TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Ayshah???
Na’am”’tace a sanyaye batareda ta ‘dagoba yace,
Na yarda dake nasan bazaki iya ta6a sa6a Mana ba ko take doka da umarnin mu Dan haka ga garga’di da umarni Mai qarfi,,,,daga yau ko hanyar dayabi karki Kuma kallo bare har wata magana ta hadaku harma afara Kuma irin wannan zargin Dan ni ko maganar wani kafiri banaso acikin zuri’ata bare har irin wannan mummunar zancen ya tabbata..
‘dago Kai tayi ta kallesa tareda cewa,
To baba insha allah.
Miqewa tayi ta bar palon ahankali ya Umar yabita da kallon tuhuma danshi yana ganin abubuwa da dama datake 6oyewa Amma saiyasa ta bayyanasu da kanta agaban kowa na gidan.
Koda wasa dama batai gangancin tunanin bacci zaizo Mata ba hakanan ta kwana cikin tunanin wane Hali Nik yake ciki.
Koda gari ya waye taje gaida umminta saitaji duk jikinta ya da’da sanyi sbd ganin ga dukkan alamu ma umminta na cikin tunani da fargabar Kar zancen jiya ya tabbata.
Gaida ummin tayi cikin sanyi tareda kallon nuratu dake Mata kallon tausayi tana gaisheta.
Amsawa tayi tareda kallon ummi tace,
Ummi zan tafi makaranta..
Cikin kulawa da sanyin jiki ummin tace,
Ayshah Dan Allah karki bari zuciya takaiki ga Dana sani da muguwar rayuwa.
Hawaye taji sun taho Mata Dan tasan saidai Kuma wani ceto daga Allah Dan Mai Sha tarigada Tasha.
Zama tayi tareda kar6ar cup ‘din kunun tsamiyar da ummin ke miqo Mata ta kar6a badan zata iya sha ba saidan kadata kuma bawa ummin damar wata damuwar.
Abbanta ne yashigo tareda sallama ta sunkuyar dakai ta gaidasa cikin sanyin murya..
Amsawa yayi kadaran kadahan kafin ya zauna kan tabarmar kusada ummin Yana cewa,
Ki qara kiyayewa sbd gudun jawo fitina da tashin hankali tareda 6acin suna acikin zuriar gidan nan Dan yanxu ina amfanin irin hakan tunda shi yaron sun Masa mummunan duka sun barosa can kangon gidan bayan layi sbd……
Wata mummunar sarqewa tayi tafara tari Mai qarfi sbd gigitar da zancen baban yasata.
Saurin miqa Mata ruwa nuratu tayi tana Mata sannu..,
Baba da ummi kuwa kallo suka bita dashi fa’duwar gabansu na tsanantuwa .
Miqewa tayi ahankali tace,
Na tafi..
Allah tsare ummi tace a gajerance baba kuwa ko amsa Mata baisamu yiba sbd damuwa da fargaba.
Bakin titi ta tsaya cikin zurfin tunanin rashin sanin abin yi….
Kusan Rabin Rabin awa tashare bakin titin Dan Sam zuciyarta taqi barinta tafiya…
Juyawa tayi ta canza hanya zuwa bayan layin gidansu.
Bakin wani kangon gida ta tsaya da kusanma anmaidasa bola sbd dadewar da’akayi ba’a cigaba da gininsaba.
Jujjuyawa tayi taga Babu mutane sosai agurin saitayi saurin shigewa gabanta na tsananta fa’duwa Dan jikinta har rawa yake.
Cak ta tsaya tareda zubewa qasa ba shiri…
Kwance yake baisan inda kansa yakeba cikin jini duk gabaki ‘daya kamannunsa sun canxa da sbd duka da wahala.
Da rarrafe ta qarasa gurinsa tareda tallafosa jikinta ta fashe da kuka Mai qarfi tana Kiran sunansa.
Kuka take sosai kamar ranta zai fita Dan tabbas batasan sonsa yayiwa zuciyarta mugun kamuba Sai yanxu data gansa cikin wannan mummunan halin….
Jin tayi kamar ya motsa tayi saurin ‘dagowa suka ha’da ido sabbin hawaye suka gangaro Mata ta fara girgixa Kai cikin kuka tace,
Why….why…why Nik,,,,why did you choose to make me suffer by seeing you like this????
Duk da a wahalce yake danko hannunsa bai iya motsawa Amma ganinta yakawo farin ciki sosai acikin ransa barema dayaga halinda tashiga ganinsa haka..
Wani mugun yunqurin amai yayi saiga jini na fitowa ta bakinsa..
Zaro manyan idanuwanta dasukai ja tayi takalli jinin takuma maida kallonta kansa taga Yana numfashi sama sama
Da gudu ta fito tareda mantawa da wani tsoron Kar aganta tasamo taxi itada mai taxi ‘din suka sakasa mota..
