Uncategorized

TAKUN SAKA 48

      Dole cikin tashin hankali masu tsaronsu suka kira Master suka sanar masa halin da ake ciki. Yay ƙoƙarin nufar gidan I.G ya dakatar da shi danshi tausayi Master ke bashi matuƙa saboda sanin shima likitan yake buƙatar gani. Wasu jami’an aka tura da motar Ambulance domin kwaso waɗanda ke a halin ciwon. lafiyayyun kuma za’a kawosu station ɗin.   

_________________

         A ɓangaren su A.G ɗin suma an cire musu bullets ɗin dake a jikkunansu tun bayan isarsu station ɗin, sannan aka garƙamesu cikin cells ɗaya na musamman na masu aikata manyan laifuka. Da wannan damar sukai amfani wajen titsiye master cikin bahagon yanayi, zayyane musu komai na yanda akai Isma’il (Master) ya dunƙule rayuwarsa ya maye gurbinsa ya basu. tare da azabobi kala-kala daya dinga gana masa ta hanyoyi da dama da bazai iya tuna wasuba a tsahon shekara biyun nan ma. 

      Tabbas sun harzuƙa ƙwarai da gaske, sai dai babu damar ɗaukar mataki, yayinda mamaki, al’ajabi na hatsabibancin Master ya sake kashesu matuƙa. Sosai zukatansu ke zafi da ɗaci, musamman idan suka tuna ɓarna da tabargazar da suka dinga zubawa a gaban Master ɗin da a yanzu sunsan bakin alƙalami ya rigada ya butse. Basu da wani sauran tasiri akan kansu ma balle akan wani. Daga ƙarshe takaicinsu da haushinsu suka shiga saukewa akan Halilu daya gallabi rayuwarsu da kukan azabar da yakesha a jikinsa na dukan da suka saka akai masa da karayarsa data koma sabuwa dan shi Master bai sa an harbesa ba saboda ganin halin da yake ciki.

       Marayan kukan azabar da Halilun keyine da ihu ya saka jami’an dake zagaye da su saurin sanarma C.P da keta kai kawo. Dole yasa aka ciro Halilun daga cikinsu dan gaba ɗaya ya galabaita har numfashinsa na fusga na alamar mutuwa. Cikin hanzari C.P ya bada umarnin a miƙasa asibiti.

_____________________________

       A gaba ɗaya yinin yau ma dai su Master basu samu kansu ba har dare, dan shi zazzaɓi ma ya masa rijif koda yasha magani bai samu ya kwantan ba yanda ya kamata. Sai kusan ƙarfe ɗaya da wani abu na dare bayan sun gama meeting ya samu da ƙyar ya rarrafa gida bisa taimakon Abdull.

      Hakama Yaya Abubakar sai dare ya shiga gida, inda su Hibbah da barci ya gagari idanunsu suka zagayesa suna masa sannu dan kallo ɗaya zai baka tausayi shima tsabar zirga-zirgan da sukasha yau. A bakinsa suka sake jin abinda ya faru da Halilu a hannun su A.G harda Hajiya mama da baisan miya kaita hannun su A.G ɗin ba. Mamaki sukai suma matuƙa sai dai ko kaɗan basu wani ji tausayin Halilun ba balle Hajiya mama. Garama Ummi ta ɗan nuna tausayawarta ga Hajiya maman. Sai ko Master da takejin kamar tai tsuntsuwa taje taga halin da yake ciki dan Yaya Abubakar ya sanar musu shima bayajin daɗi.

      Hibbah dai batace komaiba, sai da tazo kwanciya kuma abun yayta damunta arai. A sace ta ɗauka wayar Ummi datai barci tai kiran layinsa. Sai dai harya tsinke ba’a ɗaga ba. Massege ta tura masa ta kashe wayar ta koma ta kwanta zuciyarta tab bege da ƙishirwar son ganin halin da yake ciki.

*_WASHE GARI_*.

            A yau ɗin ma bada daɗin rai aka tashi ba. Dan dandazon jama’ar gari bisa jagorancin matasa tun farar safiya suka zagaye station ɗin. Su kansu su Master da ƙyar suka iya samun hanyar shiga Station ɗin suka fito dasu A.G da za’a miƙa kotu bisa shawarwarin masana da dattijan ƙasa. Dan kowa ya fahimci jinkirin miƙa su kotu zai iya kawo babbar tarzoma da matasan ke son tadawa tun a jiya. 

         Tsabar yanda mutane suka fusata wasu da ƙafa suka ringabin motocin su Master ɗin da wadda aka ɗakko su A.G a ciki dake tafiya a hankali kasancewar titin ma babu sauƙi. Haka suka tafi cikin wannan gangamin jama’a har zuwa kotu. 

