TAKUN SAKA 44

Ganin yanda hajiya maman taƙi nutsuwa ya sakasu banka mata maganin barcin itama dan bazasu iya da kwakwazonta ba. suna ganin ta tafi sukai kama-kama suka kaita ɗakinta suka zubar a gado suka fito. Abban ma maganin barcin suka ɗirka masa dansu sami lafiya.
Wannan abu daya faru a jiyane ya saka ƙafafun Hajiya mama kumbura suntum kafin safiya, dan kuwa dai da gaske taji ciwo a ƙugunta. Hankalin su momy yaɗan tashi sai dai basu wani damuba. Dan sukam dai dama tsohuwar ta gallabi rayuwarsu da hanasu rawar gaban hantsi komai saita saka baki. Suna tsaka da jajanta yanda zasuyi da hajiya mamar sai ga yaran su A.G wai sunzo kai Abba asibiti. Jin hakane yasa su momy cewar a haɗa da hajiya mama. Da farko sunƙi yarda dan Halilu kawai akace su ɗakko. Sai dai gudun kar jami’an da aka zagaye gidan dasu su zargi wani abu tunda su ba nasu bane su duka yasa su kiran su A.G suka sanar musu. Umarnin ɗakkosu duka suka basu, dan a ganinsu ma kawo hajiya maman zaisa Halilu ya faɗi gaskiya ko bayaso ai……
______________________
Tunda ta kammala shiryawa dan harda yin sabon wanka taketa faman leƙen falon. Ji take kamar ta kora Abdull a gidan amma babu dama. Sarai master na sane da ita amma ya basar abinsas cigaba da hirarsu shi da Abdull. Dan abincin ma basu cisa ba sai gab da la’asar. Zuwa sannan Hibbah ta cika da takaici harta koma ɗaki ta kwanta harda su kuka. Kiran sallar la’asar ne ya sata miƙewa ta ɗauro alwala. Koda master ya shigo yin alwalar shima batako kulasa ba. Shima baice mata komai ba ya shige toilet yayi abarsa yazo ya fita.
Bayan sun dawo salla Abdull baima shigo ba shi kaɗai ya dawo ciki. Yanzun ma Hibbah na kwance a inda tai salla tana jinsa tai likimo. Komai baice mata ba ya nufi toilet bayan ya rage kayan jikinsa. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya fito yana raɓar ruwa da alama wanka yayo.
Fitowar tasa tayi dai-dai da miƙewar Hibbah dake faman kumbura baki na haushi. Da sauri ta juya baya saboda kallon datai masa. Shiko ko’a jikinsa ya nufi gaban mirror. Shiryawa ya farayi a nutse yana kallon duk motsinta ta cikin mirror ɗin. Harya kammala baya tunanin tako kalli sashen da yake. Sai da yazo gabanta yana baza ƙamshi cikin ɗanyar shadda getzner dake ta maiƙo da ɗaukar ido ɗinkin haf jamfa na zamani. Duk da ba wannan bane karon farko da Hibbah ta fara ganinsa cikin manyan kaya a fuskar Isma’il, sai ta samu kanta da saki baki tana kallonsa batare dama ta sani ba, dan gani take tamkar bashi baneba wanine daban.
Ɗan duƙowa yay ya hure mata idanu. Ta shiga ƙyaƙyƙyaftasu da saurin kauda kanta zata juya masa baya. Ƙugunta ya riƙo da kamo hanunta na dama ya zuba mata link ɗin da zaisa a hannu. “Miye na juyawar bayan lada kike samu idan kina kallona madam”.
Sake ƙasa Hibbah tai da kanta duk da yana maganar ne da ƙoƙarin ɗago fuskarta dan son su haɗa idanu amma taƙi yarda.
“Fushi kikeyi ne?”.
Ya sake faɗa yana ɗago haɓar tata sosai duk da taƙi kallonsa. Kanta ta girgiza masa da zare hanunta daya zuba mata link ɗin a ciki. Shima komai bai sake cewa ba ya miƙa mata hannun nasa. Cikin son ɓoye kukan dake son taso mata ta ce, “To ka sakeni sai na saka maka”.
Babu musu ya saketa, ta sauke ƴar ajiyar zuciya da fara saka masa link ɗin. “Nagode”.
