HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Lumshe idanuwansa yayi tareda sakin murmushin da iyakacinsa zuciya ya tuno baby face da fararen idanuwanta lokacinda take kuka tana Kiran sunansa.

Ahankali cikin maqoshinsa yace’
I love you my sweet ninja lady…

 

 

Washe gari ma data fito kasa wucewa makaranta tayi saita samu kanta dabin umarnin zuciyarta ta nufi asibiti gabanta na tsananta fa’duwa Amma ba yanda ta iya Dan batajin zata iya Kai yamma batareda taga halinda yake ciki ba..

Baba alhaji da baba shehu tareda Yaya Ahmad da Yaya abbakar ne suka dawo daga gurin wani taron fatawa…

Daf dazasu Kai anguwarsu wata baqar mota Tasha gaban taxi ‘din dasuke ciki kafin suyi want motsi qartin maza majiya qarf suka fito da bindigogi suka tasa qeyoyinsu baba alhaji dayaso gardama aka ‘dibesa wani mummunan Marin dayasashi ha’diye maganar dayaso yi sukabar gurin da mugun speed.

 

Kodata isa asibitin Kai tsaye emergency ta nufa cikin sauqi saiga ‘daya daga nurses ‘din dasuka kar6esa a jiyan ta tareta cikin sanyin murya ta tambayeta room ‘din dayake.
Nuna Mata tayi ta nufi ‘dakin gabanta na tsananin bugawa.

Nesa ka’dan da ‘dakin ta tsaya tareda qurawa qofar ‘dakin ido tana qoqarin controlling matsuwarta tason ganinsa.

nurses biyu taga sun fito ‘dakin mace da namiji tayi saurin qarasawa ta tare macen cikin sanyi tace,

Please patient ‘din dake ciki yaji sauqi kuwa?

Kallon up and down tayi Mata kafin tace,

Eh Amma dai yanxu mun Hana kowa shiga gurinsa har family ‘din sbd munason yasamu isashen hutu.

Bin bayan nurse ‘din tayi da kallo bayan ta wuce tana tunanin kenan ba kowa a ‘dakin.

For the first time taji wani farin ciki bayan tsawon lokaci..

‘dakin ta dosa gabanta nacigaba da fa’duwa.

Tsayawa tayi bakin qofa tareda rintse ido tasaki numfashi ahankali tareda tattaro Yar nutsuwa ta tura qofar ahankali.

Cak ta tsaya sbd idanuwanta dasuka sauka cikin nasa Yana kwance ya qurawa qofar Ido kamar Daman yasan itace zata shigo..

Tashi zaune yayi batareda ya ‘dauke idanuwansa cikin nataba..

Har ya iso gabanta Bata motsaba sbd garkuwar jikinta da idanuwansa suka kaririya..

Hannunta ya riqo ya jawota ciki ya rufe qofar har time ‘din batayi wani qwaqwaran motsiba.

Zaunar da ita yayi bakin gadonsa tareda durqusawa gabanta idonsa cikin nata yace,

Ayeeshah did you came to hia see?

‘daga Masa Kai tayi sbd batada kuzarin magana..

Wani qayataccen Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka bayyana ka’dan..

Tasowa yayi ya zauna kusada ita yakai bakinsa saitin kunnenta da wata kasalalliyar murya yace,

Did you love me ayeeshah?

Shiru tayi tareda sunkuyar dakai qasa.

Murmushi yakuma saki yace,

Please talk to me ayeeshah..

Juyarda Kai tayi still batace qalaba.

Murmushi yayi tareda zubewa qasa ya riqe kansa Yana juye juye cikin tsananin azaba.

A ki’dime ta sauko gabansa tana Kiran sunansa cikin tashin hankali da tsoro Amma saitaga Yana qara mimmiqewa saikuma yayi dif ba alamar numfashi ataredashi.

Kansa ta rungumo batareda tasaniba tafara kuka tareda Kiran sunansa…
_*I love you Nik*_,,,pls wake up..
_*I love you so very much*_…..

Miqewa tayi da sauri Dan kirawo Dr taji anriqo hannunta tayi saurin juyowa sukai Ido biyu Yana sakar Mata wani hot smiling…

Kallon mamaki take Masa da sauran guntayen hawayenta Dan tagano da gangan yayi hakan Dan ta fa’di abinda yake son ji..
Wata fitinanniyar kunyace ta rufeta tayi saurin juya Masa baya tana sauke numfashi ahankali…

Zagayowa yayi tareda matsota sosai danshi Sam bai ‘dauki hakan komai ba…

Matsota sosai yayi jikin bango tareda duqo da fuskarsa daf da Tata har numfashinsa na mugun ha’duwa ya ‘daga hannu ahankali ya cire Mata niqaf tai saurin rintse ido… fuskarta na bayyana wani sahirtaccen murmushin daya Kuma tafiya dashi.

