TAKUN SAKA 47

“Okay Master ALLAH ya bada nasara”.
Kai kawai Master ya jinjina masa. sai da ya je ƙofa ya tsaya yay addu’a kafin ya fice cikin zafin naman da ALLAH ya azurtashi da shi. Mashin ɗin dake can gefe a fake ya nufa, sai da yay addu’a nanma ya haye samansa yay masa key. Da sauri maigadi dayaji motsinsa ya fito ya buɗe masa gate ɗin.
Akan hanya Master dasu Yaya Abubakar suka haɗu, su kusan ashirin duk cikin shirin kota kwana. Tun a farkon shiga anguwar datai tsitt alamar mutane sunyi barci suka faka motocin da suke ciki. Duk fitowa sukai, hakama Master ya sauka a mashin ɗin nasa yana sauraren abinda ke faruwa daga can ta ɓangaren su Zaidu ta abin da ke a kunnensa. Cikin tawagar yaya Abubakar ɗaya ya karaso gaban Master ɗin da bullet proof jacket ya saka masa. Yana gyara masa ita suna magana da yaya Abubakar akan yanda zasu zagaye gidan hutun na Alhajin Mande da su A.G ke a ciki suna sabon meeting…….
Acan ɓangaren su A.G kuwa a kiɗime yakema su Dr Sufi bayanin wai yaron master ne ya kirashi akan ga master ɗin nan yana son zuwa inda suke. A zabure suma suka miƙe har suna haɗa baki wajen ambaton sunan master ɗin.
Engineer yace, “Anya kuwa ba wata gadar zare yake neman ƙulla mana ba?”.
“Komaima zai iya dan yaron nan shaiɗanine. Amma karku manta a yanzu muna a gaɓar neman mafitane akan iyalanmu da dukiyoyinmu. Ina ganin kodai yarasa yanda zaiyi ya gudu ko makamancin haka shiyyasa ya dawo garemu”.
“Tabbas maganarka na’akan hanya R.D, inaga mu bashi damar zuwan amma mu taresa cikin ɓadda kama muma”.
Duk sun gamsu da zancen Alhaji Sallau, dan haka a take A.G ya danna kiran no ɗin da su Zaidu suka kirasa. Bugu biyu kuwa suka ɗaga sai dai basuyi maganaba. Dr Sufi daya amshe wayar a gadarance yace, “Yazo muna jiransa”.
Batare daya jira cewar su Musbahu ba ya yanke wayar. Murmushi sukayi suna kallon juna batare da master ya lura ba dan kwance yake har yanzu jikinsa babu ƙarfi. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso dan dama dai suna gab. Maigadi da dama yasan da zuwan nasu sunayin horn ya leƙo cikin kare fuska da suka haske masa. “Wane mara mutuncine haka wai?”.
Dira Musbahu da Zaidu sukayi sunama maigadi kurari, ƴar hararar su yay sannan ya fara maƙyarƙyata irin dai ya tsoratan nan. Zaidu ya kai masa halbi yana zagi da faɗin, “Mara mutunci kaine zaka goya oga har cikin gidan nan kuwa. Maza zoka duƙa ya hau bayanka. Bin umarninsu yayi, cikin rawar jiki yazo ya tsugunna, Adam ya taimakawa master ya hau bayan maigadi. Suna ganin ya shiga cikin gidan suka koma napep Adam yaja suka kauce dan Master daga can yana sanar musu suyi maza subar wajen suna gab da gidan.
Su A.G na ɓaɓɓoye maigadi ya shigo goye da master yana nishi da ƙyar, zubesa yay ƙasa kusa dasu Abba da zuwa yanzu da ƙyar suke numfashi dan azabar wahala. A.G ne ya fara fitowa da sauri a inda ya ɓuya riƙe da bindiga. Maigadi ya ɗaga hannu sama yana makyarkyata daja baya. “Oga ka rufan asiri ka sauke wannan abar, baƙone gashinan, ya kuma tabbatarmin kunsan da zuwansa”.
A.G dake tsaye kan master da bindiga yayma maigadi nuni daya fita. Da gudu kuwa ya fice har yanacin tuntuɓe. Bai tsaya a gate ɗin ba yay waje bisa umarnin Master shima.
A.G dake bin master da kallon mamaki cikin daka tsawa yace, “Munafuki da wannan salon kazo kuma? To ai ka makaro dan zuwa yanzu mu babu abinda zakai ka layance mana”.
Da mamaki master ke duban A.G ɗin. “A.G kardai kace baka ganeni ba. master ɗinku ne fa, kodan ka ganni da wannan gashin buzu-buzu, ku bani abun aski na saukesa nasan zakufi fahimta ta”.
