HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Cikin mintuna qalilan ta suka iso hankali tashe
Suna ganin halinda yake ciki mum tace ayi musu Shirin komai subar qasar zuwa gobe.

 

Duk inda hankalinta yake yayi mummunan tashi sbd har dare bashi ba shaikh…

Koda gari ya waye ko gani batayi sbd kuka gashi da ko Zama Bata iya yi sbd ciwo gashi Sai shirye shiryen ‘daurin aure ake bayan sallar juma’a..

Su anty amina ne suka shigo ‘dakin tareda kamota ta tashi suka kaita har cikin toilet daqyar ta iya ‘daga bucket ‘din tajuyewa jikinta har cikin Kai tafito suka miqa Mata Kaya ta zura aka fito da ita sbd Mai qunshi da’aka Kira.

Tana fitowa tsakar gidan wani mummunan jiri ya ‘dibeta sbd rashin qarfin jiki da zafin zuciyar daya yunquro Mata Nan take ta zube gurin asume…

Agigice sukayi kanta suna Kiran sunanta Amma ba alamar numfashi atareda ita.

Da sauri aka zuba Mata ruwa amma ba alamar zata motsa ba Nan hankali ya Kuma tashi su baba alhaji da ya Umar da mama sakina aka kwasheta Sai asibiti.

Cikin gaggawa aka kar6eta akai cikin emergency da ita.

Zama su mama sakina sukayi jiran tsammani har kusan awa ‘daya saiga Dr yafito ya nufi office ‘dinsa su baba da ya Umar suka bisa.

Zama yayi Yana warware tie ‘dinsa ya kafin ya kalli su baba dake raba idanun jiran bayani.

Alhaji maganar gaskiya yarinyar Nan tana fama da damuwa tareda yunwa Kuma hakan babban barazanace ga lafiyarta da abinda ke cikinta,,,,ma’ana juna biyun dake cikinta na wata ‘daya da kwanaki….

*_MAMUH GEEE_*

 

_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida…._

_Viawattpad@mamuhgee_

 

*27*

*_godiya Mai tarin yawa ga masoyan TAURA BIYU aduk inda suke.._*????

 

Babbar Riga baba alhaji ya gyara Yana qara gyara Zama sbd shi Sam bai fahimci zancenba ya kalli Dr yace,

Aa wannan dakake magana ba itace Wadda muka kawoba,,
Wadda muka kawo itama tanan cikin ‘dakin sunanta ayshah Kuma budurwace Bata ta6a aure ba…yauma ne dai za’a ‘daura auren nata kaga mijin Nan a tsaye.

Takaici ne ya ‘dan Kama Dr Amma fahimtar dayayi da Rashin sanin komai dasukayi akan ‘yarsu saiya gyara Zama Dan sake musu bayani dalla dalla..

Alhaji maganar danake fa’da muku anan bayanine akan ‘yarku da kuka kawo..’yarku ayshah tana ‘dauke da ciki na haihuwa ‘dan wata ‘daya da satittika…

Sharce zufa baba alhaji yayi ya juyo ya kalli baba qarami dashima tuni babbar rigarsa ta Shirin ‘daurin aure ta jiqe sbd zufa…

Atare suka juyo suna aikawa Umar da zuciya tagama kashesa Banda mazari ba abinda jikinsa keyi idanuwansa kuwa ko gani sosai bayayi dasu sbd baqin ciki da tafasar zuciya…

Juyawa yayi a fusace zai fita baba qarami yayi saurin Shan gabansa tareda sharara Masa lafiyayyan Mari…

Ji yayi kansa na neman bugawa ya ‘dago da jajayen idanuwansa yakalli su baban yaga irin kallon dasuke Masa ya daki bango da qarfi kamar zautacce yace,

Karma kufara wannan tunanin,, tunda nake a rayuwata ko hannun ayshah banta6a riqewa bare har ni nayi Mata…..

To idan bakai bane wane?””””” Baba alhaji yafada da qarfi cikin zafin zuciya da 6acin Rai.

Jiki sanyaye baba qarami ya kalli baba alhaji yace,

Muje gida mayi komai acan gaban malam babba.

Fitowa sukayi kowanne daqyar babbar rigarsa ke ‘daukarsa sbd kunya da baqin ciki..

Kallonsu mama sakina tayi cikeda damuwa tace,

Lpia kuwa?
Meke damunta likitan yace?

Fuskarsa na kallon wani gurin yace,

Ayshah cikine da ita Dan haka kitashi maza yanzu muje gida ayi komai can gaban kowa.

Yawu ta ha’diye daqyar jikinta itama Yana ‘daukar rawa sbd gabaki ‘daya ta nemi nutsuwarta ta rasa dajin wannan mummunan zance daga bakin baba alhaji.

