TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Yau kwana hudu da afkuwar tsautsayin su baba..
Matuqar zafi gidan kusan kowa ya ‘dauka musamman matasan gidan wannan karon ko baba malam ya ‘dau zafi matuqa….
Shiyasa ya tarasu yau kowada kowa..
Gyara Zama yayi tareda kallon ayshah murya a karsashe yace,
Ayshah Kinga abinda wa’innan mutanen sukayi Mana ko?
Shiru tayi gabanta na bubbugawa da sauri..
Cigaba yayi da cewa,
Duk bazanyi wani tashin zanceba ko dogon zance auren Umar da ayshah nasaka Nanda wata biyu kowa yaje yafara shiryawa Kuma nijar zasu koma bayan auren nagama magana kowa zai iya tafiya.
Takaici ne ya turniqe Yaya Umar Dan so yayi ace Nanda sati ‘daya a ‘daura auren..
Iyayensu da sauran ‘yan gidan kaf sunyi na’am da hukuncin baba malam ‘din Dan tsoron abinda zai iya biyowa baya.
Ayshah kuwa jitayi hankalinta yayi mummunan tashi hawaye yaciko idanuwanta jikinta har rawa yake ta miqe ko gani batayi sosai tabar palon.
Kuka take sosai cikin qaramin sauti zuciyarta na tsananta shiga qunci..
Kamar munafuka takoma cikin gidan ko fitowa Bata cikayiba..hakama zuciyarta a matse take dason ganinsa.
Zaune take akan carpet ‘din sallah kaman kullum tayi shiru idanuwanta a lumshe..
Zama kusada ita taji anyi ta bu’de idanuwanta ahankali ta sauke kan nuratu…
Qasa qasa da murya nuratu tace,
Anty ayshah jiya Da ina dawowa daga makaranta nagansa acikin anguwar Nan..yauma Dana dawo nagansa.
Qurawa nuratu jajayen idanuwanta tayi gabanta na duka da qarfi….
Muryarta na rawa tace,
Kinfa’dawa wani kingansa?
Girgixa Kai tayi tana kallon ayshahn tace,
Anty ayshah kina sonsane?
Hawayen dasuka gangaro Mata ta goge da bayan hannu tace,
Ina sonsa nuratu..
Dafata nuratun tayi cikin danne mamakin da tausayawa tace,
Anty ayshah karki Bari zuciya da shai’dan suyi galaba akan tarbiyar da iyayenmu sukai shekaru suna bamu.
Cusa kanta tayi tsakiyar qafafunta ta bawa hawayen datake dannewa Daman kwarara..
Washe gari shiryawa tayi a sanyaye Dan batada tabbacin za’a barta cigaba da karatun duk da tuni ya fara wargajewa.
Cikin ikon Allah ba’a hanata tafiyaba saidai tana fitowa titin anguwarsu taga motarsa ajiye gefen titi nanta ha’diye wani yawun tashin hankali Dan tabaro su Yaya Umar dasu ya Ahmad qofar gida suna Shirin fitowa…
Tabbas idan haryana cikin anguwar akwai yiyuwar su gansa Kuma tasan wannan karon bazasui Masa Mai kyauba.
Juyawa tayi da sauri taking cikin layin saigasu sukuma sun fito layin tayi saurin shigewa soron wani qaramin gida..
Jitayi hayaniya ta kaure da sauri ta leqo saita hangosa tafe izuwa gurinsu batareda ya ankare dasuba.
Ya sani yafara ganinsa ya zabura tareda nunawasu Umar shi…
Qatuwar spanner dake hannun ya abbakar dazai gyara mashin ‘dinsa ya saitashi ya jefa Masa Sai a goshinsa ba zato yaji saukar qarfe Nan take goshinsa ya fashe ya ‘dago lazy eyes ‘dinsa dasukai jan azaba yakallesu duk da yaji tsoron ganinsu bayajin zai iya guduwa ko tafiya batareda yau ya gano gidansuba.
Tsayawa yayi jini na fita a goshinsa ya kalli sani daya shaqo kwalar rigarsa Yana huci.
Azafafe yace,
Uban me kakeyi anan?
Kallo yabisa dashi sbd baisan meyake fa’daba..
Mari Umar ya wanka Masa akan kyakkyawar fuskarsa dayakejin kamar ya zuba Mata batir..
Yace,
He said wat are you doing hia you monkey fool.
Kallon Umar ‘din yayi akaro na farko dashima yaji tsanar wani ‘dan Adam Kai tsaye yace,
I came hia to see my love.
Ture sani Umar yayi da qarfi ya shaqo wuyan Nik ‘din yace,
Wh…wh..who is your love?
Ayeeshah””””ya fa’da Kai tsaye ba tsoro a idanuwansa.
Hannu ya dunqule yakaiwa Nik wani mugun duka Saida bakinsa ya fashe.
