TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Malam ya ‘daga Masa hannu idanuwansa na qarasa rufewa Nan hankalinsu Yakuma tashi…
Kasa motsawa tayi sbd babban tashin hankalin dataji…
Cikin zafi da ‘daga murya babanta yace,
Umar fitar Mana da ita daga gidannan Kuma koni duk ranar data Kuma waiwayar gidannan ban yafe haihuwar danayi mataba…
Hannu ta ‘dora akai tareda fashewa da wani sabon kukan tashin hankali ta rarrafo gurinsa da sauri tana want irin kuka hartana shaqewa ya janye qafafuwansa tareda barin palon jininsa na hayewa danshima daqyar yake gani.
Gurin baba alhaji ta rarrfa tana kuka Mai ban tausayi da tsananin nadama shima yabar palon ta koma gurin baba qarami kukanta ya ta6a zuciyarsa matuqa sbd kukan datake ya wuce tunani dan komai na jikinta rawa yake…
Cikin tsananin tsawa baba yace,
Ka fitar da ita Umar…
Matsowa yayi jikinsa a sanyaye idanuwansa jajir Dan tun ‘dazu shima kukan yake kamar ransa zai fita sbd yasan ya rasa ayshah kenan tabbas daya sani tun farko zaice cikin nasane kodan ya sameta.
Idanuwansa a rufe yake janta,
Kuka take tana kiran sunayen su baba tana bayyana tubarta da Basu hakuri amma Saida Umar yakaita waje ya kalli cikinta wani baqin ciki ya taso Masa ya jefata da qarfi kan qaton dutsen dake qofar gidan cikinta yayi mummunan buguwa Nan ta dafe ciki cikin wata mummunar azaba sabbin hawaye na bin fuskarta…
Jitayi wani sanyi nabin cinyoyinta tasa hannu ta shafo saitaga jini…
Rintse ido tayi cikin tsananin azaba da kuka ta miqe da qyar goshinta da bakinta na jini ga Wanda yake bin qafafunta ta tsaya ta kalli gidan sabon kuka na zuwar Mata ta juya jiri na ‘dibarta tayi titi.
Napep ta tsayar ko gani sosai Bata iyayi sbd jini daya daketa ga kukan datasha kamar na hauka Kuma har lokacin Bata daina kukanba.
Qofar gidansu Deen aka ajeta ta fito a dudduqe ta nufi gate maigadi na ganinta ya bu’de Mata sbd tun wancan zuwan datayi Deen yayi Masa kashedin datazo ya bu’de Mata kofa.
Aharabar gidan ta tarardasu mum sun rufe ko’ina zasu shiga mota Sai ganinta sukayi.
Tana zuwa gaban mum ta zube tana wani irin kuka Mai tsima Rai Dan nantake ya ta6a zuciyar Davina Da tsananin qaunar datakewa ‘dan uwanta tasa tafara qaunar ayshah ‘din.
Bu’de mota mum tayi zata shige tayi saurin riqe qafarta cikin tsananin kuka tace,
Mum pls I need to see him..I want to talk to him,,,I was thrown out of my house,my family,,,,
I have no one now,,,he is my only hope now….
Fusge qafarta tayi tareda damqarta tafara janta cikin masifa takai wajen gate ta watsar tareda nunata da yatsa cikin tsananin baqin ciki tace,
I’ve never hated something or someone so badly the way I hate you,,,
I hate you to the last core that I can strangle you to death…
My son Nik will never see you or be with you again because he’s already in somewhere else,,,
You’ll never set your eyes on him for the rest of your miserable existence…
So go, leave,stay out of our lives….
Cikin karaya da tashin hankalin Jin zancen mum ‘din hawaye nabin fuskarta tace,
Mum please don’t do this to me,,,if not for me please let me see him for sake of his unborn child…..
Cikin tashin hankali dukkaninsu suka zaro idanuwa musamman ma Davina da wani irin da’din zancen ya kasheta kafin tayi magana mum ta tura ayshan baya da qarfi ta fa’di kife Nan tasaki qara tareda dafe cikin Nan sauran jinin daya tsaya ya qara 6alle Mata ta kalli qafafuwanta da sauri taga yanda jinin ke gudu kafin tayi want motsi ruwan sama suka 6alle mum takalli su Davina ta nuna musu mota da Ido kafin ta bu’de jaka ta Ciro bundle ‘din one one thousand ta jefawa ayshah ta fa’da mota sukabar gidan aguje Sai airport suna Isa ko minti ashirin basuyiba jirginsu ya tashi sukayi bankwana da Nigeria..