‘dakin tashiga ta tararda ayshan ta tashi saurin ‘dauke Kai tayi cikin tashin hankalinta daya kasa 6oyuwa tace,

Taso maza gida zamu yanxu..

Ba musu ta sauko gadon ahankali jikinta na tsananta sanyi hakama fa’duwar gabanta na tsananta..

Koda suka fito su baba harsun samu mota sun shiga suna fitowa Umar yabar gurin yaje yahau mashin Dan bayajin zai iya shaqar numfashinda jinin Deen dake cikin ayshah yake shaqa.

Tunda suka shiga motar Babu Mai ko qwaqwaran motsi sbd kowada tunanin dayake ransa.

Umar ya rigasu isowa shiyasa koda suka iso ya Tara kowa a palon ana jiran isowarsu Dan ko magana baya iyayi bare yafa’di abinda yake faruwa..

Suna shigowa palon kowa yabisu da idanuwa sbd fargabar Jin koma menene Dan tun a yanayin Umar ‘din suka tabbatarda koma meyene bamai da’di bane.

 

Gyara Zama malam babba yayi ya fuskanci baba qarami yace,

Shehu lafiya dai Naga fuskokinku ba da’din kallo..

Gumi na qara yanko Masa yace,

Ba lafiya ba…

Wani ‘daci malam babban ya ha’diye tareda maida kallonsa ga baba alhaji dashima har lokacin zufa yake yace,

Bello yimin bayanin komai yanxu Ina sauraronka.

Yaya muna cikin gagarumin tashin hankali sbd mutunci da sunan wannan gidan ya gama lalacewa daga yau…
Ayshah gatanan zaune cikine da ita na haihuwa ma’ana dai cikin banxa..

Ba kowa daya ki’dima dajin zancenba ita kanta zabura tayi cikin masifaffen tashin hankali umminta dake kusada ita ta mayarda ita zaune tareda rufe Ido ta saukar Mata da kyakkyawan mari tareda fashewa da kuka numfashinta na qoqarin ‘daukewa da sauri nuratu da salma sukayo kanta duk da dukkaninsu jikinsu rawa yake sbd tashin hankalin dasuke ciki.

Malam babba kuwa qoqarin fita hayyacinsa yake sbd hawan jininsa daya Haye gabaki ‘daya Nan take zufa ta jiqasa yafara gani dishi dishi..

Hankali tashe su baba qarami dasu abbakar sukayi kansa ana Masa firfita hankali a matuqar tashe..

Rarrafowa tayi da sauri gaban malam babba ‘din tana kuka sosai zatayi magana babanta da zuciya tagama kashesa ya rufeta da duka tako ina Nan hankali ya Kuma tashi sbd ganin baban nata ya zube qasa Yana kuka sosai…

Ba qaramin duka baban yayi Mata ba Amma haka ta miqe baki na jini ta qara rarrafowa gaban malam babba cikin tsananin kuka tace,

Wallahi baba banyi watsi da tarbiyar da kuka bani ba wannan al’amarin qaddarace daga Allah wlh baba na yarda danayi babban kuskuren barin soyayya ta rufemin Ido nayi aure batareda saninku ba….

Shaqota Umar yayi ahasale yace,

Da wa Kika ‘daura auren?

Cikin tsananin kuka tace,

Niklaus..

Wurgi yayi da ita da qarfi cikin 6acin saida kanta ya daki dutsin da aka tare qofa dashi Nan take goshinta ya fashe duk da haka Bata tsayaba saima kukanta daya tsananta ta rarrafa taqara zuwa gaban malam babba da har lokacin numfashinsa bai daidaita ba ta riqo qafafunsa cikin tsananin kukan dayake jijjiga jikinta tace,

Baba wlh da gaske nake ban aikata zinaba na samu wannan ciki wlh aure…..

Hannu ya ‘daga ba zato kowa yaji kukan Marin daya sakar Mata.

Tsit sukayi cikin mamaki da tsoro sbd malam babba bai ta6a ‘daga hannunsa akan kowaba Sai yau.

Miqewa yayi su abbakar na riqe dashi numfashinsa na sama sama ya rintse Ido cikin kakkausar murya da bai ta6a magana da itaba yace,

Daga yau nacire ayshah daga cikin zuri’ata,,,

Daga yau ayshah Bata cikin zuri’ar gidan Nan,,,

Daga yau na Kori ayshah daga cikin gidan Nan har abada bana buqatar sake ganin fuskarta,,,

Daga yau ko sunan ayshah karna kumajin wani ya furta acikin gidan Nan,,,
Kuma ban yafe ta ra6i ko ‘daya daga cikin zuri’ar gidan Nan ba haka Kuma ban yafe taje gida nijar ba da wannan mummunan abin kunyar…..

Cikeda tsoro da fargaba baba qarami ya matso zaiyiwa malam magana akan Kar akoreta ayimata duk wani hukuncin cikin gida…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button