Uncategorized

TAKUN SAKA 47

*_Typing????_*

_______________________

*_MATAYEN ƘWARAI KUNA INA NE?._*

_Maza ku garzayo da gudunku ga ƴar zuru mamar zee-zee mai kayan mata na maida tsohuwa yarinya????????._

*Kayan matan ƴar zuru zasu maidaki shalele ƴar gaban goshin maigida koda kina da kishiya ƴar birnin shehu????????????*.

_Kayan ƴar zuru nada matuƙar sirrika da inganci irin wanda sai an gwada akansan na ƙwarai. Idan da ƙyautar gida akemiki a master room kikai amfani da kayan ƴar zuru Nigeria za’a baki harda jirigin sama na yawata ƙasashen duniya????????????_.

*MUNADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA*????????

Kaza akwai 10k

15k

5k

Tsimi 5k 10k

Matsi 5k

Gumba uku 2k 

Zumar gorun tula syrup3k

Garuka 3k

Cicccibi 5k

Zakara 20k

Zabo20k

Humra 

Turaren tsugunni 

Butar tsarki

Maganin infection

Tsimin tabaje 

Turaren al,ajab 

*Muna maraba da maisayen ɗaya ko sari, kayanmu garantee ne in har basuyimaba zan maidama kudinka*.

 

_Address maberar jariri bayan FGC sokoto_ 

08068526455

*Zaku iya saving number ta domin ganin hajata*

Zaku iya samun mu amanhajar

Facebook

Istagram

Yar_zuru_mamar_zeezee- kyn_mata.

Sai kunzo????????????????????????????????.

_____________________

*_Chapter Forty Seven_*

……….Su Hibbah na baje a falo suna kwasar hira ita da su Zahidah dake ta mata sheri itama cikine da ita, dan ta matsa musu tunda ta ƙyalla ido taga cikunna a jikinsu. Shinefa suma suka tasata gaba da nasu tsokanar Ammar na tayasu da dariya wai wayaga auta da ɗa. Tun tana kai ƙararsa wajen su Yaya Umar harta koma jifansa da throw pillows tana kukan taɓara.

         Hatta Ummi kasa daurewa tai saida tai dariya dan taɓarar autar tata sai ita. Kiran da yaya Abubakar yayma Ummi ne ya sanar mata bazai kwana a gida ba ya sakasu barin Hibbah ɗin suka koma hirar rashin dawowar Master shima. Suna cikin zancen kuma sai ga ɗan halak ɗin ya kira Ummi shima ya sanar mata Hibbah zata kwana anan shi wani uziri ya riƙesu tare da yaya Abubakar. Addu’a tai musu na fatan alkairi baki ɗaya.

      Yana katse kiran kuma ya kira Ammar yace ya haɗasa da Hibbah. Amma ya jata gefe dan yasan halin kayarsa. Da ƙyar Ammar ya danne dariyarsa ya kama hannun Hibbah suka nufi bedroom ɗin Ummi.

      Zatai magana ya manna mata wayar a kunnenta ya fice. Hibbah dake hararar Ammar dake mata gwalo zai fice tace, “Mai kan gwanda kawai”.

         “Nine mai kan gwandan?”.

Sassanyar muryarsa ta daki dodon kunnenta a bazata. Dan tama manta waya Ammar ya saka mata a kunne. Idanu taɗan waro tamkar tana gabansa. “ALLAH shine shaida ni dai bada kai nake ba da yaya Ammar nake”.

        Master dake goge jikinsa dake raɓar ruwan wanka da ga can yay murmushi yana ɗan lumshe ido. “Ki shirya ganinan zuwa zan ɗaukeki”.

       Kamar tana gabansa ta marairaice fuska. “Dan ALLAH ka barni na kawana wajen Ummi”.

      “Idan na barki ni kuma na kwana da wa?”.

     Ƙasa-ƙasa batare da tunanin zaiji ba ta ce, “To da dawa kake kwana?”.

“Okay hakama zakice, to nama fasa barin ki shirya kawai”.

      “Dan ALLAH kayi haƙuri bazan sake ba”.

      Yanda tai maganar da alamar kuka ya sashi danne dariyarsa da ƙyar. “Idan na barki duk bashin da kikaci zaki biyasa in kin dawo”.

      Da yake so take a barta babu tunanin komai tace ta amince. 

    Murmushi ya sakeyi yana ƙoƙarin shiryawa. “Okay tunda hakane sai ki fara da sumba ɗaya ƙwaƙwara yanzun nan kona taho”.

      “Ni dai a’a dan ALLAH”.

“Oh to ki shirya ganinan zuw…..”

       Kafinma ya rufe baki ta mannama wayar kiss da yazo masa cikin kunne a bazata. Sai kuma ta yanke wayar ƙitt. Duk yanda yaso dannewa ya gagara sai da yay dariya yana girgiza kansa da ajiye wayar ya cigaba da shirinsa.

