HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Kallon fannah tayi cikin murmushi tace,

Anty baquwa Kika kawo Mana.

Zama tayi kusada ita tareda ‘daukar yankan guava ‘daya taci tana cewa,

Eh ‘yar aiki ce nasamo sbd abubuwa sunyi yawa gashi kina gaf dashiga watan edd ‘dinki so Dole muna buqaran helper.. she’ll be the one gyaran gida da girki so that I will be able to take good care of our prince or princess…

Murmushi tasaki tareda kallon cikin tana danne ‘dacin zuciyarta da haryau takejinsa kullum kamar sabo Amma ta koyi danne abinta tun kafin ta haihu abin yashafi ‘danta.

‘dakin dake gaf da kicin fannah ta nunawa yarinyar Mai suna Nana bayan tayi Mata bayanin aikinda zata riqayi.

Tunda Nana tazo gidan ayyuka sukayi ma fannah sauqi Dan tuni takoma aikinta na office Dana harkokinta da mazanta.,

Yau Kam kwance take zuciyarta a dagule sbd kukan data kwana tanayi Wanda kusan kullum saitayisa kafin ta kwanta…

Shiru tayi tana tunanin rashin adalci irin na zuciyarta data kasa cire Deen aranta duk da yaudararta dayayi tareda cin amanarta ya gudu yabarta cikin mummunan Hali.

Fannah ce tashigo ‘dakin cikin shirinta na zuwa office ta kalleta cikin sanyin jiki sbd itama kwanakin hakanan takejin ranta ba da’di.

Ina kwana anty””””tace murya a sanyaye.

Lpia klau ayshah ya jikinki hope dai bakyajin komai?

Kai ta ‘daga tareda tashi zaune ta sauko gadon tana Shirin miqewa tsaye taji takasa yunqurawa sbd riqewar da bayanta yayi tayi saurin kallon fannah cikeda tsoro tace,

Anty bayana nakasa miqewa..

Wat””fannah tace da sauri tareda aje handbag da keys ‘din hannunta ta matso tana riqota….

Ya salam” anty bayana da cikina….

A ki’dime fannah tace,

Ayshah bansani ba ko haihuwace Bari muje asibiti kawai idanma ba itabace Sai muji meyene.

Nana ta qwalawa Kira da qarfi saigata ta iso Nan suka kamota suka saka mota Sai asibiti…

Tashin farko nurses na karbarta sukace haihuwace Nan aka Kira doctors suka shige labour room da ita aka barsu anty fannah cikin fargaba Dan Koda suka iso asibitin ciwon yayi mugun tsanani.

Abu kamar wasa haihuwa taqi zuwa ga azabar datake ciki tayi yawa Suma doctors ‘din dakansu suna tausaya Mata Amma sunyi iya yinsu haihuwar taqi zuwa Sai naqudar wahala takeyi..

Ganin ana neman rasa uwar da babyn yasa suka yanke shawarar yimata aiki cikin qanqanin lokaci fannah tasa hannu tabiya komai aka shiga tiyata da ita.

 

Alhamdulillah cikin ikon Allah ansamu nasarar aikin anciro Mata qaton lafiyayyan balaraben ‘danta daya ‘dauko komai na ubansa.

Tunda aka miqowa fannah shi takallesa cikin showel na jarirai taji wani mugun so da qaunar yaron tashigeta ta rungumesa tana Jin hawayen tausayinsa na gangaro Mata.

Ayshah Bata farkaba Sai gab da asuba Kuma tana farkowa babynta tafara tambaya fannah ta miqo matashi tana kar6arsa taji wani farin cikinda rabonta dashi harta manta,
Cikin tsananin sonsa idanuwanta suka ciko da hawaye cikin farin ciki tace,

My junior Deen,
My love,
My happiness,
My mistake,, you’re my everything now my sweet boy…

Murmushi fannah tayi tareda matsowa ta shafo fuskarsa cikin so tace,

Ayshah is now a mother…

Dariya tayi tana kallon face dinsa tace,

Yes I’m a mother now but not only me,, you’re his mother too.

Nana daketa faman murna ta matso ta kar6esa cikin tsananin farin ciki tace,

Anty ayshah babyn Nan yanada kyau sosai Amma dai ni Zan ringa goyashi ko?

Eh Nana harsai kin gaji da goyo sbd ayshah makaranta zata koma da zaran yafara wayo.

Cikin tsananin farin ciki ayshah takalli fannah tareda cewa,

Anty da gaske?

Yes ayshah coz already admission letter ‘dinki is in hand.

Thank you””””tace tareda kar6ar ruwa da brush ‘dinta take miqo Mata.

Kwanansu uku a asibiti aka sallamesu suka koma gida..

