TAKUN SAKA 47

Jin kamar ana magana ta bayan window ne ya sakashi nutsuwa yana saurare. Tabbas komai ya shiga kunnensa, tamkar yanda Master yay fata kuma yayi yunƙurin ganin ya gwada miƙewa ya gudu. Cikin azabar zogi da ƙafarsa ke masa da raɗaɗi ya miƙe da ƙyar, dan bayan cire bullets ɗin ko paracetamol Master bai bashiba dan rage zafin ciwon. Gwada buɗe ƙofar yayi, sai ko gata ta buɗe. Jikinsa har rawa yake wajen turo illahirin jikinsa waje sosai dan gani yake mafarki yake tamkar yanda ya saba. Sai dai ganin ya fito falon sosai ya sashi saki wata dariyar ƙunar rai da zuciya. Tare da jerama kansa kirari irin na gawurtattun arnan saman dutsin nan. Cikin tafiyar dake nuna ƙashin kafafunsa sunyi sanyi saboda zaman waje ɗaya ya nufi hanyar fita ƙofar falon, dan ya haƙƙaƙe a ransa yau zai bar gidan nan koma ta halin yaya ne. Duk inda auta (Master yake cema auta) yake sai ya halaka rayuwarsa kafin kowa.
Ba kai tsaye suka buɗe masa ƙofar falon ba dan karya zargi komai, sai da ya ɗan sha wahala kafin ta buɗe duk tunaninsa ƙwazonsa ne. Daga falon ma zuwa tsakar gidan da ƙyar ya iya isowa ƙofar waje, sai dai itafa a rufe take dan haka yay tunanin haura katanga. Kasancewar dukanin hanyar da zata bashi sauƙi na barin cikin gidan sun bar masa ya samu damar haura katangar tunda dama horarrene ba saboba. Dukan abinda ke faruwa su Habib na kallonsa harya fito cikin layin, ya jima a kwance bayan dirowarsa daga katangar kafin ya ƙara tashi ya fara tafiya cikin haɗa hanya, cikin sauri Habib ya dannama master waya ya sanar masa.
Sosai Master yay mamakin yanda aikin ya tafi a sauƙaƙe, yanke kiran yay ya maida ga Adam. Adam dake daga farkon layi a napep yana gani ya ɗaga cikin sauri.
“Maza ka tada napep ɗinka ka taresa gashi nan zai fito”.
“Okay master ”. Adam ya faɗa yana ƙoƙarin sakama napep ɗin key. Cikin azama yabi umarnin Master. Cikin ɗan shawagi tamkar ya ajiye mutum ya shigo farkon layin, yay reverse kamar zai juya ya fita cikin sa’a ya haske mutumin. Ƙasa yay da fitilar sai kuma ya sake haskashi. Tabbatar da shi ɗinne ya sakashi burga napep ɗin zuwa gabanshi, Cikin hanzari ya fito yana ambaton “Subahanallahi mai gida kana lafiya kuwa?”.
Hannu kawai mutumin ke iya jinjina masa, cikin matuƙar wahala ya fara magana. “Ka fitar dani a layin nan yanzu-yanzu, ko nawane zan baka saurayi”.
“Babu damuwa baba, kaga taho muje, ko’ina kakeso zan kaika, ina fatan dai lafiya”.
Bai iya bama Adam amsa ba harya taimaka masa ya shiga napep ɗin, sai da Adam ya tada napep ɗin suka bar layin ya dubesa daga kwancen da yake a baya. “Yaro ko zaka aramin wayarka?”.
“Babu damuwa baba gata”.
Kamar yanda Master yay hasashe number *Katafila* kuwa ya fara lodawa a wayar ta Adam ɗin, da farko bata shiga ba kamar yanda suka tsara, sai a na biyu. Koda ta shigan kuma su Zaidu basu ɗaga ba harta yanke. Sai da ya sake kira cikin tashin hankali dan sune kaɗai damarsa a yanzun. Tana gab da tsinkewa Zaidu ya amsa.
Cikin muryar gawutattun marasa ji irinsu Katafila Zaidu ya fara magana. “Kai waye da duhun daren nan hakane?”.
Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar mutumin, sanin halin katafilansa baya son jira ya fara magana da sauri-sauri. “Master ne Katafila na!”.
“What!!?. Kai ALLAH ganganne wannan, gagarar da mukai mukune ta sakaku fara canja layi na yi mana shigo-shigo da oga. To ku sani bazaku taɓa sani kojin komai ba dan oga ya muku zarrah”.