Wani dattijo ayshah tagani zai wuce tayi saurin Shan gabansa tana hawaye tace,
Baba Dan Allah kaga wasu can suna fa’da Dan Allah ka hanasu karka Bari ayi fitina.
Juyawa yayi ya kalli gurin daidai sun nanna’de rigunansu zasu cire takaicin dukan daakayiwa iyayensu dattijon yayi saurin tarewa tareda matsarda Nik dake tsaye baida alamar motsawa gefe yace,
Haba Kuna ‘yayan musulmai ‘yayan manyan malamai zakuyi Abu irin na jahilai…
Meyayi zafi haka dabazaku Kira hukuma ba Zaku ‘dauki mataki da hannunku…
Fa’da yahau yi musu sosai suka basa hkr tareda barin gurin sbd duk zafin ransu sunada tarbiyar girmama babba sosai Koda basusanshiba.
Juyowa yayi ya kalli Nik yace,
Kaima ka wuce tunda Suma sun tafi..
Juyawa yayi ahankali yabi bayansu duk da baisan abinda mutumin yafadaba…shidai yau alqawarine yayiwa zuciyarsa saiyaganta Dan haka zaibi bayansu saiyaga gidansu..
Daf dazai shiga kwanar yaji anriqo rigarsa ta baya yayi saurin juyowa sukai Ido biyu ta juya yabiyota da sauri Yana Kiran sunanta Amma taqi tsayawa.
Saida takai bakin motarsa ta tsaya tareda juyowa ta kallesa taga yanda goshinsa da bakinsa ke jini ta ‘dauke Kai tareda ‘daure fuska ta nuna Masa motarsa tace,
Leave…
Da sauri ya kalleta zaiyi magana tace,
Go… please..
Idanuwansa ne suka ciko da hawaye ya kalleta kaman zaiyi kuka yace,
Ayeeshah please don’t ask me to leave because I can’t….
Rintse ido tayi cikin ra’dadin ganin jininsa na zuba ta sake juyar dakai tace,
Please Nik go…
I don’t want to lie to myself again..
I don’t want to continue believing in a fake dream…
My parents fixed date for my marriage with someone…..
Wani mugun jiri ya ‘dibesa dama jurewa kawai yake Dan tuni yakejin jirin jinin dayake fita a goshinsa…
Hawaye taga sun 6alle Masa yayi ya ‘dago lazy eyes ‘dinsa taga sun canza launi tayi baya ka’dan ba zato taji ya damqo hannunta tana fixge da qarfi yakuma damqota tafara qoqarin qwacewa Amma takasa Dan mugun riqo yayi Mata ita batama ta6a tunanin yanada qarfin dazaiyi Mata wani riqo takasa qwacewa saigashi yabata mamaki..
Da gudu wani Dan sauri dake bakin titin ya isa yafadawasu Umar dake qofar gida suka dungumo a guje daidai lokacinda ya turata mota tana tirjewa yabar gurin da mugun gudu da ita.
iska Umar ya daka da qarfi Yana cewa,
Wlh duk yayi kuskuren ta6ata ko sauke haushi akanta saina nayi ajalinsa.
Gida suka koma suka sanar da iyayensu Nan hankula suka qara tashi suka ‘dunguma station don Kai report.
Gudu yake sosai har lokacin idanuwansa basudaina hawayeba jiyake kozai rasa ransa bazai ta6a Bari arabasa da ayshah ba…
Kuka take sosai itama ahankali batareda takalli gefensa.
Fita gari yayi ya qarawa motar gudu tayi saurin kallonsa tareda fashewa da wani sabon kuka zuciyarta na karyewa gabanta na tsananta fa’duwa.
Awa ‘daya da rabi saigasu a wani babban gari dabazata iya cewa inane ba.
Anguwar dasuka shiga tasata ‘dan sararawa da kukanta Dan lurada kamar anguwar duk malamai ne da almajirai tareda masu ‘daukar karatu.
Kallonsa tayi taga fuskarsa tayi jajir sbd azaban ciwon dayakeji akansa hakama jinin dake goshinsa duk ya bushe a fuskarsa…
Wani mugun tausayin kansune yakamata Dan Sai a lokacin ta lurada muguwar ramar dayayi..
Parking yayi tareda juyowa ya kalleta tsowon minti goma murya a sanyaye yace,
Ayeeshah can you please come inside with me..
Goge jajayen idanuwanta dasuka kumbura tayi tareda kallon qofar gidan ta ‘daga Masa Kai.
Bu’de motar yayi yafito ya zagayo ya bu’de Mata ta fito jiki ba qwari ga idanuwanta da Bata gani sosai dasu sbd kuka.
Babban palon dake zauren gidan yashiga ga mamakinta saitaji yayi sallama duk da kusan a birkice yayita Saida takusan fa’duwa sbd mamaki…