HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Wata dariyar farin ciki da samun ‘yar uwa fannah tayi tareda bawa motarta wuta suka Kama hanyar barin gari.

 

 

*Nasiha,,,,,,iyaye da abokan zaman rayuwa akoda yaushe yiwa dan Adam uzuri abune Mai mahimmanci sbd rashin bada dama da uzuri shike qarasa ta6ar6arar da alamari qarshe ayi aikin jahilci da Dana sani ta biyo baya Wanda hakan baida kyawu kwata kwata a addini…*
*Iyaye komai girman laifin da ‘yaya zasu yimuku Kar ku kasance masu rufe Ido ku aikata abinda zai dawo ya zame muku abin Dana sani Don kuwa qeya ce.*

*Allah ya tsare yakuma Kare zuri’ar mu gabaki ‘daya*…

_masu cewa wannan yayi, wannan baiyiba wannan yakamata ayi, wannan bai kamata ba kokuma ga abinda sukeso ace anyi to duk wannan bashine ba idan kun nutsu kunbi labarin ahankali to ahankali Zaku fahimci yanda labarin yake dakuma darussa tareda alajabin dayake cikinsa._

*Nagode da qauna*????

 

 

 

Mamuh????

 

_dont forget to follow, vote and comment_

 

 

Mamuh????

 

_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*

 

_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida…._

_Viawattpad@mamuhgee_

*28*

 

_*A zahirin gskia banajin da’din yanda wasu da dama suka dameni da zancen wani bai kamataba ace ayshah tayi karuwanci da aurenta ba,,*_
*_kusani nimafa musulmace Kuma gwargwado inada ilimi da sani akan addina nakumasan me nakeyi Kuma ni nasan abinda nake rubutawa amma ku masu karantawa Sai ku kasa hakuri kuga yanda labarin zai kasance wasuma harda zagi da munanan kalamai to Wanda hakan ba tunani bane Dan haka please and please for god sake idan Kunga abinda bakwa iya karantawa to ku barshi ba dole bare zagi da cin fuska yashigo._*????

 

Tsakar dare suka shiga garin Abuja Kuma zuwa Time ‘din ayshah gaf take da ficewa hayyacinta sbd mugun zazza6i da ciwon marar datakeji.

Sannu fannah ke Mata cikin tausayawa da damuwa tareda tsoron Kar ‘yar mutane ta mutu a hannunta.

Wata ‘yar babbar private hospital dake kusada anguwarsu ta nufa Kai tsaye batareda sun Isa gidaba Nan aka kar6eta tareda qoqarin fara Bata treatment ‘din gaggawa sbd tashin farko suka gano cikin dake jikinta ne ke qoqarin qarasa zubewa Nan suka fara qoqarin tsayar da jinin.

Tun fannah na ‘daukar abin da sauqi saigasu da kwana asibitin.,,

Koda ayshah ta farka abun farko da fannah tace Mata shine azubar da cikin.

Kallon mamaki ta aiketa dashi fuskarta na qoqarin bayyana farin cikinta tace,

Cikina yananan bai zubeba?

Cikeda mamakinta fannah tace,

Yana Nan amma banga amfanin barinsa ba gwara ki zubar tunda shege n….

Cikin tsawa ta dakatarda ita hawaye suka gangaro Mata tace,

Cikina ba shege bane ‘dan halak ne,
‘dan sunna Kuma Koda shegen ne ta bazan ta6a zubarwaba sbd shika’dai ne abinda Zan riqa gani naji sanyi arayuwata zuwa Nan gaba,,,,
Bansakaki Zama Dani doleba idan kinajin bazaki iya Zama Dani Dan inada cikiba to ko anan Zaki iya tafiya kibarni ahakanma nagode..

Ajiyar zuciya fannah tasaki tareda miqewa tsaye cikin kulawa tace,

Ayshah bance lallai saikin zubarba shawarace nabayar a tunanina ba cikin aure bane Kuma kince bazaki zubarba ba shikenanma ki daina kukan ya Isa haka…Bari naje na kar6o Mana sallama muje gida Dan gskia nagaji da zaman asibitin.

Tana fita ayshah tabi bayanta da kallo cikin mamakin sanyin halinta sbd yanda ta gasa Mata maganganu Amma bataji haushiba..

Fannah ta girmeta zaikai kamar da shekaru biyar,,
Fannah kyakkyawar chocolate mace Mai kyan jiki,,Sam batada zafi tanada hakuri da tausayi Amma a gurin maza labarin bambam ne don kuwa Bata raga musu Bata ‘daga musu qafa hakama batajin wuyar ci musu mutunci sbd namiji ne sanadin qorar da iyayenta sukayi Mata,,

Ahankali tariqota suka fito tashigarda ita mota suka bar asibitin.

