TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Nik ‘dan gayune na qarshe daya ha’du iya ha’duwa sbd tun farko a hannun dad ‘dinsu yake a qasar Germany danshi Sam bayason takura yanason yayi rayuwarsa a sake shiyasa yaqi biyo mum ‘din dazata dawo Sai daga baya ta matsa tareda ‘daga hankalinta akan saiya dawo Nigeria.
Gabaki ‘dayansu suma farare ne tas bama kamarshi dayafisu son hutawa akoda yaushe kamar mace.
Davina ma kusan kamarsa take ‘yar gayu kullum Tana tareda friends ana gurin shopping ko gurin hutawa..
Hutu da gata tareda dukiya sun ratsasu sosai shiyasa kullum cikin qara kyau Nik yake,
Duk wani son life ‘dinsa mata basa burgesa tunda yadawo Nigeria sbd Sam bazai iya ko kallonsu ba bare ya iya kulasu yan matansa nacan sunfi burgesa sbd sune sukafi sakasa nisha’di.
Tsaf take cikin kayanta na aiki ta fito ta hawo sama bedroom ‘dinsa Dan shika’dai ne ‘dakinsa yake sama sbd tsananin so data fili ta nuna qarara tafisonsa fiyeda sauran ‘yayan nata.
Tura qofar tayi ahankali sanyin ac da qamshin turarensa na signature hugo ya daki hancin takai kallonta kan lafiyayyan gadon dayake kwance Yana bacci dunqule cikin falin bargo qal.
Takowa tayi ta Isa bakin gadon tareda durqusawa ta rintse ido tafara kwararo masa adduarsu ta church Wanda kullum saitayi Masa kafin tafita office hakama da daddare komai Daren dazaiyi awaje saita jira yadawo tayimasa sbd ba qaramin so takeyiwa ‘dan nataba.
Ahankali ya ‘daga hannunsa ‘daya ya janyo dayan pilonsa batareda ya bu’de idanuba ya toshe kunnensa dashi sbd damun baccinsa da mum din keyi da addua.
Jin ta qara ‘daga murya tana fa’din,
Ohhhh Lord I pray for……….Jesu….
Cikin muryar bacci Yana qara tora kansa cikin pillow yace,
Mum pls I hate this…
Miqewa tayi bayan tagama tareda ‘duqawa ta shafi fuskarsa bayan ta janye pillon cikeda kulawa tace,
Nik can pls promise me you’ll……
Katseta yayi cikin qosawa yace,
Yes I promise I will.
Thank you sweetheart”” tace tareda miqewa tafice tana murmushi.
‘dakin Davina tanufa Kai tsaye daganan.
Kwance take tana bacci itama Amma ki’da ke tashi a hankali cikin ‘dakin sbd ita Bata iya bacci Saida kida qaidarta ne.
Tada ita tayi itama kafin tafito ta tsaya Saida masu aiki suka jera komai na breakfast ‘dinsu Nik idan sun tashi kafin takalli Finn dake shirye Yana jiranta suka wuce office.
WANNNAN KENAN.
Mamuh????
_Dont forget to follow,vote and comments_ _@mamuhgee_..
*_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida_….
_viawattpad@mamuhgee_
*2*
Yauma a sanyaye ta iso makarantar sbd duk jinta take a takure badan tana tsananin son karatunba da batajin zata iya cigaba da zuwa sbd wannan new site ‘din yafi qarfin abinda qwaqwalwarta zata iya ‘dauka.
Lectures biyu tayi yau Dan haka da wuri tagama Tana fitowa hall ta fiddo niqaf ‘dinta ta rufe kyakkyawar fuskarta sbd kallo dayayi mata yawa Wanda tasan bai wuce na suturartaba sbd har ja hijabinta keyi.
Sauri takeyi ta tafi gida duk da niqaf ‘din data saka kanta a qasa yake bazaka ta6a cewa sauri takeyiba sbd cikin nutsuwa take tafiyar kaman yanda addini ya koyar.
Tsayawa tayi cak tareda juyowa ahankali sbd sunanta dataji ankira daga bayanta.
Ajiyar zuciya tasaki sbd ganin wata ayshar ce ake Kira ba itaba.
Juyawa tayi zata wuce batareda sanin isowa mutumba sukai wani irin karon dayasa wayar hannunsa da car keys ‘dinsa zubewa qasa.
Ya salam” tafada ahankali cikin sauri tareda ja da baya jikinta na matuqar rawa sbd jikinsu daya ‘dan ha’du Wanda wannan shine karo na farko da jikinta ya ta6a ha’duwa da jikin wani ‘da namiji.