Baya tazauna taredashi duk da numfashinsa zuwa time ‘din yakusa ‘daukewa…
Damqe hannunta yayi cikin nasa hawayen wahala na gangaro Masa murya qasan maqoshi yafada Mata sunan asibitin dazata kaisa.
Shihhhhhhhh don’t talk pls”””””””tace Masa qasa qasa cikin kunnensa tareda qara damqe hannunsa tanajin zafi da ra’dadin ciwonsa na shiga zuciyarta.
Asibitin daya fa’da can takaisa suna zuwa akai emergency dashi Dr naganinsa yayi saurin zare farin glass ‘dinsa cikin tashin hankali da mamaki yace,
Oh my God,,Nik ne wanna ai…
Fitowa yayi tareda kallon nurse ‘din data biyosa yace,,,
Waya kawo patient ‘din dake ciki?
Ada sauri ta nuna Masa ayshah dake zaune ta sunkuyar dakai sbd kukanta dayaqi tsayawa Dan yanda taga hankalin nurses ‘din dasuka kar6esa ya tashi tasan ba qaramin Hali Nik ‘din yake ciki ba.
Qarasowa gabanta Dr yayi tareda kallonta dakyau kafin cikin mamaki yace,
Kece Kika kawo Nik?
Kai ta ‘daga da sauri cikin tsoron Mai zaice yasamu Nik ‘din.
Kallon tuhuma yakuma jifanta dashi kafin yace,
Ina muma ‘dinsa da….
Bata Bari ya qarasaba cikin fargaba tace,
Please Dr kafadamin idan zaiji sauqi..
Yes zai zamu sauqi but….
Ok Dr ngd Amma Dan Allah idan kanada number mum ‘dinsa kafa’da Mata.
Share hawayenta tayi tajuya batareda tabari yakuma wata magana ba.
Kwance take nurse ‘din da’aka ‘dauko Mata tun Daren jiya Dan kulada ita tana zare Mata drip ‘din dake hannunta har lokacin idanuwanta dasukai mummunar kumbura Basu daina zubar da hawayeba..
Finn ne akusada ita ya kwantarda kanta kan kafa’darsa Yana shafa kanta alamar rarrashi.
Mr Aiden ma daya iso da safen zaune yake kusada ita Davina na zaune kusadashi tashige jikinsa…
Dukkaninsu kallo ‘daya zakayi musu kasan mummunan alamarine yasamesu Mai kamada mutuwa.
Waya Mr Aiden ya Kuma ‘dagawa akaro na ba adadi yakuma Kiran police yayi Koda akwai wani update Amma still Babu.
Wayar mum ce tafara ringing Amma ko qyafta idanuwanta batayiba bare ta motsa…
Finn ne yayi qarfin halin ‘dauka tareda saka loudspeaker…
Gabaki ‘dayansu atare suka zabura Jin abinda Dr yafada mum kuwa tuni takai qofa jiri na ‘dan ‘dibarta Amma batajin zata iya jira.
Da sauri Finn ya riqota suka ‘dunguma mota gabaki ‘daya Sai asibitin.
Tashin farko da mum taga halinda Nik ‘dinta ke ciki Sai ganin sukayi ta yanke jiki Saida dadinsu yayi saurin riqota ta fashe da kuka tana kallon yanda Nik dinta ke numfashi cikin azaba da wahala duk da har lokacin tashiba.
Saidata shaqi kukanta kafin ta miqe Finn ya Kama hannunta suka nufi office ‘din Dr suka bar dad da Davina a room ‘din.
Dogon bayani Dr yayi musu akan Yana tunanin mummunan dukane akayiwa Nik ‘din Wanda harya ja Masa internal bleeding Dan qila andaki kansa.
Share hawayenta tayi ta Kuma kallon Dr tace,
Where did you find him I mean who brought him here?
It was a lady,,, she was all covered by…..I think she’s a Muslim.
Tafasa zuciyar mum tafara Nan take 6acin ranta da baqin cikinta suka danne damuwar dayake ciki…
Miqewa tayi tareda kallon Finn dashima yacika yayi fam dajin cewar ninja lady ce tayiwa Nik wannan mummunan aikin.
Kallon Finn tayi bayan sunbar office ‘din cikin tuquqin da zuciyarta keyi tace,
I want them to pay double for wat they’ve done to my poor darling boy…make them cry and regret their lives.
Yes mum””””yafada Yana fiddo wayarsa aljihu Dan making call.
Da daddare ya farka Nan dukkanin familyn suka kewayesa suna basa kulawa cikin so da qauna musamman mum da kamar tayi ihu takeji duk ya motsa taga ya rintse Ido alamar azaba.
Da daddare bayan Finn da Dad ‘dinsa sun taimaka Masa yayi wanka ya saka kayan bacci ya kwanta mum ta lullu6esa ya lumshe idanu alamar bacci duk suka fito Dan tafiya gida.