A wata anguwar masu Hali gaban wani qaton flat Mai kyau da tsari taga sunyi horn Mai gadi yazo da saurinsa ya bu’de musu gate suka shiga harabar gidan sukayi parking..

Kallonta gidan tayi zuciyarta na karyewa idanuwanta na qoqarin kawo hawaye sbd tunanin iyayenta daya fa’do Mata Dan tabbas tafi sha’awar Zama taredasu Koda acikin ruga suke akan irin wannan daular da aka Tara ta hanyar 6arna.

Qofar shiga babban palon sukayi fannah ta fiddo keys ta bu’de suka shiga.

Zaunar da ita fannah tayi tareda Zama kusada ita cikin sanyin murya tace,

Ayshah Kinga gidana Kuma nikadaice nake rayuwa acikinsa shiyasa ban cika zamaba kullum ina gurin tafiye tafiye Amma ayshah nayi Miki alqawarin ‘dage duk wasu tafiye tafiye na na zauna na kula dake har lokacinda Zaki haihu Insha allah.

Kallon palon ayshah tayi taga ya ha’du matuqa Dan komai najin da’din rayuwa an zuba Masa kafin ta maida kallonta ga fannah cikin hawaye batareda tace komaiba sbd ita duk ba wannan takeso iyayenta da Deen takeso..kuka tasaki ahankali tana shesheka.

Dafata fannah tayi cikin son danne Tata damuwar da kullum take dannewa tace,

Ayshah dole hakuri zakiyi for now har lokacin da Allah zai kawo qarshen damuwar.

Kukanta Tasha Mai isarta kafin fannah ta riqo hannunta takaita bedroom ‘daya daga cikin two bedrooms ‘din dake palon..

Qaton ‘dakine Mai ‘dauke da lafiyayyan makeken gado da wrdrope ‘dinsa da qaton mirror Sai lafiyayyan toilet.,komai na room ‘din is blue and white shiyasa ‘dakin yayi masifar ha’duwa.

Zaunar da ita bakin gado fannah tayi tareda cewa,

Ayshah ga room Nan kishiga kiyi wanka kifito kici abinci saiki kwanta ki huta zuwa anjima idan na huta Zan fita nasiyo Miki ‘yan kayanda Zaki riqa sawa..

Bedroom ‘dinta takoma Wanda ya’danfi na ayshan tsaruwa sbd tsadaddun designers perfumes da kayan kwalliya masu tsada da mayukan dake jere gaban mirronta hakama.

Ayshah kuwa saidata shaqi sabon kuka kafin ta lallashi zuciyarta ta shiga toilet ‘din tayo wanka..

Doguwar riga Mara nauyi ta tarar a kan gado data fito saita ‘dauka ta saka Dan tasan fannah ce takawo Mata.

Abinci fannah tashigo dashi cikin plate ta aje Mata agabanta tareda ruwan faro da magaungunanta.

Dafa cikinta tayi cikin yanayin sonyin kuka tace,

Sbd Kai ko ke zanci abinci Nasha magani…

Murmushi fannah tayi cikin nutsuwa tace,

Na tabbatarda sonda kikewa wannan cikin ba qaramin so kikewa ubansa ba.

Hawayen datake tarewa ne suka gangaro tace,

Ada kenan,,

Miqewa fannah tayi tareda tattara kayan ta Fice dasu batareda tasake mgnba.

Da daddare fannah taje tayowa ayshah siyayyar kayan sakawa Mai ‘dan yawa.

 

**********
Sannu ahankali tafara sakewa sbd yanda fannah ke kulada it’s sosai gashi itama ta ‘dauki son duniya ta ‘dorawa cikin kaman yanda ayshah ke matuqar son abinta,,

Lafiya tasamu gareta sosai Dan tuni fatarta ta canxa sbd hutu daya ratsata danko fita Bata ta6ayiba harsaida cikinta yafara tsufa kullum Sai sun fita shopping kayan baby..

So da dama ayshah najin matuqar tausayin fannah na irin rayuwar data jefa kanta aciki musamman yanxu datake jinta kamar Yar uwarta ta jini.,

Duk wani Jin da’di da kulawa Babu Wanda fannah Bata Bata hakama duk sati take kaita awo asibiti.

 

Zaune take a Palo ta miqarda qafafuwanta dasuka matuqar kumbura sbd tsufan da cikinta yayi tanacin guava da fannah tasiyo mata tana kallon wani shirin larabci a tasar salamtv.

Fannah ce tashigo palon riqeda handbag wata yarinya kimanin shekara goma Sha bakwai tana bayanta riqeda ‘yar Viva bag.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button