TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Ok Allah ya taimaka ai gskia nuraddeen Yana qoqari Dan wlh samun irinsa acikin sa’anninsa zaiyi wuya ta yanda yake yiwa addini yaqi da hidima duk da dai ba acikinsa yatasoba mudai saidai muce Allah yasakawa Wanda yayi jahadin musuluntar dashi,ke Kuma Allah yabaku Zama lpia da zuria Mai albarka.
Amin””””tace cikin farin ciki da Jin da’din anyabi farin cikinta ma’ana mijinta.
Ayshah datun zuwan matar taji zuciyarta na Mata nauyin ganinta ta rintse ido Amma Jin abinda suka fa’da yatabbar Mata dako matar wace,.
Jitayi tana qoqarin ha’diye wani Abu daya tsaya maqoshinta Yana neman danne numfashinta ta miqe da qyar tabar gurin zuciyarta na gaf da bugawa..
Ganin yanayinta yasa shanty saurin Kiran nurses tareda Dr Nan suka fara qoqarin dubata sbd numfashinta dake sama sama kaman zai fita…
Wani qarfine da mummunan 6acin Rai suka taso Mata ta fusge hannunta da ake qaqarin zubawa ruwan allura ta cannula.
Riqota shanty tayi cikin tsoron sabon yanayin data ganta ta girgixa Sai kawai ta fashe da wani irin kuka Mai tafasa zuciya.
Sanyi jikin shanty yayi ta zauna kusada ita tareda dafata cikin sanyin murya tace,
Ayshah Dan Allah kiyi hkr ki rungumi qaddarar Allah har zuwa lokacinda Allah zai iyakance miki..
Tsananta kukanta tayi ta ‘dago cikin kuka tace,
Shanty na rasa komai duk sbd soyayyar Wanda ba Sona yakeba amfani yakeso kawai yayi Dani,
Shanty rayuwata ta lalace sbd mugun mutumin da yake Kiran kansa da shaikh yanxu,,
Na rasa komai na rasa kowa Banda abinda zan dogara dashi naji qarfin gwiwar qarasa rayuwata.,
Shanty I’m nothing but a loose…
Inama ace zan manta komai nakoma rayuwata ta da,,,inama ace Zan iya ciresa a Raina kwata kwata batareda na tunosa Koda na second ‘daya bane,,,,,
Shanty I can’t bear this pain anymore,,, it is really hurting…I can’t bear it.,,,ji nake gwaramin mutuwa sbd kowa bayasona,,,,
Basa Sona basa buqatana sbd laifi qalilan Kuma naso subani dama na gyara babban kuskuren Dana tafka…
Gashi mahmud ‘dina baya taredani duk nasarasa mutanen danake tsananin so da qauna a rayuwa so what is the point of living in misery….
Rufe Mata baki shanty tayi cikin tsananin tausayinta cikin hawaye tace,
You’re my best my only friend I can’t see you suffering like this I promise you won’t feel this pain again,,,you’ll be happy again my eshaaa insha Allah..
Bu’de hanbag ‘dinta tayi ta ‘dauko wasu qwayoyi ta miqawa ayshah tace,
Take this now and I promise you won’t feel a thing again…
Kallonta ayshah tayi da jajayen idanuwanta ta kawai da Kai saikuma wata zuciyar ta ingizata ta kar6a Tasha batareda dogon tunaniba sbd kawai buqatarta ta dainajin ra’dadin da ciwon datakeji cikin zuciyarta..
Kanta taji yafara ‘dan juyawa ta ‘dago takalli shanty saitaga biyu biyu take ganinta Nan ta tashi tana bin ‘dakin da kallo Yana juya Mata saitaji abin namata nisha’di Dan kamar a sama take jinta…..
_mugun mafari_,,,
Sannu ahankali saiga ayshah ta warware Ras kamar ba itaba tuni aka sallamesu suka dawo gida duk da anty fannah tayi mamakin ganin sauyin gaggawa daga ayshan Amma saita dangana hakan da adduar datake kwana tanayi Mata.
Ayshah kuwa sabuwar duniyar sha aka shiga Dan kuwa tuni takoma school duk wata mashaya yanxu tare suke zuwa da shanty Wanda Nan take idanuwanta suka qara bu’dewa ta qara zanzarewa Dan yanxu ko Zama gida Basu cika ba kullum suna club suyi nis su lalla6o gida su kwanta,,,,,
Lokuta da dama tana idan tana cikin hayyacinta zaunawa take tayi kuka kamar ranta zai fita sbd ganin mummunar rayuwar data tsinci kanta sanadiyar iyayenta da Deen,,,
Tanason dainawa Amma abin yayi matuqar shiga jikinta Bata iyawa Dan yanxu shiga kowace iri taga dama yitake ta fita sbd abin ba qaramin fara shiga cikin kanta yayiba Dan ita Shan hauka takeyi harsaida shanty tafara Dana sanin sata aharkar.