         Su A.G laifi garesu har a wajen manyan ƙasar ma. Dan shi kansa shugaban alƙalan alƙalai da aka gayyato domin yin shari’ar tasu sun saka Master ya taɓa guma masa uban yasa a accaunt ɗinsa tun a farko-farkon shiga jikinsu da yayi. Rashin sanin Master ne yay waɗan nan yashe-yashen kuɗaɗen har yanzu yasa su gaba ɗaya zarginsu akan master ɗan ta’adda yake. Dan haka aƙali dake cike fam da mikin tabon da aka bar masa ya shirya musu tsaf shima domin acewarsa *RAMUWAR GAYYA TAFI GAYYA ZAFI.*

     

           Duk da shari’arsu shari’a ce buɗaɗɗiya hakan bai hana a bama lauyoyinsu damar fafatawa ba da lauyoyin gwamnati. Sai dai manya-manyan hujjojin da lauyoyin gwamnati ke riƙe da su yasa suka kada nasu A.G tun ma kafin shari’ar tai nisa. Dan dole aka matsi bakunan su Alhajin Mande suka zayyane kaso mafi yawa na daga tsiyatakun da suka aikata da rigunan mutunci da wanda master ɗan ta’adda ya aikata bisa umarninsu. Koda suka kawo maganar yashe asusan mutane ba master ɗinsu bane sam alƙali baima sauraresu ba. Dan ihu da boren dake faruwa ta waje daga jama’ar gari da kuɗin da alƙali yaci na manyan mutane irinsu matar gwamna yasa shi yanke musu hukuncin zaman gidan kaso na tsahon shekaru ɗari da hamsin-hamsin. A takaice dai kowa yasan ɗaurine na rai da rai wannan kawai.

       Sosai wannan hukunci yayma kowa daɗi a cikin manyan, nan take aka cikuykuyi su A.G da aka hana sake cewa komai akayo waje da su domin miƙasu magarƙama (prison). Duk da wannan hukunci da aka yanke musu hakan bai hana jama’ar gari da sukai ready ɗin fitowar tasu ba fara jifansu da gasu har jami’an da suka fiddosu. Dansu burinsu kawai a basu su A.G su kashe kawai yafi hukuncin zaman gidan yarin a wajensu. Sosai ruwan dutsuna ke sauka a kansu har takai da ƙyar aka turasu mota. Nanma basu tsiraba dan motar mutane suka dinga jifa tako ina suna fasa glasses ɗin. Dole jami’an tsaro suka koma kare kawunansu kawai basu A.G ba. Kafin a bar harabar kotun da anguwarma baki ɗaya dasu an musu mugayen raunuka sunata ihu da kururuwa. 

       Dan dole aka canja akalar miƙasu prison aka nufi asibiti dasu domin fara treating nasu. Da wannan damar Master yay amfani wajen yima master ɗan ta’adda allurar guba batare da kowa ya farga ba, yayi kuma hakanne domin ɗaukar fansar iyayensa tamkar yanda yay ƙudiri a ransa tun farko. Bayan anyi treating ɗinsu dole nan ma aka bar asibitin dasu zuwa asibitin cikin prison ɗin saboda tsaro ba tsoro ba. Dan duk da boren nan na jama’a akwai magoya bayan su A.G a gefe musamman ƙasashen ƙetare da suke kallon ƙazantar da su A.G ɗin ke aikatawa wadda jama’a ke tada jijiyoyin wuya a kanta ba komaiba. Za’a kuma iya yin amfani da wannan damar a kuɓutar dasu, duk da kuwa a prison ɗin ma dai bawai sakaran tsaro aka barsu da shiba. An sakasune cikin tsatstsauran tsaro da horo mai tsananin gaske da sai sun gwammaci mutuwa da da rayuwa. A yanda mutane ma suka jigatasu da raunikan ruwan duwatsu da wahala wasu a cikinsu sukai labari. 

             Abubuwan sun ɗan lafa kaɗan, sai dai an cigaba da cecekuce a kafafen sada zumunta dana yaɗa labarai musam akan abubuwan da suka biyo baya daga bakunan ahalin su A.G, tun daga kan matansu, ƴaƴansu, zuwa danginsu daketa fitaowa suna nuna ƙyama da nisanta kawunansu da su. Yayinda wasu keshan tsinuwa a wajen tsoffinsu da basu riga sun mutu ba irinsu Hajiya mama dake kwance a asibiti rai hannun ALLAH. Dan da ƙyar take iya gane wanda ke kanta. Sai dai bakinta bai gajiyaba wajen jan tsinuwa da ALLAH ya isa ga Halilu.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button