HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Lumshe ido yayi Yana tunano ko awane Hali ayshah take ita data fisa Shan dukan ruwan.

A daddafe yayi kwana biyu agidan mum na jinyarsa a kwana na ukun ya shirya yace yaji sauqi makaranta zashi.

Kallon mamaki mum tayi Masa tace,

Sweetheart you’re not fully recovered… you’re still weak.,,I can see it in your eyes.

Atishawa Mai qarfi yayi tareda saka farin lallausan handkerchief ya tare hancinsa kafin ya ‘dago ya kalleta da lazy eyes dinsa yace,

Mum I’m fine.,,I promise.

Cikin kulawa da yar damuwa tace,

Ok my sweet boy,,but please take care..

Yes mum,,,,yace tareda ‘daukar wayarsa da key ‘din sabuwar motarsa ya sauko ya fice batareda ya tsaya bawa Davina amsar Murphy datake tambayarsa ba Dan shima nemansa yake Amma haryanzu wayarsa Bata zuwa.

Duk inda yake sakaran zai ganta ya Duba bai gantaba Nan take yaji jikinsa yafarayin sanyi..

Tunda yafara nemanta tagansa tayi saurin 6oyewa bayan wata mota tana kallonsa zuciyarta a sanyaye Amma hakanan taji dadin ganinsa yaji sauqi duk da dai tana iya ganin baida wani kuzari.

Tundaga ranar tafara 6oye Masa duk da baqaramin tirsasa zuciyarta takeba gurin aikata hakan.

Tun mum ‘dinsa na ‘daukar abin wasa saigata hankalinta yayi mugun tashi sbd wata irin damuwa da muguwar Rama data sako Nik ‘din agaba sbd rashin ganin ayshar gashi yakasa samun ko wane information akanta.

Sam shida kansa baisan son da yake Mata yakai hakaba Sai yanzu..

Iya bincike da lallashi mum tayi Masa yafa’da Mata damuwarsa Amma yaqi.

Yau tun 6 na safe yatafi makarantar kosu mum basusan da fitarsaba..

Bakin bus stop ya Parker motarsa zuciyarsa sanyaya da damuwar dayake ciki game da ita Dan yau jiyake kozai kwana ya yini agurin saiya ganta zai iya samun sukunin masifar da zuciyarsa take ciki.

Ahankali bacci ya ‘daukesa sbd rashin baccin dayake fama dashi na kwanakin.

A kunne yabar motar sbd Ac.

Sai 10 ta iso makarantar ana ajesu busstop ta fito ta nufi hanyarta cikin sanyin jiki sbd rashin kuzarin da itama take fama dashi.

Kamar daga sama ta hangosa kwance Yana bacci cikin motar yayi matuqar ramewa saitaji zuciyarta na neman karyewa tayi saurin juyawa tabar gurin.

Qarfe biyar na yamma ta gama lectures ta fito a galabaice sbd ranar azumi take..

Cak ta tsaya sakamakon ganin har lokacin Yana gurin saidai wannan time ‘din yafito jingine yake jikin motarsa yayi wani irin fadawa sbd yunwa da wahala Amma yaqi tafiya.

Kamar ance ya juyo Sai kawai idonsa yashiga cikin nata yayi saurin miqewa tsaye daidai Yana kallonta amarairaice.

Dakewa tayi ta matso tareda ra6asa ta wuce tashige bus tareda sunkuyar da kanta Dan karma su hada ido.

Binta yayi da lazy eyes ‘dinsa suna taruwa da ruwa sbd tunanin qila wani laifi yayi Mata.

Matsowa yayi da sauri zai shiga bus ‘din cikin tsautsayi yaron direban motar ya turesa sbd already motan yacika ya fa’di qasa cikin ruwan saman dake taruwa awurin Nan take kayansa da jikinsa ya lalace bai tsaya dubawaba ya miqe da sauri zaikuma matsowa aka tada motar sukabar gurin.

Motarsa yashiga da sauri yabi bayansu saigasu har anguwar su ayshah ‘din.

Tana fitowa motar tagansa Yana qoqarin parking ya fito.

Saurin wucewa tayi batareda takuma kallon inda yakeba.

Biyota yayi da gudu batareda ya tsaya kashe motarsa ba..,,

Sauri ta qara gabanta na tsananta fa’duwa daf da zata shiga kwanar layinsu saiga ya Umar…

Wata mummunar fa’duwa gabanta yayi ta saci kallon bayanta taga Sai zubo sauri yake Dan ya iso wurinta ta rintse ido zuciyarta na tsinkewa da tausayinsa.

Kallonta ya Umar ‘din yayi Yana son karanto firgicin daya gani tattare da ita.

Kamar ance ya Duba bayanta saiya hangosa Yana zubo sauri tareda tsalle Yana qoqarin fa’duwa sbd agwagi dasuka biyosa Sai tsalle yakeye Yana kallota karta 6ace Masa.

