TAKUN SAKA 47

Komawa Master yay ya lafe jikin kujerar yana saki tagwayen ajiyar zuciya a jajjere. Ji yake kamar ya harbesu baki ɗaya tun anan ya huta kawai. Dubansa yakai ga ɗaya a cikin yaransu na ƴan sanda. “A ciremin gashin fuskar wannan”.
Cikin saurin ɗan sandan yace, “Okay sir”. Yana nufar master da zuciya ta kumesa, ji yake kamar ya miƙe ya damƙi Isma’il (Master) yay gunduwa-gunduwa dashi. Dan babu abinda ke masa kaikawo a rai sai irin ɗunbin ƙaunar daya nuna masa a baya da yarda ta haƙiƙa, ashe shi ɗin jami’in tsaro ne dama. Cike da mugunta ɗan sanda ɗaya ya kama hannayensa ya banƙare ta baya yasa masa handcup, wani ya duƙa ta gabansa ya fara aske gashin fuskarsa dake buzu-buzu. azaba ta saka master fara ihu dan aski ne mai kama da ana tsigar gashin da hannu dan azaba.
Sauke gashin da aka gamayine tsaf ya bayyana ainahin fuskarsa. Tabbas su A.G sun sake tabbatar da wannan shine master ɗinsu, suna mamakin taya akai basirarsu ta toshe haka har suka gagara fahimtar badashi suke tare ba sai a yau da guri ya ƙure musu. Wayar Master ce ta katse musu tunani.
Yana zaune har yanzu ƙafa ɗaya kan ɗaya tamkar wani jinin sarauta. Magana yake cikin fushi da harzuƙa. “Sir a yanzu haka mun sami nasarar kamashi tare da iyayen gidansa, sai dai dalilin gaddamar da sukai mana kowannensu ya samu harbi”. Ya ɗanyi shiru alamar saurare. Sai kuma yace, “Okay sir” yana sauke wayar a kunnensa. Da idanu yayma zaratan ƴan sandan dake tare da su magana. Kamar jira suke suka shiga ɗana kunamun bindigunsu. Rikicewa su R.D sukayi dan tunaninsu kashesu Master ɗin yace ayi. Kafin suyi yunƙurin tashi ƴan sandan nan sunbi ƙafafunsu da harbi tako ina. Cikin ƙanƙanin lokaci falon ya rikice da ihu, Hajiya mama dake a sume ta kawo numfashi, dan duk abinda ake ita bama ta sani ba. Yaya Abubakar kuwa sarai ya ganta ita da Abba ya nuna baima san da zamansu a wajen ba dan Master ya bashi dukan bayanan Abba ya gani.
Cikin abinda bai wuce mintuna goma ba sai gasu kwance wanwar a ƙasa suna ihu da kururuwar azabar harbin da suka sha, a dai-dai nan ƴan sandan da I.G ya sake turowa suka iso gidan tare da tawagar wasu ƴan jarida duk da kuwa asubahi ma tayi…………✍
*_MATAYEN ƘWARAI KUNA INA NE?._*
_Maza ku garzayo da gudunku ga ƴar zuru mamar zee-zee mai kayan mata na maida tsohuwa yarinya????????._
*Kayan matan ƴar zuru zasu maidaki shalele ƴar gaban goshin maigida koda kina da kishiya ƴar birnin shehu????????????*.
_Kayan ƴar zuru nada matuƙar sirrika da inganci irin wanda sai an gwada akansan na ƙwarai. Idan da ƙyautar gida akemiki a master room kikai amfani da kayan ƴar zuru Nigeria za’a baki harda jirigin sama na yawata ƙasashen duniya????????????_.
*MUNADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA*????????
Kaza akwai 10k
15k
5k
Tsimi 5k 10k
Matsi 5k
Gumba uku 2k
Zumar gorun tula syrup3k
Garuka 3k
Cicccibi 5k
Zakara 20k
Zabo20k
Humra
Turaren tsugunni
Butar tsarki
Maganin infection
Tsimin tabaje
Turaren al,ajab
*Muna maraba da maisayen ɗaya ko sari, kayanmu garantee ne in har basuyimaba zan maidama kudinka*.
_Address maberar jariri bayan FGC sokoto_
08068526455
*Zaku iya saving number ta domin ganin hajata*
Zaku iya samun mu amanhajar
Istagram
Yar_zuru_mamar_zeezee- kyn_mata.
Sai kunzo????????????????????????????????.
[ad_2]