HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Katseta yayi da cewa,

I’m ready to convert my love….I want to become Muslim too…

Kallonsa tayi idonta na cikowa da hawaye sabuwar soyayyarsa na qara shigarta sbd ganin yanda idonsa ya rufe bayako tuna masifar dake gabansu ta dukkanin 6angaren biyu…Dan tasan gidansu sun gwammace ta mutu dasu barta dashi..

I love you ayeeshah…

Juyarda Kai tayi tareda sakin 6oyayyen murmushi..

Fira yafara yi mata ahankali Yana Bata lbarinsa saidai tayi murmushi kawai batareda tayi maganaba.

Mantawa suka da komai da kowa Saida sukaji knocking tayi saurin miqewa tsaye gabanta na fa’duwa jikinta na rawa..

Kallonta yayi tareda sakin qaramin murmushin daya bayyana white teeths ‘dinsa qasa qasa yace,

Wait hia…

Qofar ya 6ude ahankali saiyaga nurse ce yasaki ajiyar zuciya ahankali tareda juyowa ya kalli yanda ayshan tayi zuru duk saiyaji tabasa tausayi ya matso kusada ita yakai bakinsa saitin kunnenta zaiyi magana tayi saurin zillewa ta Fice ‘dakin da sauri tana Jin farin ciki na shigarta tako ina.

Shafa kansa yayi tareda kwantawa a gado Yana Jin farin ciki Mara misaltuwa.

Tundaga nesa ta hango qofar gidansu da kamar mutane gabanta yayi fa’duwa ta qarasa a darare..

Su Yaya sani dasu babanta ne ke qoqarin shigardasu baba alhaji cikin gida dukkaninsu ba kyan gani kawunansu da fuskokinsu a kumbure da jini a kayansu..

Yawu ta ha’diye daqyar tashigo gidan Nan ta tararda kowa hankalinsa a tashe su husna ma harda kuka ganin mummunar aika aikar da akayiwa su baban.

Sosai itama hankalinta ya tashi Dan koba’a fa’daba tasan wannan aikin mum ne..

Har dare gidan ba da’di Dan kowa na cikin jimami da baqin ciki..itadai Bata kosanyin wani qwaqwaran motsi sbd tsoron Mai zai biyo baya.

Har akai kwana biyu ba’ai zancen komaiba kan al’amarin Kuma tun ranar Bata fitaba sbd tsoro da fargabar abinda zai biyo baya duk da ba qaramin tausar zuciyarta takeyiba akan son sanin ya jikinsa yakeba..

Yau kwana hudu da afkuwar tsautsayin su baba..
Matuqar zafi gidan kusan kowa ya ‘dauka musamman matasan gidan wannan karon ko baba malam ya ‘dau zafi matuqa….
Shiyasa ya tarasu yau kowada kowa..

Gyara Zama yayi tareda kallon ayshah murya a karsashe yace,

Ayshah Kinga abinda wa’innan mutanen sukayi Mana ko?

Shiru tayi gabanta na bubbugawa da sauri..

Cigaba yayi da cewa,

Duk bazanyi wani tashin zanceba ko dogon zance auren Umar da ayshah nasaka Nanda wata biyu kowa yaje yafara shiryawa Kuma nijar zasu koma bayan auren nagama magana kowa zai iya tafiya.

Takaici ne ya turniqe Yaya Umar Dan so yayi ace Nanda sati ‘daya a ‘daura auren..

Iyayensu da sauran ‘yan gidan kaf sunyi na’am da hukuncin baba malam ‘din Dan tsoron abinda zai iya biyowa baya.

Ayshah kuwa jitayi hankalinta yayi mummunan tashi hawaye yaciko idanuwanta jikinta har rawa yake ta miqe ko gani batayi sosai tabar palon.

Kuka take sosai cikin qaramin sauti zuciyarta na tsananta shiga qunci..
Kamar munafuka takoma cikin gidan ko fitowa Bata cikayiba..hakama zuciyarta a matse take dason ganinsa.

Zaune take akan carpet ‘din sallah kaman kullum tayi shiru idanuwanta a lumshe..

Zama kusada ita taji anyi ta bu’de idanuwanta ahankali ta sauke kan nuratu…

Qasa qasa da murya nuratu tace,
Anty ayshah jiya Da ina dawowa daga makaranta nagansa acikin anguwar Nan..yauma Dana dawo nagansa.

Qurawa nuratu jajayen idanuwanta tayi gabanta na duka da qarfi….

Muryarta na rawa tace,

Kinfa’dawa wani kingansa?

Girgixa Kai tayi tana kallon ayshahn tace,

Anty ayshah kina sonsane?

Hawayen dasuka gangaro Mata ta goge da bayan hannu tace,

Ina sonsa nuratu..