Tsayawa kallonta yayi sbd ganin yanda jikinta ke tsananin rawa abin dayafi basa takaici ma kenan,
Samanta zawa qasanta ya kalla cikin qyanqyamin shigarta sannan shibaiji baqin cikin ha’duwar jikinsuba shida yakeda komai na rayuwa musamman kyawunsa dake fuzgar mata Sai itace da fuskarta ke rufe qilama nakasasshiyace shiyasa ta rufe fuskar.
Dafasa abokinsa Murphy yayi bayan ya ‘dauko Masa kayansa dasuka zube Yana cewa,
Let’s go Nik we’re getting more late..
Wucewa yayi tareda qara juyowa ya kalleta yana 6ata fuska.
Hawayen datake dannewa ne suka gangaro mata ta ‘dago Kai ahankali takalli inda sukabi dai dai yakuma juyowa manyan idanuwansu suka ha’du da juna.
Atare gabansu ya Fadi yayi saurin ‘dauke Kai sbd tsoro da idanuwanta suka bashi danshi mutum ne Mai tsoron mutane sbd bai cikason ko kallon wasu mutanen ba.
Ita ma cikeda tsoro ta juya jikinta na tsananta rawa ta fice tabar makarantar.
Harta Isa gida nutsuwarta bata gama daidaita.
A qofar farko ta ha’du da ya Umar gabanta yakuma yankewa ya Fadi sbd ganin Yana qureta da kallo tai saurin tattaro nutsuwa tareda qaqalo murmushi cikin sanyin murya tace,
Ya Umar ina yini?
Cikin Jin da’di da tsananin qaunarta ya amsa tareda cewa,
Ayshah da gani kin ‘debo gajiya ko?
Eh”’tace tana sauke Kai qasa.
Bata hanya yayi ta wuce batareda yakuma wat maganarba.
A ‘dakin umminta ta yada zango ta cire hijab ‘dinta tareda sakin ajiyar zuciya ahankali.
Washe gari jiki a sanyaye ta shirya ta nufi makarantar duk da yau ya Umar da kansa ya rakota har bus stop tashiga mota.
Tunda suka shiga first lecture ‘dinsu taga tamuqar ba tattaro nutsuwa tayiba to bazata fahimci komaiba shiyasa ta ‘dan nutsu ta karanto addua tareda maida hankali saigashi tana fahimtar komai.
Sai four suka fito a gajiye take sosai ga yunwa datakeji sbd Sam basa cin abinci a waje komai rintsi shiyasa ko ruwan makarantar Bata ta6a siya tashaba.
Sam bazaka kalleta kace yunwa takejiba sbd acikin nutsuwarta take tafiya.
Saukowa take daga sama Dan hall din dasukai lectures yau a sama yake.
Wasu samari ta hango qasa a tsaye suna sheqa dariya suna nunota
Tasan da ita suke Dan idan da sabo yakamata ace tasaba da tsokanarsu Dan kullum idan zata fita Sai sun tsokaneta suna kiranta da ninja lady Wanda sunan tuni yafara binda acikin makarantar Dan gabaki ‘daya yanxu ba Wanda yasan fuskarta sbd kullum rufe fuskarta take cikin niqaf,,
Ba kalar mummunar halittar daba’a kiranta da ita sbd kawai ta cire niqaf ‘din aga fuskarta Amma Sam ta danne duk da sau tari idan an mata tana Jin zafi harda hawaye musamman idan matane sukai mata.
Ihu suka ‘dauka suna Kiran,
Here comes our ninja lady..hahhhhhhh
Sunkuyar da Kai tayi tacigaba da saukowarta sbd Bata ta6a kulasuba.
‘daya daga cikinsu mace taci ado ta matse cikin qananun Kaya kamarba musulma ba ta ‘daga musu hannu tareda miqewa tsaye cikin ‘daga murya tace,
Yau dai Kam dole muga fuskar ninja lady sbd bamusaniba Koda aljana muke tare,,wat do you say guys????
Ihu suka ‘dauka cikin shewa suna cewa,,
Yesss ohhhh..
Cak ta tsaya gabanta na tsananta fa’duwa ganin yarinyar ta nufota ana mata kirari gurin na da’da ‘daukar ihu sbd kowa dakeson ganin fuskarta ta.
Ayshah mutumce Mai tsananin tsoro da rashin qwarin zuciya sbd Sam batada kuzarin dazata iya qwatar kanta Sai kawai tafara hawaye ahankali tareda rintse idonta tadan ja baya daidai lokacinda yarinyar takai hannu zata bu’de mata niqaf taja baya ka’dan cikin rashin sa’a Ashe takai bakin qarfen stairs ‘din ta fa’da.
A tsorace kowa gurin ya ‘dau ihu..
Sanye yake cikin wasu tsadaddun designers qananun Kaya blue jins da blue shirt datayiwa farar fatarsa kyau bazaka kallesa kallo ‘daya kace christian ne ba sbd yamafi Kama da akirasa bafulatani sbd komai nasa Mai kyawu ne.,