HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Babban mutum tagani zaune cikin shigar babban malami Yana karatun wani littafin larabci Yana ganinsa yasaki murmushi tareda amsa masa sallamarsa Yana qara gyara Masa yanda take daidai.

Zama yayi a qasa kusada qafafun malamin tareda fashewa da kuka ahankali….

Subhanallah…..sheik abdallah yace da sauri Yana kallon Nik ‘din cikin kulawa yace,

Wat is the matter Muhammad?

Kuka taji itama taji ya qwace Mata sbd sunan dataji ankirasa dashi na Muhammad.

Shiru shaikh abdallah yayi Yana sauraran kukansu na tsawon mintuna kafin Nik ya ‘dago manyan lazy eyes ‘dinsa ya kalli Ayshah cikin sanyin murya yace,

Ayeeshah….

Bata ‘dagoba haka zalika Bata amsa ba har lokacin kuka take..

Ayshah please let get married today…

Sabon kuka tasaki tareda miqewa da sauri zata bar gurin yayi saurin Shan gabanta tareda zubewa qasa ya riqe qafafuwanta..

Gyara murya shaikh yayi tareda Kiran sunanta cikin nutsuwa yace tadawo ta zauna.

Ba musu tadawo a sanyaye tazauna hawayenta na tsananta gudu..

Ayshah ke musulma ce Kuma ‘yar malamai Masana addini kamar yanda yanda Muhammad yayimin bayani..

Muhammad yazo Nan kwana biyu dasuka wuce ya bayyanamin komai akan qaunar dakukewa juna Kuma aranar ya kar6i musulunci ya kar6i kalmar shahada Kuma daga ranar kullum saiyazo Nan garin koyan abinda ya danganci addinin musulunci…
Amma bai za6i sunaba yace kece Zaki za6a Masa suna Kuma ya tabbarminda qalubalen da fitinar dake gudanuwa a tsakanin gidajenku Dan haka ya bayyana buqatarsa tason a na ‘daura muku aure Dan shika’dai ne zai kawo qarshen fitinar dake tasowa..

Girgixa Kai tahau yi tana cigaba da kuka duk da zuciyarta cike take da muguwar soyayarsa musamman yanzu dataji ya musulunta…Amma bazata yarda suyi aure yanxu ba Saida yardar iyayensu.

Matsowa yayi gabanta a susuce yace,

Please ayeeshah say yes,,,I promise I won’t do anything to you until everything is right… please ayeeshah I beg you in the name of Allah…

Rintse idanuwa tayi hawaye nacigaba da xubo Mata ta miqe tsaye tareda juya Masa baya dan matuqar taci gaba da sauraransa zuciyarta na daf da karyewa…

Sake zubewa qasa yay ya riqe qafafuwanta Yana fidda sautin kuka ahankali jikinsa har rawa yake sbd wani mugun zazza6ine ke cin jikinsa Amma bayaji alokacin.

Jin kuka yake sosai zuciyarta takasa controlling kanta ta durqusa da sauri gabansa itama tana tsananta kukanta.

‘dagowa yayi fuska jajir ya bu’de baki daqyar yace,

Ayeeshah please…..

‘daga Masa Kai tayi da sauri cikin tsananin sonsa da tausayinsa..

Thank you… thank you…yafada cikin farin ciki tareda juyowa gefen shaikh saiyaga baya palon…fita yayi da sauri kaman zai Fadi yakirowosa Yana kallon tsakiyar idanuwanta yace,

Shaikh she accepted… please get us married today…

Kallon ayshah shaikh yayi ta sunkuyar dakai yace,

Allah yabaki ladar wannan jahadin ayshah,,Kuma Allah ya kawo haske a rayuwar aurenku yakuma shirya iyayenku sanadin wannan auren..

Amin tace axuciyar na bugawa very fast..

Kallon Nik dake faman murmushi yayi yace,

I will send her inside now you’ll see her after the fatiha…

Ok…yace Yana kallonta cikin farin ciki..

Wait shaikh let her choose a name for me..

Kallonta sukayi su duka Dan sauraron sunanda zata fa’da ahankali cikin sanyin murya tace,

*_DEEN_*….._*NURADEEN*_….

wani lazy smiling ya aiketa dashi yanabin bayanta databi shaikh cikin gida da sauri.

 

*_ZUCIYA MUGUN NAMA_*……

Cikin qanqanin lokaci layin ya ‘dan cika da malamai da ‘dalibai tareda masu zuwa ‘daukar karatu aka shaida ‘daurin auren _NURADEEN DA AYSHAH_…Akan sadaki naira dubu hamsin Wanda shaikh ne yabiya sbd qaunar NURADEEN da Allah yasaka Masa aransa tun ranar daya fara zuwa gurinsa..