Kallonta Umar ‘din yayi cikeda zargi kafin yayi Mata alamar ta wuce da ido.

Sum sum ta wuce Amma saita kasa shigewa konar ta juyo.

Manyan agwagin dasuka fi girma Umar ya ‘dauka tareda jefa Masa cikin baqin ciki da takaicin ganinsa.

Baya yayi da sauri cikin tsoron agwagin cikin rashin sa’a Ashe yakai kwata sai gashi zaune cikinta.

Batareda 6ata lokaci ba ya yunquro yataso har lokacin idonsa nakan kwanar datake la6e tana kallonsa.

Qoqarin wucewa yake cikin takaici Umar ya fixgosa tareda wurgar dashi ya nunasa da yatsa cikin xafi yace,,

Zanbarka yau katafi Amma wlh duk nakuma ganin wannan kafirar fuskar taka cikin anguwar Nan saina yanka maka ita da kwalba..

Juyawa yayi zai wuce tayi saurin barin gurin tayi gida da sauri zuciyarta na wani irin nauyi.

 

 

Mamuh????

 

_dont forget to follow, vote and comments_
*_MAMUH GEEE_*

 

_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

 

*17&18*

 

koda Nik Yakoma gida ya tsaya gaban mirror yakalli kansa saiyaji hawaye sun ciko idanuwansa..
Tubewa yayi ya jefo kayan qasa ta windown dakinsa ya fa’da toilet yayo wanka Banda zazza6in wuya Babu abinda yakeji.

A daddafe ya saka kayan bacci black yashige bargo ya kwanta jikinsa na rawar sanyin zazza6i..

Qarfe Tara mum tashigo dakinsa Finn na biyeda ita tana ganin yanda yake shaking cikin bargo ta qaraso da sauri tana Kiran sunan Jesus..

Tallafosa tayi taji jikinsa da mugun zafi ta kalli Finn cikin tashin hankali tace,

quickly call Dr Finn.

Fiddo wayarsa yayi daga aljihu ya latsa Kiran Dr cikin gaggawa.

Shigewa yayi jikin mum ‘dinsa yana fiddo numfashi ahankali cikin azaba yace,

Mum I’m fine,, it’s just a fever,,I will get better soon there’s no need to call the Dr….

Cikin karyewar murya kamar zatayi kuka tace,

Quite.. you’re not fine my love and it’s not a normal fever,, you’re hiding something from me,,I can feel it.

Lumshe idanuwa yayi cikin sanyin murya qasa qasa yace,

Mum,,,,mum..i.i..I’m in love….I love someone.

Wat””””tafa’da da qarfi tareda kallon fuskarsa cikin rashin Jin dadi tareda rashin na’am da zancen cikin damuwa tace,

You can’t be in love my boy,, you’re too young for that and I ca….

Katseta yayi cikin sanyin murya da cewa,

I love her so very much mum,,,I can’t even imagine my life now without her mum…mum..I really want her for myself,i love her mum..I madly love h….

Rungumesa tayi cikin tausayinsa sbd dukkanin alamu sun nuna Mata baqaramin so yakewa kowaceceba..

Share Masa hawaye tayi tana adduar Allah yasa ko wacece kada tayi amfani da wannan zazzafar soyayyar da Nik yake Mata ta cutatar Mata da yaro.

 

Kwanansa biyu Yana zazza6i Mai zafi ko qasa baya iya saukowa bare ya fita,,
Mum dinsa kuwa hutu ta dauka Dan bawa ‘dan lelenta kulawa hakama ‘yan uwansa wannan karon dukkaninsu sun matuqar tausaya Masa sbd yayi matuqar sanyi kamar ba Nik ba danko irin muguwar sakuwar dayake acikin gidan ta rage kullum Yana kwance.

 

Duk iya yanda take danne damuwarta saidata bayyana a jikinta sbd ramar datayi su husna sunyi faman tambayar harsun gaji Amma alamarin bamai kar6uwa bane ko a zuciyarta bare fa’duwa.

Kwananta biyu kotaje makaranta Bata gane komai sbd dukkanin nutsuwarta ta tarwatse Wanda Sam takasa samun kuzari ko qarfin tattarota.
Ahaka take lalla6awa har tsawon kwana biyu.

Yau Bata samu bus da wuri ba shiyasa tayi yammacin dawowa gida,,

Ahankali take tafiya cikin nutsuwa duk da kwanakin nutsuwarta rawa take,,

Daf dazata shiga kwanar layin gidansu taga su ya Umar taredasu Yaya abbakar kusan su shida kowanne da abun duka jikinsu har rawa yake bama Kamar ya Umar ‘din da idanuwansa yafi nakowa rufewa da 6acin Rai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button