Anty fannah alamarin duniya ya taru yasata gaba tayi kukan harta gaji Amma ayshah ta zare ko maganarta ba wani jitakeyiba saidai idan abin yasaketa tazo tana kuka tana Bata hakuri.,,,
Tun anty fannah na ‘daukar abin da sauqi harta gaji tafara tsanantawa ayshah Amma maimakon sauqi saima ayshah ta qara zarewa danko gida Bata dawowa wataran idan sukayi dare saidai takwana gidansu shanty.
Rama da ciwo yafarasaka anty fannah gaba danko fita office Bata iyayi tayi kuka tayi addua tayi fa’da Amma ba wani sauqi Sai kawai ta tattara kayanta tabar gidan bayan ta rubutawa ayshah wasiqa.
Yau da wuri tadawo Qarfe bakwai parking tayi taga ba motar anty fannah gabanta taji ya’dan fa’di sbd tasan anty fannah batada lpia Bata fita ko’ina tunda da’dewa,
Fitowa tayi riqeda handbag dinta cikin shigar doguwar straight gown ta English wear black Sai blue Vail ‘daure akanta da blue designer takalmi masu tudu sosai.,,,
Tayi haske saidai Rama dake tattare da ita dakaga idanuwanta zakayi zargin tana kora qwayoyi sbd a wani lumshe suke.
Palon tashigo Kai tsaye cikin sanyin jiki Sai ganin Nana tayi rakube tanata darzar kuka…
Rass gabanta ya buga cikin tsawa tace,
Can you please keep quiet,,,ke kullum bakida aiki Sai kuka..
Sharce hawaye Nana tayi tareda miqewa ta miqa Mata doguwar letter.
Kallon Nana tayi ta kalli lettern ta kar6a tana yamutsa fuska ta bude tafara karantawa…
Jikintane yayi mugun saki ta zube gurin jikinta na rawa Sai kawai tasaki kuka cikin mummunan yanayi na tashin hankali…
I’ve lost another part of my life today,,,
Once again rayuwa ta nunamin I will never be happy in my life again..,,
Kuka takeyi cikin mummunan yanayi Dan har wani qanqamewa take..
Sunanta taji Nana takira ahankali ta ‘dago da jajayen idanuwanta saitaganta tsaye da kayanta ta rintse ido cikin ra’dadi da quncin zuciya tace,
Kema tafiya zakiyi bazaki iya rayuwa daniba…
Dama wazai iya rayuwa Dani iyayen dasuka haifenima sun gujeni mijin danake tsananin so ya gujeni,
Mahmud ya tafi,,anty fannah ta tafi kema kitafi dama ni nasan bani ba farin ciki arayuwa sbd rayuwata tagama lalacewa bamai iya tolerating din mugayen halayen danake dasu yanxu,,,.
Tana gurin zaune tana kuka Nana ta wuceta tabar gidan cikin tsananin kuka da damuwar halinda tabar ayshah aciki Dan tasan ayshah ada Mai sanyin Hali da hkr tareda nutsuwa Amma yanxu takoma Banda tsiwa da masifa tareda rashin mutunci ba abinda ta iya.
Tunda Nana ta tafi takasa tashi agurin har tsakar dare da shanty tazo suje mashaya ta tararda ita cikin tashin hankali tayi kuka har kukan ya daina fita…
Acikin Daren shanty ta kwashe Mata kayanta suka koma gidansu shanty ‘din sbd iyayenta basa qasar zaune ita kadaice Sai tsohuwar dake tayata Zama sbd karatunta.
Duk iya wani farin ciki tarigada tasan ya qare Mata damuwa da baqin cikin rayuwa sun rigada sun yiwa zuciyarta mummunan kamu sai rayuwa ta qara lalace Mata sbd rugujewar da rayuwar ta ida yi.
_Years back_…..
Lokacinda manyan doctors suka gama iya bincike da nuna qwarewarsu akan matsalarsa sun gano yasamu shafewar qwaqwalwa,,
Sunyiwasu mum bayanin komai maimakon nuna damuwa Sai mum ta nuna farin cikinta akan hakan Dan ko ba komai she’ll get her son back yanda takesonsa…
Davina kuwa hakanan taji hankalinta yatashi zuciyarta taqi yarda da amincewa da karsu fa’dawa Nik komai akan abinda yasamesa dakuma auren dayayi,,,