Tunda babban ‘dan shaikh yashigo ya sanarda an ‘daura auren taji hankalinta ya tsananta tashi wani sabon kuka yazo Mata ta sake cusa kanta cikin qafafunta tana yi.

Uwar gidan shaikh ‘dince ta ringa rarrashinta tana jero Mata nasihu akan tabbas Bata kyautawa iyayentaba Amma tunda jahadine tayi Allah bazai Bari ta wulaqantaba insha allah…Dan ba’asan iya Wanda zai musulunta ba sanadiyar auren.

Awa ‘daya da gama ‘daurin auren shaikh ya Aiko kiranta tashiga pilonsa da sallama a qasan maqoshi sbd muryarta data shaqe sbd kuka..

Nasiha yayi Mata sosai Mai matuqar shiga jiki kafin yace taje Deen na waje yana jiranta zai maidata gida.

Tana fitowa idanuwansu suka ha’du Nan take taji jikinta yakuma sanyi gefe ‘daya wahalalliyar soyayarsa na ‘dawainiya da ita.

Shikuwa ji yake tabbas Babu abinda yakai musulunci da’di tunda ya mallaka Masa ayeeshansa.

Ya zagayo Yana rintse ido sbd mugun zazza6i da rawar sanyi da jikinsa keyi…
Bu’de Mata motar yayi tashiga asanyaye kafin shima yashiga suka bar gurin…

Ko anguwar Basu fitaba yaji jikinsa na neman rikicewa ya ‘dan saci kallon gefenta yaga kanta a sunkuye ya tattaro ‘dan kuzarinsa Dan yasamu yakaita gida kafin ciwon ya kwantardashi..

Dashi dishi yafara gani saura qiris yadaki wata babbar mota yayi saurin take burki….

‘dagowa tayi a ‘dan tsorace saitaga jikinsa na rawa sosai idanuwansa sunyi jajir jijiyoyin kansa duk sun yanko…

A rikice takira sunansa hawaye na gangaro Mata…

Kallonta yayi kaman zaiyi kuka yace,

Ayeeshah my head….I can’t see properly…

Shaking yake sosai ta juyo takalli waje taga hadarine sosai a garin Dan kowa Sai hanxarin guduwa gida yakeyi..

Maido kallonta kansa tayi taga yayi mugun laushi ta ‘daga hannunta ahankali Yana rawa ta dafa goshinsa taji zafi sosai cikin hawaye tace,

Deen let’s go back to shaikh house..

Daqyar ya iya ‘dagowa yace,

My love I can’t drive that far..

Idonsa ne ya sauka kan wani qatoton babban hotel and suites dake bakin babban titin dasuke..

Juyarda kan motar yayi daqyar daidai lokacinda ruwan sama masu qarfi suka 6arke..

Tunda yashiga yayi parking yafita jikinta ya’dau rawa sabbin hawaye suka 6alle mata harya dawo kaman zai zube sbd jiri ga ruwa na sake dukansa ganin Yana tsaye ruwa na dukansa ta kasa yi Masa musu ta fito suka shige tareda shigewa lift zuwa floor ‘din sama gaba ‘daya.

Suna shiga ko Kaya ban iya cirewaba ya zube a doguwar sofa jikinsa na tsananta shaking a wahalce yace,

Ayeeshah please cover me.

 

 

Mamuh????
*_MAMUH GEEE_*

 

_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

*21*

Tsayawa Finn yayi akansu Yana kallonsu cikin wulaqanci ganin har lokacin da sauransu ya juyo ya kalli tiger yayi Masa alama da ido…

Kallon yaransa tiger yayi Sai aka Kuma ‘debo ruwan qanqanra a qaton bucket aka Kuma jiqasu tareda cigaba da dukansu..

Iya dakuwa Kam sun daku bama kamarsu Yaya abbakar dasuke samari anfi dukansu duk da dai Suma su baban ba a raga musu ba…

Sake kallonsu Finn yayi yaga sun bugu yasaki murmushin qeta tareda fiddo wayarsa ya ‘daukesu yaturawa mum kafin yakirata yace ta duba..

Dariyar Jin da’di tayi lokacinda taga hoton takira tace a kaisu inda aka ‘daukosu a watsar..

 

Zamewa tayi daga rumfar dayayi Mata takoma bakin gado ta zauna kanta a qasa tana kallon dogayen fingers dinta..

Dawowa yayi kusada ita ya zauna shima ya qurawa hannun nata ido..

Ayshah please lets get married before informing our families about us…

‘dagowa tayi ahankali takallesa ta kawar da idonta kafin ahankali tace,

No Nik…I can’t marry you without my family’s approval.. besides that I’m Muslim you’re Chris…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button