A karon farko master ya kece da wata shegiyar mahaukaciyar dariya da har ta bama Adam tsoro da mamaki. Duk da a yanda yake haka ya fara jerama Katafila kirarin da shi kaɗaine ke masa shi duk duniya. Cikin nuna alamar mamaki da ga can Zaidu yace, “Kai oga!!”
“Tabbas nine Katafila. Ka fadamin kuna ina dan ma kuɓuta daga hannunsu, maza faɗamin”.
“A’a oga, kai dai faɗamin inda zamu sameka gani nan ni da Dage a ɓoye muke muma saboda farautarmu da ake dare da rana tun bayan ɓacewarka”.
Wani sanyi ne ya ratsashi na daɗi, ya mikama Adam wayar akan yayma su Katafila ɗin kwatancen inda zasu haɗu. Babu musu Adam ya amsa ya kwatanta musu yanda Master ya tsara musu dama tun farko.
Turyan-tiryan Adam ya isa har inda su Zaidu suke, waɗanda gaba ɗaya sun canja kamanni daka gansu kaga ƴan sara suka zam. Sai wani rangaji suke da magana uwa ta bugaggu. Cikin wata irin zabura master ya miƙe zaune saboda jin muryar su Dage, suma ihu suka buga da faɗawa cikin napep ɗin suka cikuykuyesa a dole su murnar ganinsa sukeyi. Adam ya danne dariyarsa da ƙyar yana toshe hanci, dan tunda ya ɗakko master wani shegen wari ke bugar hancinsa. Su kansu su Zaidu da ƙyar suka iya daurewa warin nan. Harda hawayen drama kuwa sukayi su a dole ogansu ya dawo.
Adam dake nuna kamar a tsorace yake dasu, cikin marairaicewa yake tambayarsu ina zai kaisu?. Musbahu (Katafila) ya duba Adam ɗin sheƙeƙe ya ɗauke kansa yana maidawa kan master. “Oga ko’ina a hargitse take a yanzu haka. Dan wani na amfani da sunanka yana ɓarna ta maƙudan kuɗaɗe, inaga yanzu babu inda ya dace mu kaika sai wajensu A.G, sune kawai zasu baka mafaka har komai ya lafa”.
kai kawai master ya jinjina musu, dan har yanzu ya lura basu fahimci akwai harbi a jikinsa ba. “Ni yanzu banda lambar kowa, tayaya kenan zamu sami wani a cikinsu?”.
Zaidu (Dage) ya zaro ruɓaɓɓar wayarsa, “Ai oga kwantar da hankalinka, inada ita a zane kan kwakuletata bara a danna mas kira”. Batare da ya jira cewar master ɗin ba ya dannama A.G kira. Ba’a ɗaga ba sai da tana gab da tsinkewa. A.G dake a tsakkiyar su Alhajin Mande ana sabon meeting yay musu alamar suyi shiru yana kaiwa kunne.
Daga nan Zaidu yace, “Hallo yallaɓai Dage ne na master mai jurar wahalar duniya!”.
“What!?”.
A.G ya faɗa yana miƙewa a zabure. Zaidu dake saurarensa yace, “Yes yallaɓai. Yanzu haka muna tare da oga mun tsintosa acan bayan gari, ya kuma tabbatar mana kai kawai yake son fara gani dan bakinsa da goro…”
“Kai dalla saurara bana son yaudara. Ni shegen yaron nan zaice yana son gani bayan ya halaka rayuwata, kama tabbatar masa inhar ya bari idona yaga nasa to ko kashinsa wani bazai gane ba ok;. Yana gama faɗa ya yanke kiran.
Duk da Zaidu yaji mi A.G ɗin ya faɗa sai cewa yay ai yace su ƙarasa yana gidan hutun Alhajin Mande. master dai bajin A.G yay ba, dan haka ya aminta kawai dan yasan su Dage bazasuci amanarsa ba. Zaidu ne ya dinga nunama Adam hanya duk da kuwa shima ya sani sarai.
____________________________
Dukkan abinda ke faruwa Master yana saurarensu ne tiryan-tiryan da ga gida, dan haka yanajin sun ɗauka master ya miƙe ya hau shiri a gaggauce. Yanayi yana waya dasu Yaya Abubakar da suma ke shiri daga can station. Yayinda su I.G suma ke daga can suna jiran tsammani dan Master ya kirasu akan samun inda ainahin master ɗan ta’adda yake a daren nan. Cikin kanƙanin lokaci Master ya fito cikin shiri yana soke bindigu biyu cikin jikinsa.
“Idris ka kula da komai yanda ya kamata. Ko yaya ka fahimci matsala da ga su Adam kai saurin sanarmin dan su A.G sun wuce dukan tunanin mai tunani.”