Harbin ƙafarsa A.G yayi a fusace. master ya saki wahalalliyar ƙara. A dai-dai nan suma su R.D dake laɓe suka fito kowanne hannu da makami. Zasu fara lugudarsa ya zabura gefe cikin magiya da roƙon su saurareshi. Dan sai yanzune ya tuna cewar su Dage sun sanar masa akwai wani Master dake basaja da shi yana aiki. Ya buɗe baki zai fara musu bayani kawai sukaji an banko ƙofar falon da masifar ƙarfi har sai da suka zabura. Su Master ne da suka shigo cikin gidan da sanɗa. Tamkar ƙyaftawar ido sukaima su A.G zobe a cikin falon.
Yaya Abubakar ya daka musu tsawa akan su ajiye makaman hannunsu koya fasa kan mutum. Cikin rawar jiki dabin ƴan sandan da kallon mamaki su A.G auka shiga ajiye abubuwan hannunsu suna ɗaga hannaye sama na alamar surrender.
Master daya kasance shi kaɗai a waje ya shigo falon cikin takun izzarsa da ƙasaita yana tafa hannaye. Gaba ɗayansu suka maida hankalinsu ga ƙofar dan son ganin wanene zai shigo. A wani irin zabure duk sukai baya, domin ganin wani Master ɗin kuma. Suka duba yaya Isma’ill suka duba master na ainahi dake zaune shima yana dubansa. Kafin wani a cikinsu ya sami damar cewa wani abu Master yakai hannu bisa face ɗinsa ya zare mask ɗin dakesa su kallesa a master ɗan ta’adda. Sai ga fuskarsa ta ainahin Muhammad Shuraim da jami’an tsaro suka sani ta bayyana.
Master yakai zaune yana wata shaƙiyyar dariya da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya kaɗa musu yatsun hannunsa uku. “Hy! Guys”. Yay magana da muryar master ɗan ta’adda. Cikin sake rikicewa suka dubesa, suka dubi master dake zaune fuska buzu-buzu da gashi. A zafafe master ɗan ta’adda ya nuna Master yana girgiza musu kai, “karku yarda da wannan matsiyacin yaron, bakowa bane face yarona, shine ya ari dukkanin salona yazo muku a suffata bayan ya ɗaukeni ya ɓoy…….”
“Relax! Relax oga. Miye na zazzari bayan nima da kaina zan iya faɗa”. Isma’il (Master) yay maganar cikin tsantsar rainin wayo da kai hannu saman face nashi ya shafa a hankali.
“What!!!?”.
A.G ya faɗa cikin rawar jiki har yana neman faɗuwa. Hakama su Alhajin Mande wani irin aradu ne ya saukar musu bisa kawuna cikin ƙanƙanin lokaci, Abba dake kwance duk yanaji da ganin komai ya saki wani marayan kuka ianunsa akan yaya Abubakar sa Master.
Master dake dubansu yana murmushi ya tsaida idonsa akan A.G. “Haba ɗan sanda ya da firgita haka?! A tunaninka kaine kawai ka iya mufunci da salon makirci nacin amanar ƙasa? No, no my dear akwai ƴan iska a saman iyawarka masu tasowa irina!!!!”.
Master yakai ƙarshen maganar a matuƙar hargitse yana doka hanun kujera da ƙarfi tamkar face nashi zatai aman wuta. Basu kawai ba, hatta su yaya Abubakar kallon razana suke masa. Dan gaba ɗaya ya juye musu tamkar bahagon zaki, Abba da gaba ɗaya suffar Master ta dawo masa irin ranar daya illata Junaid ya fara rawar jiki da faɗin, “Wlhy shine, shine wlhy A.G. shine ya illatamin yarona!”.
Ina babuma wanda yasan yanayi duk da kunnuwansu na saurarensa. Yaya Abubakar ya fahimci idan Master yay fushi babu sauƙi, dan koyaya kuke da shi sai kaji shakkar koda kallonsa ne. Ganin Master ya ɗauka bindiga Yaya Abubakar yay saurin nufosa, sai dai kafinma ya iso harya harbata a ƙafar A.G. wata irin gigitacciyar ƙara A.G ya saki da kaiwa ƙasa durƙushe.
Cikin gargaɗi da waro manyan idanunsa masu tamkar zaki ya ke nuna A.G da ɗan yatsa. “Wannan harbi ne na razana matata da ka dingayi!!”.
Wani irin kuka A.G keyi na azaba, zufa ta gama wanke jikinsa sharkaf kamar wanda yay wanka. Yaya Abubakar dake ɗan bubbuga kafaɗar Master ɗin alamar lallashi yace, “Please Cool down Shuraim”.