         Gudu-gudu yay shiri ya fito dan su Habib na jiransa a falo. Barka da fitowa suka shiga yimasa har yakai zaune. Lap-top ɗin dake ajiye saman centre table ajiye ya ɗauka yana gyara zamansa ƙafa ɗaya kan ɗaya. Cikin maida hankalinsa ga abinda yake a ciki ya fara magana batare daya kallesu ba. “Salis, Khalid, Habib. Kune zaku shiga cikin gidan. Khalid kaine zaka fara bubbuɗe ko ina ta yanda idan ya farka zaiyi tunanin kuskure akai wajen buɗesa. Sannan Salis ka tabbatar ka ajiye dukkan abinda zai iya gani da zai taimaka masa neman su A.G a farko kafin kowa, ko cikin yaransa. Da zarar kun kammala duk wannan Khalid sai kai masa allurar da Abdull ya baka. Kasancewar tanada ƙarfi zai saurin farkawa ya kuma dawo hayyacinsa da wuri. Habib zai amfani da wannan damar ta komawa da ga can ta bayan Windown ɗakin da yake ciki kayi wayar ƙarya akan abinda zaka shirya kansa a halin yanzu. Daga nan sai ku koma tacan sama bayan ƙarfen nan ku ɓuya har sai ya fito a gidan sannan ku kirani”.

      Cikin girmamawa suka amsa masa. da hannu yay musu nunin suje, tare da cilla musu key ɗin mota. Salis ya cafe.

    Sai da suka fice ya ɗago ya duba Adam tare da miƙa masa key ɗin Napep. “Kaje ka jira a bakin layin, da zaran sun kira ya fito ka ɗaukesa zuwa duk inda ya sanar maka zaine. daga nan na sani”.

       “Okay Master”.

Adam ya faɗa shima cike da girmamawa.

     Bayan fitarsa shima yaɗan cigaba da aiki, bayan wasu mintuna ya dubi Musbahu da Idris da Zaidu. “Nasan da ya samu damar fitowa babu wanda zai nema a halin yanzu sai yaransa biyu daya yarda dasu fiye da kowa bayan ni. Dage, da Katafila, Musbahu, Zaidu baku da matsala da hakan, dan kun iya komai nasu, ga wayoyinsu nan sai ku ɗauka, zaku haɗa hannu da Adam wajen kaisa inda su A.G suke”.

       Suma cikin girmamawa suka amsa masa tare da ɗaukar keys ɗin mashin guda biyu da wayoyin suka bar wajen domin zuwa suyi nasu shirin. Ya dubi Idris daya rage, “Kai kuma zamu kasance tare da kai anan domin bibiyarsu da ga nan har zuwa lokacin dazan fita”.

      Kansa ya jinjina masa shima, tare da neman waje ya zauna. Waya Master ya ɗauka, yay kiran yaya Abubakar da ya kammala haɗa jami’an da zasuyi aikin tare a can, bayan sunyi magana akan duk yanda tsarin zai kasance ya ajiye wayar da maida hankalinsa ga Idris.

_______________

        Tafiyar kusan mintuna talatin da wani abu ya kai su Habib inda suka nufa, gida ne madai-daici dake cikin sabuwar anguwa, duk da akwai duhun dare haka suka ajiye motar acan baya da gidan sosai suka ƙarasa da ƙafa. Kamar yanda Master ya tsara musu suyi basu ƙetare magana ko guda ba duk sukayin. Bayan Khalid ya kammala nasa aikin na bubbuɗe ko ina ya shiga ɗakin ƙarshe daya buɗe. Ƙugu ya riƙe yana maibin ɗakin da kallo hannunsa ɗaya rufe da hanci, lafiyayyen ɗaki ne madai-daici mai ɗauke da toilet a ciki, sai gado ƙarami na ƙarfe irin na ƴan makaranta da kwanon cin abinci da kofi. Daka gani dai ɗakin baida maraba dana ƴan prison. Cikin nutsuwa ya tsaida idanunsa akan mutumin dake kwance bisa gadon fuskarsa buzu-buzu da gashi har kansa kai kace mahaukacine. Yayi datti matuƙa, na jiki dana sutura, ga wani wari dake fitowa daga jikinsa mai ban tashin hankali. Sai dai babu alamar yunwa tattare da shi ko kaɗan. Khalid ya ɗanja numfashi da ɗage kafaɗa yana zaro syringe dake ɗauke da ruwan allura a aljihunsa. Matsawa yay jikin gadon yayma mutumin, yana zarewa bai tsaya wasa ba yay wuff ya fito da ga ɗakin yanama Habib ƙaramin fito alamar ya kammala nasa aikin.

      Rufe bakin Khalid keda wuya mutumin ya farka, zumbur yay ƙoƙarin miƙewa, sai dai azabar data ziyarci jikinsa na harbin dake a hannunsa da ƙafa wanda Master yazo yay masa shi a daren shekaran jiya tamkar yanda akai masa ya sashi sakin ƴar ƙaramar ƙara. Sai da ya ɗan ja numfashi sannan ya ƙarasa miƙewa da ƙyar yana cizar lip ɗinsa na ƙasa. Ɗakin yabi da kallo cikin ƙunar rai da zuciya, tsahon shekaru biyu kenan yake a ciki batare da yasan wanda ya kawosa ba. Tun yana gwada ƙoƙarin fita harma ya haƙura yasama sarautar UBANGIJI ido. Ana bashi abinci wadatacce ana kuma kula da lafiyarsa. Amma akan bugar da shi da maganin barci a wasu lokutan ta hanyar abincin da ake bashi. Kamar shekaranjiya, sai da aka buhar dashi sannan aka harbar masa ƙafarsa da hannu. Gigitar shigar bullets da azaba ya sashi farkawa, sai dai baiga wanda ya harbesan ba dan harya fice a ɗakin, sai bayan kusan awa guda ya jigata matuƙa sannan yaronsa daya yarda da shi fiye da kowa ya shigo, cikin wata sabuwar azabar ya cire masa bullets ɗin yana zuba masa maganganun da har yanzu daya farka bazasu bar gigitashi ba. 

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button