TAKUN SAKA 48

Fashewa tai da kuka jikin ta na rawa ta sake mamuƙe hanun Ammar dake riƙe da ita. “Y…ya…ya Ammar banaso ku fita da ki.f.in”. Ta faɗa da ƙyar tana sake sakin sabon kuka. Cikin sauri Hafsat ta nufi kitchen domin fita da kifin, yayinda Ammar ya ɗauka Hibbah ɗin gaba ɗaya sukai ɗakin Ummi dan a samu tabar jin ƙamshin kifin.
Yanda ta galabaitan dole ne ta baka tausayi, da taimakon Ummi ta gyara mata jikinta a toilet ɗinta da Ammar ya kaita can direct. Kuka take wiwi jikinta duk ya saki harda su ɗan zazzaɓi. Har yanzu kuma jin kamshin kifin take har tsakkiyar ƙwalwar kanta saboda tsaya mata da yay a rai. Ummi data gama gaskata cikine da Hibban ta kamota suka fito a toilet ɗin. Zaunar da ita tai a gado ta fita zuwa ɗakinta ta ɗakko mata wasu kayan. A falo ta wuce Ammar da Hafsat na gyara wajen da Hibbah ta ɓata.
Ummi na dawowa da kayan ta iske Hibbah harta kwanta. Ɗagota tai ta taimaka mata ta saka kayan tana jera mata sannu tausayin autar tata na ratsata.
“Ummi ki bani wani abun na shinshina ko zan daina jin ƙamshin banaso zan sakeyin amai”.
Cikin lallashi Ummi dake murmushi ta shiga shafa kanta bayan ta kwantar da ita a jikinta. “Tanee ki ciresa a ranki kawai shine zaisa kibar jin ƙamshin a hancinki, dan tuni Hafsat ɗin ma ta fitar da shi a sashen nan. Amma faɗamin mikike son ci?”.
“Ummi banajin yunwa, sai dai kozan samu tumatur masu ƙyau da suka nuna sosai zansha”.
“Abu mai sauƙi”.
Ummi ta faɗa tana miƙewa bayan ta kwantar da Hibbah. Cikin lokaci ƙanƙanin sai ga Ammar da duk yay kalar tausayi kamar shine mara lafiyan da manya-manyan tumatur masu ƙyau a ƙaramin bowl har kusan goma ya kawo mata. Dan anyi sa’a an kawo musu cefanen dama babu jimawa.
Sagade yayi yana kallon Hibbah nashan tumatur ɗin cikin rawar jiki tamkar wadda ta samu wani apple ko inibi. A wannan halin su Yaya Umar da suka shigo gidan matansu suka sanar musu suka shigo suka sami Hibban. Su kansu mamakin shan tumatur ɗin suka tsayayi har Yaya Umar na yima Ammar faɗa.
Amarairaice Hibbah ta ce, “Yaya inasone akwai daɗi”.
Yaya Umar zaiyi magana Ummi ta ɗan girgiza masa kai. “Karka damu Umar barta tasha. Tunda shi zuciyarta keso shi kaɗai zatasha a zauna lafiya inhar ya zauna.”
Shiru kawai sukai badan hakan ya musu ba. Hibbah na kammala shan tumatur ɗinta kuwa ta zame ta kwanta dajan bargo tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, nutsuwa na ratsata. Wahalar data sha yasa barci saceta cikin ƙanƙanin lokaci batare data shirya hakan ba.
Koda ta farka kusan bayan magrib garau ta tashi tamkar ba’ita ba. Sai dai ɗan rashin ƙarfin jiki da takeji shima bamai cutarwa ba. Salloli tayi ta fito falo inda take jiyo hayaniyar yayunta da matansu suna hira. Duk sunyi farin cikin ganinta garas. Suka shiga tambayarta jikinta tana amsa musu cikin shagwabar tata saba musu. Suko da kulawa suketa sake sonjin ko tana son wani abu da zataci. Kanta ta girgiza musu tana kaiwa zaune da faɗin, “A’a yaya ku kwantar da hankalinku zanci duk abinda aka dafa indai babu wancan abun na ɗazu (ko sunansa batason faɗa dan ma karta tuno). Sunji daɗin hakan suka sake mata addu’ar sauƙi mai ɗorewa. Daga haka suka cigaba da hirarsu tana lafe a jikin Umminta da tun ɗazun take cikin tsantsar farin ciki akan baiwar da ALLAH yay mata na albarkar auren ƴaƴan nata biyar reras kusan lokaci guda. Bata yarda tayi zancen cikin dasu ba dan batason ma zancen ya fita har sai Hibbah ta tare gidan mijinta. Shiyyasa tunkan aje ko’ina ta cewa Hafsat ma tai shiru da bakinta ko mijinta karya sani tunda ta lura Ammar shi dama bai fahimci komai ba garan????………….✍
*_MATAYEN ƘWARAI KUNA INA NE?._*
_Maza ku garzayo da gudunku ga ƴar zuru mamar zee-zee mai kayan mata na maida tsohuwa yarinya????????._
*Kayan matan ƴar zuru zasu maidaki shalele ƴar gaban goshin maigida koda kina da kishiya ƴar birnin shehu????????????*.
_Kayan ƴar zuru nada matuƙar sirrika da inganci irin wanda sai an gwada akansan na ƙwarai. Idan da ƙyautar gida akemiki a master room kikai amfani da kayan ƴar zuru Nigeria za’a baki harda jirigin sama na yawata ƙasashen duniya????????????_.
*MUNADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA*????????
Kaza akwai 10k
15k
5k
Tsimi 5k 10k
Matsi 5k
Gumba uku 2k
Zumar gorun tula syrup3k
Garuka 3k
Cicccibi 5k
Zakara 20k
Zabo20k
Humra
Turaren tsugunni
Butar tsarki
Maganin infection
Tsimin tabaje
Turaren al,ajab
*Muna maraba da maisayen ɗaya ko sari, kayanmu garantee ne in har basuyimaba zan maidama kudinka*.
_Address maberar jariri bayan FGC sokoto_
08068526455
*Zaku iya saving number ta domin ganin hajata*
Zaku iya samun mu amanhajar
Istagram
Yar_zuru_mamar_zeezee- kyn_mata.
Sai kunzo????????????????????????????????.
[ad_2]