Dafata nuratun tayi cikin danne mamakin da tausayawa tace,

Anty ayshah karki Bari zuciya da shai’dan suyi galaba akan tarbiyar da iyayenmu sukai shekaru suna bamu.

Cusa kanta tayi tsakiyar qafafunta ta bawa hawayen datake dannewa Daman kwarara..

Washe gari shiryawa tayi a sanyaye Dan batada tabbacin za’a barta cigaba da karatun duk da tuni ya fara wargajewa.

Cikin ikon Allah ba’a hanata tafiyaba saidai tana fitowa titin anguwarsu taga motarsa ajiye gefen titi nanta ha’diye wani yawun tashin hankali Dan tabaro su Yaya Umar dasu ya Ahmad qofar gida suna Shirin fitowa…

Tabbas idan haryana cikin anguwar akwai yiyuwar su gansa Kuma tasan wannan karon bazasui Masa Mai kyauba.

Juyawa tayi da sauri taking cikin layin saigasu sukuma sun fito layin tayi saurin shigewa soron wani qaramin gida..

Jitayi hayaniya ta kaure da sauri ta leqo saita hangosa tafe izuwa gurinsu batareda ya ankare dasuba.

Ya sani yafara ganinsa ya zabura tareda nunawasu Umar shi…

Qatuwar spanner dake hannun ya abbakar dazai gyara mashin ‘dinsa ya saitashi ya jefa Masa Sai a goshinsa ba zato yaji saukar qarfe Nan take goshinsa ya fashe ya ‘dago lazy eyes ‘dinsa dasukai jan azaba yakallesu duk da yaji tsoron ganinsu bayajin zai iya guduwa ko tafiya batareda yau ya gano gidansuba.

Tsayawa yayi jini na fita a goshinsa ya kalli sani daya shaqo kwalar rigarsa Yana huci.

Azafafe yace,

Uban me kakeyi anan?

Kallo yabisa dashi sbd baisan meyake fa’daba..

Mari Umar ya wanka Masa akan kyakkyawar fuskarsa dayakejin kamar ya zuba Mata batir..
Yace,

He said wat are you doing hia you monkey fool.

Kallon Umar ‘din yayi akaro na farko dashima yaji tsanar wani ‘dan Adam Kai tsaye yace,

I came hia to see my love.

Ture sani Umar yayi da qarfi ya shaqo wuyan Nik ‘din yace,

Wh…wh..who is your love?

Ayeeshah””””ya fa’da Kai tsaye ba tsoro a idanuwansa.

Hannu ya dunqule yakaiwa Nik wani mugun duka Saida bakinsa ya fashe.

Wani dattijo ayshah tagani zai wuce tayi saurin Shan gabansa tana hawaye tace,

Baba Dan Allah kaga wasu can suna fa’da Dan Allah ka hanasu karka Bari ayi fitina.

Juyawa yayi ya kalli gurin daidai sun nanna’de rigunansu zasu cire takaicin dukan daakayiwa iyayensu dattijon yayi saurin tarewa tareda matsarda Nik dake tsaye baida alamar motsawa gefe yace,

Haba Kuna ‘yayan musulmai ‘yayan manyan malamai zakuyi Abu irin na jahilai…
Meyayi zafi haka dabazaku Kira hukuma ba Zaku ‘dauki mataki da hannunku…

Fa’da yahau yi musu sosai suka basa hkr tareda barin gurin sbd duk zafin ransu sunada tarbiyar girmama babba sosai Koda basusanshiba.

Juyowa yayi ya kalli Nik yace,

Kaima ka wuce tunda Suma sun tafi..

Juyawa yayi ahankali yabi bayansu duk da baisan abinda mutumin yafadaba…shidai yau alqawarine yayiwa zuciyarsa saiyaganta Dan haka zaibi bayansu saiyaga gidansu..

Daf dazai shiga kwanar yaji anriqo rigarsa ta baya yayi saurin juyowa sukai Ido biyu ta juya yabiyota da sauri Yana Kiran sunanta Amma taqi tsayawa.

Saida takai bakin motarsa ta tsaya tareda juyowa ta kallesa taga yanda goshinsa da bakinsa ke jini ta ‘dauke Kai tareda ‘daure fuska ta nuna Masa motarsa tace,

Leave…

Da sauri ya kalleta zaiyi magana tace,

Go… please..

Idanuwansa ne suka ciko da hawaye ya kalleta kaman zaiyi kuka yace,

Ayeeshah please don’t ask me to leave because I can’t….

Rintse ido tayi cikin ra’dadin ganin jininsa na zuba ta sake juyar dakai tace,

Please Nik go…
I don’t want to lie to myself again..
I don’t want to continue believing in a fake dream…
My parents fixed date for my marriage with someone…..

Wani mugun jiri ya ‘dibesa dama jurewa kawai yake Dan tuni yakejin jirin jinin dayake fita a goshinsa…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button