Bakinsa yakai daidai kunnenta cikin wata kasalalliyar murya yace,,

You finally said it my love…

Sake tamke idanuwanta tayi sbd Jin kalar muryar dayayi amfani da ita ba qaramin shigarta tayiba.

Kallon dogayen eye lashes ‘dinta yayi yace,

Will you marry me ayeeshah…

‘daga Masa Kai tayi ahankali sbd tuni ta manta da wani banbancin yare da addininsu.

 

Su baba alhaji kuwa wani qaton gida aka kaisu suna shiga aka ‘daddauresu tareda jiqasu tsaf da ruwan qanqara kafin aka fara jibgarsu baji ba gani.

 

 

Mamuh????
*_MAMUH GEEE_*

 

_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

 

*21*

Tsayawa Finn yayi akansu Yana kallonsu cikin wulaqanci ganin har lokacin da sauransu ya juyo ya kalli tiger yayi Masa alama da ido…

Kallon yaransa tiger yayi Sai aka Kuma ‘debo ruwan qanqanra a qaton bucket aka Kuma jiqasu tareda cigaba da dukansu..

Iya dakuwa Kam sun daku bama kamarsu Yaya abbakar dasuke samari anfi dukansu duk da dai Suma su baban ba a raga musu ba…

Sake kallonsu Finn yayi yaga sun bugu yasaki murmushin qeta tareda fiddo wayarsa ya ‘daukesu yaturawa mum kafin yakirata yace ta duba..

Dariyar Jin da’di tayi lokacinda taga hoton takira tace a kaisu inda aka ‘daukosu a watsar..

 

Zamewa tayi daga rumfar dayayi Mata takoma bakin gado ta zauna kanta a qasa tana kallon dogayen fingers dinta..

Dawowa yayi kusada ita ya zauna shima ya qurawa hannun nata ido..

Ayshah please lets get married before informing our families about us…

‘dagowa tayi ahankali takallesa ta kawar da idonta kafin ahankali tace,

No Nik…I can’t marry you without my family’s approval.. besides that I’m Muslim you’re Chris…..

Katseta yayi da cewa,

I’m ready to convert my love….I want to become Muslim too…

Kallonsa tayi idonta na cikowa da hawaye sabuwar soyayyarsa na qara shigarta sbd ganin yanda idonsa ya rufe bayako tuna masifar dake gabansu ta dukkanin 6angaren biyu…Dan tasan gidansu sun gwammace ta mutu dasu barta dashi..

I love you ayeeshah…

Juyarda Kai tayi tareda sakin 6oyayyen murmushi..

Fira yafara yi mata ahankali Yana Bata lbarinsa saidai tayi murmushi kawai batareda tayi maganaba.

Mantawa suka da komai da kowa Saida sukaji knocking tayi saurin miqewa tsaye gabanta na fa’duwa jikinta na rawa..

Kallonta yayi tareda sakin qaramin murmushin daya bayyana white teeths ‘dinsa qasa qasa yace,

Wait hia…

Qofar ya 6ude ahankali saiyaga nurse ce yasaki ajiyar zuciya ahankali tareda juyowa ya kalli yanda ayshan tayi zuru duk saiyaji tabasa tausayi ya matso kusada ita yakai bakinsa saitin kunnenta zaiyi magana tayi saurin zillewa ta Fice ‘dakin da sauri tana Jin farin ciki na shigarta tako ina.

Shafa kansa yayi tareda kwantawa a gado Yana Jin farin ciki Mara misaltuwa.

Tundaga nesa ta hango qofar gidansu da kamar mutane gabanta yayi fa’duwa ta qarasa a darare..

Su Yaya sani dasu babanta ne ke qoqarin shigardasu baba alhaji cikin gida dukkaninsu ba kyan gani kawunansu da fuskokinsu a kumbure da jini a kayansu..

Yawu ta ha’diye daqyar tashigo gidan Nan ta tararda kowa hankalinsa a tashe su husna ma harda kuka ganin mummunar aika aikar da akayiwa su baban.

Sosai itama hankalinta ya tashi Dan koba’a fa’daba tasan wannan aikin mum ne..

Har dare gidan ba da’di Dan kowa na cikin jimami da baqin ciki..itadai Bata kosanyin wani qwaqwaran motsi sbd tsoron Mai zai biyo baya.

Har akai kwana biyu ba’ai zancen komaiba kan al’amarin Kuma tun ranar Bata fitaba sbd tsoro da fargabar abinda zai biyo baya duk da ba qaramin tausar zuciyarta takeyiba akan son sanin ya jikinsa yakeba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button