Uncategorized

TAKUN SAKA 48

     Koda su Ummi ma sukaje dubata bisa tursasawar Ummi ɗin da ƙyar ta ganesu tana darzar kuka da roƙon su yafe mata musamman ma Ummi. Ummi tasha kuka dan duk mai imani yaga yanda ƙafar Hajiya mama zuwa rabin jikinta sukai wani masifar kumbura dole ne ya tausaya mata. Ahakanma wai an samu anyi mata gyaran karayar datai a ƙugun a daren jiya a asibitin. Ba itaba. hatta su likitocin kamsu basu san adadin sumar da Hajiya mama tayi ba saboda azabar wahala. Fitsari kam ai ba’a magana ko fanfon birtzatse ya shafa mata lafiya.

     Ko’a jikin su Hibbah, dan ita hankalintama nakan mijinta da sam bataji ɗuriyarsaba yau ma. sai ganin data ɗan masa a tv sanda ake kotu da su A.G. Bisa jagiorancin Yaya Abubakar shima Abba aka kaisu suka dubashi. dan shima dai prison ɗin za’a miƙasa bisa hukuncin alƙali zaiyi shekaru ashirin a gidan yarin. Anan ko Ummi komai batajiba sai ma kallon kaɗan ka gani dataima Halilun. Hakama su Yaya Usman ko’a kwalar rigarsu tamkarma ba dubiyarsa sukazo ba. Basu wani jimaba suka koma gida abinsu.

___________________________________

       Tun Hibbah nasan ran Master harta cire rai, dan tsahon kwanaki biyar kenan babu shi babu alamarsa. Harma sun bar wannan gidan sun koma gidansu da yau Hibbah ta fara shiga. Duk da damuwar rashin ganin mijinta dake cin ranta haka ta danne ta nuna farin cikinta akan cigaban da yayunta suka samu. Dan ko gida sai sam barka komai yaji gishiri da magi. Sai fatan ALLAH ya sauki su Hafsat lafiya kuma.

        Sarai Ummi na lure da halin da Hibbah ke ciki na kewar mijinta amma ta fuske. Kowa yaƙi mata maganar Master ɗin ma a gidan dan ba’ason sanar mata baida lafiya kamar yanda ya roƙa a ɓoye mata har sai ya warke kan hankalinta ya tashi. Ba kuma dan ciwon ma kaɗai ya nisanceta ba. Harda shirye-shiryen ƙarin girma da zai samu shi da wasu tawagar jami’ai irinsu yaya Abubakar. Dan haka yay tunanin haɗewa da ɗan walimar cin abinci na ƙara’in bikinsu da ba’ayiba dana komawa sabon gidansu da yake fatan suyi rayuwa ta din-din-din shi da sauran ƴan uwansa.

          Sai da Ummi taga damuwar Hibbah na fitowa ƙarara akan fuskartane ta zaunar da ita tai mata nasiha da kwantar mata da hankali akan wani babban uzirine yasa Master ɓuya amma yana nan dawowa daga tafiyar da yayi nan kusa. Ta ɗanji sanyi, amma taji ciwon rashin sanar mata da yayi bai kuma nemeta koda a waya ba balle ta san tanada kima a garesa.

          Da wannan damar Ummi da Mama Jiddah amaryar Sheikh Aliyu Maina da Uwargida ran gida Maimunatu sukai amfani wajen gyare Muhibbat ɗin ciki da bai da kayan gyaran jiki dana fata gangariya da ƙamshi. Tare da zaunar da ita suka fara ɗora mata karatu na musamman akan aure da zamantakewar cikinsa. Haƙoƙin miji akan mace da na macen ma akan mijinta. 

       A gefe kuma kayan auren Hibbah da aka shirya tun lokacin auren a gidan da Master ya bada matsayin Muhammad Shuraim tuni an kwashesu an maida inda zasu koma ɗin an jere mata su tsaf.

★★

       A ɓangaren Master ma cike yake da tsanin kewa da buƙatar matarsa. Sai dai yayi ƙoƙari matuƙa ya danne wajen ganin yama Ummi kawaici dan itace da kanta ta buƙaci yabar Hibbah a kaita kamar kowacce mace gidansa ita da su Yaya Muhammad. Bazai iya musa musu ba, dan sunyi matuƙar ƙoƙarin a garesa. Hakan yasashi yin amfani da wannan damar shima yay nasa shirye-shiryen da ƴan ƙannensa bayan jiyyar daya sha ta gajiya da sauran raunin jikinsa.