Koda suka koma gida ayshah tayi mamakin ganin maqwaftansu na shigowa barka harda friends ‘din fannah duk da wasu daga cikinsu ba masu kimtsi bane Amma hakan ya sanyata farin ciki koba komai sun nuna farin cikinsu sa6anin iyayenta da uban ‘dan dasuka gujesu.

Koda suna yazo ba wani taro dasukayi andai yanka raguna tareda ra’da Masa suna _Mahmud_,.

Tun bayan haihuwar Mahmud komai na rayuwarta ya canxa ta ‘dauki dangana da hakuri tabawa zuciyarta duk sbd farin cikin ‘danta,,

Tsananin son datake yiwa Mahmud yayi yawa Dan ko kukan ciwo ciki ko wani Abu yake itama zaunawa take ta darza kukanta.

Gata soyayya da tsantsar kulawa yaron kesamu daga ayshah har fannah Dan kullum cikin yimasa shopping take,,,ko Nana ba laifi tana tsananin qaunar yaron sbd kyansa kamar yanda tace,.

Ganin irin yanda fannah ke kashe musu ku’di ba sauqi yasa tayi tunanin fara zuwa makarantar da fannah ta nemar Mata sbd kotayi saurin gamawa ta samu aiki Dan ragewa fannah lalura.

Mahmud nada shekara ‘daya da wata biyar ta yayesa tafara zuwa makaranta bayan uwar siyayyar Kaya da ‘dinkuna da fannah tayi mata ciki harda Bata motarta ‘daya.

 

Shigarta makaranta ya qara canza rayuwarta kwata kwata Dan kuwa Sam Babu Wanda zai ganta yace ayshan gidansu malam babba ce sbd wayewar datayi da wani mugun Jan class daya shigeta uwa uba ayshah Bata ‘daukar reni ko ka’dan yanxu,,
Duk wani kyanta da kyawun fatarta ya da’du Dan bazaka ta6a cewa ta ta6a haihuwaba kullum ka ganta cikin gayu take danko fannah yanxu Sara Mata take a fannin gayu da qwalisa.

Duk wannan abin da’ake maza tsoron tunkararta suke sbd tsoro da fargabar kwarjininta da cika idonta dakuma fuska dabasu ganiba.

Qawarta ‘daya a school ‘din Mai suna Aisha itama Amma shanty ake kiranta,,

Shanty ‘yar tsohon ministern ku’di ce kuma ita ka’dai iyayenta suka Haifa Wanda gata da ku’di suka lalatata ta hanyar shaye shaye da yawon club duk da dai Bata ta6a iskanciba a taqaicema batada saurayi ko ‘daya Dan Bata kulasu shiyasa ayshah ke matuqar qawance da ita batareda tasan tana shaye shayeba.

Fannah zuwa lokacin girma ya’dan fara zuwar Mata ta aje komai ta rungumi aikinta dasu ayshah amatsayin iyalinta da nauyinsu ya rataya kanta musamman ma Mahmud da yanxu yafi Zama da ita sbd rashin zaman ita ayshan.

Yau batada Lectures ko ‘daya Dan haka tana gida sunata nisha’di a palon itada anty fannah suna fira Nana nata wasa da Mahmud Sai tsalle yake Yana dariya.

Kallon fannah tayi tace,

Anty fannah Dan Allah kibawa Yaya Ibrahim dama Mana Kinga Yana tsananin sonki after all Mahmud fa Yana son yaje agolanci”””””ta qarashe zancen cikin tsokana.

Dariya tayi tana kallon Mahmud ‘din tace,

Yaron mummy zonan,,
Da gudu yazo gurinta tareda fadawa jikinta tace,

Anty ce tace Wai zakaje agolanci?

Batareda yasan metake nufiba da agolanci yace,

No I don’t want to go..

Kamosa ayshah tayi jikinta tace,

Amma ai kanason dady ko?

Eh”””yace Yana tsalle tareda yiwa Nana gwalo…

Qaran doorbell yasa Nana miqewa taje tabude saiga shanty tashigo taci kwalliya tayi kyau harta gaji Dan itama ba laifi kyakkyawace farin ayshah ne kawai batayiba.

Da gudu Mahmud yaje yafada jikinta Dan yasaba da it’s sosai sbd itama tana tsananin qaunar yaron ta ‘daga qatuwar ledar hannunta sama tace,

Guess wat it s.,,,

Cheese””yace Yana tsalle.

Girgixa Kai tayi tace,
No.

Ice cream ayshah tace tana kallon ledar.

You failed too”’””shanty tafada Mata tana hararanta.

Mangwaro da yalo”””””Nana tafada tana wage bakinta cikin murna..

Dariya suka sake dukkansu shanty kuwa cemata tayi,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button