune tai ɗare-ɗare bisa cinyarsa. “Ni wlhy ka bani abuna, ai dai baice naka bane, nawa yace”.

       Master dake murmushi ya sake kaiwa bakinsa da ajiye robar ta gefen kanta batare data sani ba. Ta buɗe baki zata sake magana ya haɗe bakin nata da nasa ya fara juye mata ice-cream ɗin daya gama narkewa a cikin bakinsa. Bata da wata mafita saita shanyewa. Dan ganin tana son ture masa fuska ya sashin toshe mata hanci dole ta haɗiye. Koda ya saki hancin bai saki bakinba ya zarce da kissing ɗin ta. A salon da yake sumbatar natane ya sata nutsuwar dole tana amsar sakonsa. Sai da taji hannunsa cikin rigarta ne tai ƙoƙarin turesa jikinta na fara rawa.

        Matsar da bakin yay yakai saitin kunnenta yana sake rungumota da ƙyau. “Kemafa yarinyar nan na kula fitinanniya za’ai. Dan sosai jikinki ke amsar kowanne saƙo”.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button