        Abinda kuma bai sani ba su Habib gagarumin biki suke shiryawa tare da Abdull da su I.G dayay burin hakan akan auren Master sai dai ALLAH bai nufa ba. Dan haka yay ƙudiri da aniyar biyan bashi a yanzu bayan yayi tattaki har gidan Sheikh Aliy Maina sun bada haƙuri akan yanda abubuwa suka faru, kasancewar su Yaya Muhammad suma suna tare da Sheikh Aliy ɗinne akan zaman dama duk sai suka nuna babu komai ƙaddarace ai wadda ta riga fata. Fatansu dai ALLAH yasa hakan shine alkairi ga Master ɗin da Muhhibat a yanzun.

      Al’amarin kamar wasa sai ga Muhibbat ta cika watanni biyu a gida tana jiran tsammani. Tayi wani irin masifar ƙyau da haske dake bama kowa mamaki, su Zahidah na tsokanarta akan cikine. Ita dai bata tanka musu duk da tanajin fargaba har cikin ranta. Dan da gaske watanni biyun nan datai a gida bataga al’adarta ba sam. Sai dai kuma ita sam batajin ciwon komai a jikinta dan haka take fatali da batun nasu.

      Ummi kam a yawan barcin da Hibbahn keyi a kwanakin nan yasata zargin ko cikinne da ita. Sai dai rashin ganin sauran alamomi yasata ajiye zargin nata itama dai. 

           A randa Hibban ke cika wata biyu da sati guda a gida aka sallamo Hajiya Mama. Ƙin amsarta su Momy sukayi acan gidan dan haka yaya Abubakar ya kawota nan wajen Ummi. Ummi bata musa ba ta amsheta kodan yaranta da darajar Aliyun ta da bazata taɓa iya manta hallacinsa ba shi da Malam. Ɗaki guda aka warema Hajiya maman ta cigaba da jiyya. Su Yaya Muhammad suka ɗakko mai kula da ita acan ƙauye cikin ƴan uwanta da ƙyar. Ko sau ɗaya Hibbah bata taɓa leƙa ɗakin hajiya mama ba domin dubata. Hakama Ammar da Yaya Umar da sukafi kowa tsanarta. Ummi tayi nasihar harta gaji ta sanya musu ido kawai.

         Shirye-shiryen tarewar Hibbah ake sosai a gidan, dan kwanaki biyu kacal suka rage amarya harta sha lalli ƙafa da hannu, tare da kitso na musamman irinn ƴan maidugiri da wata ƴar da Jiddahn ya Sheikh ke riƙo ta fanin Umminsu tai mata. Gyara kam ta shasa harta gaji, dan bayan gyaran dasu Maimoon uwar gidan yah Sheikh ke mata a ɓangaren mamansu Zahidah ma sun gayyato shahararriyar mai haɗaɗun kayan gyaran jikin nan mai kamfanin *mg’s skin care*, tun daga kan mayuka, sabulai kala-kala na maida tsohuwa yarinya. *(08062991549)* akan farashi mai sauƙi da rahusa ta haɗa mata kayyaki na musamman da dorata akan kayan shafa dana gyara na mata masu aji ta kowanne fanni itama tana katalleta.

        Haka kawai yau Hafsat ta tashi da ƙwazabar son yin gasashen kifi saboda ƙwazaba irin tamai ciki. Kasancewar matar Yaya Muhammad ita kuma sam bata shiri da kifin yasa Hafsat tahowa sashen Ummi tayi dan maƙwafta sashen Hafsat da Maimunatu (Kausar) suke. Koda ta gayyaci Hibbah ta tayata ƙin zuwa tai, kamar wasa ƙamshi ya fara sirɗaɗowa falon Hibbah na kwance tana kallo. Da farko dai ta ɗan fara yamutse fuska har Ammar na tsokanarta da cewar gulma. Ƙin kulashi tai dan ita kaɗai tasan mi takeji a tsakkiyar kanta game da ƙamshin kifin nan. Ammar da bai fahimci halin da take a ciki ba ya miƙe yana mata gwalo ya shiga kitchen wajen Hafsat ɗin. Ko mintuna uku baiyi cikakku da shiga ba suka jiyo tamkar gudu a falon. Cikin hanzari suka leƙo dan Hibbah suke zargi dama.

        Hibbah da aman daya yunƙuro mata yaci ƙarfinta dole ta durƙushe tan gab da isa ɗakinta ta sakesa a matuƙar wahale. Kanta suka nufo da gudu cikin tashin hankali da tambayarta lafiya?. Ina bama tasan sunai ba. Dan da alama dai aman baizo da wasaba. Hatta Ummi dake ɗaki tana azkar na yamma da sauri tayo waje. Haka ma mai kulla da Hajiya mama babu shiri ta fito duk suka rufu akan Hibbahr datai matuƙar jigata. Dan ko aman yayi kamar zai tsaya da ƙamshin kifin ya sake shiga hancinta saita sake sabon yun ƙuri.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button