Qurawa jinin cikinta dake bin ruwan sama Yana gudu tayi zuciyarta na Mata wani irin nauyi,,,,
Jinin tacigaba da kallo har ruwa yagama wankesa yatafi dashi ta rintse ido tareda sakin wani ihu tareda kuka…
Har aka gama ruwan saman tana duqe gurin tana kuka irin Wanda Bata ta6a yinsa arayuwaba.
Rarrafawa tayi qoafar gidan ta ra6e jikin gate tana rawar sanyi da wani zazzafan zazza6i har haqoranta na ha’duwa.
Da safe Mai gadi na fitowa yaganta kwance a gurin kamar batada Rai yayi saurin komawa ciki ya ‘debo ruwa ya antaya Mata tasaki ajiyar zuciya ahankali tareda bu’de Ido daqyar.
Durqusawa yayi gabanta cikin tausayi yace,
Kiyi hkr ki koma gida ko kitafi wani guri Dan maganar gaskiya itace Nik yatafi,anvar qasar dashi Kuma bazai ta6a dawowaba.
Kamar wawiya take kallonsa zuciyarta na wata irin tafasa tabbas tayi ganganci tareda babban kuskuren barin soyayya ta rufe Mata ido tayi aure bada sanin iyayenta ba gashi yanxu yasamu abinda yake so ya gudu ya barta da ciki gashi gidansu ankoreta….
Wani mummunan nauyi taji zuciyarta tayi Mata idanuwanta sukai wani mugun ja ahankali taji tsanar kowa da qiyayyar kowa na shiga dukkanin ga6obin jikinta ta miqe tsaye tareda durqusawa ta ‘dau ku’din da mum ta jefo Mata cikin wani irin yanayi tace,
Zanbawa kowa mamaki,,,
Gidanmu sun rufe idanu sun koreni batareda bani damar gyara laifina ba ko bani uzuri amatsayina na mace,,,
Sunan dasuke gudun ya lalace har suka koreni saina lalata musu wannan sunan ta yanda ko qofar gida Babu Mai sha’awar fitowa….
Ku’din da mum ta jefo Mata takalla da jajayen idanuwanta tace,
You’ll pay for this queen…
I promise to make all your lives a living hell….
I hate you all..
You’ll all pay for my poor unborn childs blood..
Kuka tasaki tanajin zuciyarta na karyewa ahankali tace,
Meyasa duk zaku gujeni adaidai lokacinda nake tsananin buqatarku,,,meyasa Zaku barni rayuwata ta lalace akan titi….
Wata qatuwar lafiyayyar black Jeep ce tashigo kwanar layin da gudu daga gani matuqin motar ransa a matuqar 6ace yake kafin tayi wani motsin arxiki motar tayi sama da ita ta watsar.
A rikice kyakkyawar budurwar dake tuqin ta fito Mai gadi yakama Mata ita suka saka mota tayi asibiti da ita Dan ita batacika son 6ata lokaciba akomai afterall tanada gurin zuwa..
Cikin qanqanin lokaci akayi gama treatments din komai sbd ba wani ciwo tajiba kawai buguwace a hannu Sai maganin qarin jini Dana masu 6ari daya rubuta musu.
Kallonta fannah tayi cikin yanayin ‘dan tausaya tace,
Ya sunanki?
Ayshah”””””tafada ataqaice sbd lurada datayi da fannan idanuwanta a bu’de suke matuqa duk da tanada ‘dan banxan kyan ‘daukar hankali.
Ayshah Ina ne gidanku nakaiki sbd ni Nan tafiya zanyi zankoma inda nake Dan ni baqunta nazo Kuma yau zankoma.
Banida gida Kuma banida gurin zuwa.,kitafi kibarni anan.
Batayi mamaki ba dantaga alamar korarriyace kamar ita awancen lokaco Dan haka kai tsaye tace,
Korarki akayi daga gida?
‘dagowa tayi ta kalli fannan idonta na qoqarin 6oye hawayenta..
Murmushi Mai ciwo fannah tasaki Dan itama ta ‘dandani irin wannan ciwon na korar iyaye Kuma haryau Tanakan ‘dandanar ciwon..
Kallon ayshan tayi tareda cewa ta tashi sutafi.
Motarta suka shiga suka baro asibitin tana Hawa titi takalli agogo tareda juyowa ta kalli Ayshah tace,
To ayshah ni Zan tafi Zaki bini ne ko kuwa kinada gurin zuwa..
Danne karayar zuciyarta tayi tareda sauke idanuwanta Kar kan titi tace,
Muje ni 6arnar suna nafito yiwa zuriata tareda 6ata rayuwar Deen da zuriarsa.