Ya faɗa a hankali yana binta da kallo. Batace komai ba ita dai. Sai da ya ɗakko ledar da taga ya ajiye a gefen gadon ya saka cikin hannunta ne ya sata ɗagowa ta dubesa. Ido suka haɗa, dan haka ta kauda nata. “Na miye?”.
“Ki saka su ina jiranki a falo”.
Daga haka ya nufi hanyar fita ya barta da binsa da kallo. Iska ta ɗan shaƙa ta furzar tana buɗe ledar ganin ya fita. Sai kuma ta fiddo kayan cikin ledan. Lass ne mai ƙyau kusan kalar kayan jikinsa, sai mayafi babba da takalma da bag masu ƙyau suma. Mamaki ya kamata da tunanin inda ya samosu yaushe kuma ya kawosu ɗakin? Rashin amsa ga kowa yasata fara cire na jikinta ta canja. Sai ga kaya ɗas a jikinta tamkar an gwada. Ita kanta tasan tayi ƙyau koda ba’a faɗa ba, saita samu kanta da sakin murmushi. Tsaf ta shirya ta sake gyara fuskarta, ɗan kunne da sarƙan ta ɗauka a hannu bayan ta saka takalmin ta cire tarkacen takardun cikin bag ɗin ta ɗan jefa turare da ƙananun abubuwa irinsu handkerchief da ɗan Norse mask saboda tsaro.
Master dake zaune a falon yana waya a nutse takun takalmanta yasa shi ɗago idanu ya zubama ƙofar. Ya ɗan fusgo numfashinsa da ke neman harɗewa. Duk da ba tun yau yasan kwalliya na ɗaukar jikin Hibbah ba idan tayi, sai yaga yauɗin ta zamar masa ta musamman. Dan ta fito a amryarta ne ƴar gaske abin sha’awa. Ga ƙuruciyarta ta bayyana kanta tamkar amaryar ƴan shila????.
Harta ƙaraso garesa baima sani ba. Daga can sai faman hello-hello wanda suke wayar ke faɗa amma bama yajinsa…
“Yaya dan ALLAH ka samin”.
Maganarta ta katse masa tunani har yaji hello ɗin wanda suke wayar. Yanke kiran yayi yana jan ɓoyayyar ajiyar zuciya tare da miƙa mata hannunsa ta ɗora masa sarƙa da ɗan kunnen. Hannun nata ya kamo ya zaunar da ita akan cinyarsa. Hibbah ji take kamar ta nutse dan kunya. Amma dai ta daure ta dake zuciyarta. Ɗan kunnayen ya fara saka mata. Kafin sarƙar. Yanda numfashinsa keta sauka mata a jiki sai faman matse jiki take. Shi kansa kasancewar tasu a haka ba ƙaramin canja masa salon gudin jini yake ba, ya dai daure ya gyara mata sarƙan bayan ya saka da gashinta daya fito ta ƙasan ɗan kwalin kasancewar irin ɗaurin nan tayi da ake yayi.
“Nagode”.
Ta faɗa a hankali tana miƙewa daga jikinsa. Idanunsa kawai yaɗan lumshe da jinjina mata kai shima ya miƙe. Gaba yay ta bisa a baya, su dukansu sunajin wani shauƙi a ƙasan zukatansu wanda basusan kona minene ba. Tunda suka fito compound ɗin Abdull keta ƙyalla musu hotuna dan yanda suke tafiya a jere gwanin birgewa. Daka gansu kaga ango da amarya da ke ji da tashen more lokacinsu. Master da ya harari Abdull da yaƙi daina hotunan ya buɗe ma Hibbah baya da mata nuni da ta shiga. Shigar tayi, sai da ta zauna ya ɗan ranƙwafo ya gyara mata mayafinta daya sakko sannan ya rufe. Shima shi da Abdull suka shiga.
Su Habib dake laɓe suma sunata musu hotuna harda masu video suka shiga tafawa da juna suna dariya ganin motar ta fice. “Wayyo soyayya ruwan zuma”. Cewar Khalid yana dariya.
Salis yace, “Bari kawai master zai ƙonemu a gidan nan. Babban yaya ashe ya iya soyayya haka kallon tara saura kwata yake mana”.
Dariya suka sanya su duka kowa na faɗin albarkacin bakinsa cike da shaƙiyancin su. Sai dai zukatansu fal suke da tarin farin ciki dan burinsu dama suga master ɗinsu a cikin nishaɗi da farin cikin rayuwa tamkar yanda suma yake burin ganinsu akoda yaushe………
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*