TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Sam bazata iya 6oyewa ‘dan uwanta yanada Mata da ciki ba Dan gwara yasani yaje ya ceci matarsa da ‘dansa daga baqar wuya.
Tunda ya warke yakomawa normal life ‘dinsa as a Christian Davina takasa zama saidata fa’da Masa komai da farko bai yardaba harsaida yaga nacinta da dagewarta yayi yawa qarshema wayarsa dake ‘daukeda hotunan ayshah dashi ta nuna Masa Nan yaji jikinsa yayi sanyi amma ackin zuciyarsa bayajin tsananin sonta kaman yanda Davina tace yana tsananin yi..
Saidai tausayinta daya mugun shigarsa na yanda tayi sacrificing komai kan sonsa shiyasa yayi alqawarin nemota ya inganta soyayyarta garesa.
Cikin sirri suka shirya tafiya Nigeria shida Davina ta hanyar yiwa mum qaryar Mexico zasu auren wani friend ‘dinsa.
Ba musu mum ta amince suka taho Nigeria tashin farko gidansu ayshah suka nufa Kai tsaye.
Su baba alhaji suka fara cin karo dasu a qofar gida.
Gaidasu yayi cikin mutuntawa Dan Koda yake cikin yanayi na shafewar qwaqwalwa wannan mutunci da tsarkin musulunci har lokacin suna taredashi.
Kallo ‘daya sukayi masa jiki duk a sanyaye suka amsa Nan yaso fara yi musu bayanin abinda ke tafe dashi suka dakatar dashi tareda kallonsa dakyau sukace yabar gidan idan ayshah yazo nema batanan sun koreta basusan inda takeba.
Kallonsu yayi cikeda mamakin yanda suka iya rufe Ido suka Kori yarsu batareda Duba yanayinta na ‘ya mace ba Kuma harda juna biyu ajikinta.
Gida suka koma cikin ikon Allah da zallar mamaki saisuka tararda Murphy a qofar gidan cikin shiga ta alfarma ta cikakken musulmi.
Davina ita tayiwa Nik bayanin waye Murphy agurinsa Nan dai suka tattauna ya sanardasu shi yanxu musulmi ne sunansa muh’d nandai suka ha’da Kai suka duqufa gurin bincike akanta Amma ba wani lbr.,
Mum kuwa tuni hankalinta yatashi sbd antabbatar Mata dasu Nik ‘din basa Mexico.
Davina tun dawowar Murphy taji duk duniya ba abinda takeso kamarsa Dan nutsuwa da tuninta tuni suka qwace Mata Wanda Sai alokacin take qara jinjinawa ayshah Dan yanxune takejin abinda taji Kuma itama a shirye takeda ta kar6i musulunci akan soyayyar datakewa muh’d.
Tun mum na ‘daukar abin wasa saigasu sun shafe kusan wata hudu a Nigeria wanda tuni sukayi Nisa tareda maida hankali gurin koyan karatu da sani gameda addinin musulunci Dan kuwa tuni Davina ta musulunta.
Ganin sunyi neman Amma ba lbari yasa suka koma Amma batareda muh’d ba daya koma Abuja bakin aikinsa.
Lokacinda suka fuskanci mum haukace kawai batayiba ganin ‘yayanta datafi so cikin inuwa da arzikin musulunci..,,
Rufe idanuwanta tayi ta koresu fata fata a rayuwarta dadynsu kuwa bai tauyesuba yabasu damar bin addinin dasuke ra’ayin bi.
Ba 6ata lokaci Deen ya Nemo musu admission a makarantar Madina shida Davina cikin ikon Allah suka samu suka koma Madina suka maida hankali kan karatunsu batareda wata damuwa ba.
Lokacinda suka kammala karatun Davina takoma gida shikuwa zurfafa karatun nasa yayi Sai gashi allah yayi Masa baiwar sanin addini Nan take yayi fice yazamo matashi lamba ‘daya daya haddace alqur’ani da littafai da dama akan addini Dan kuwa duk wani taron musulunci da da’awa Yana cikin manyan baqi da musulunci keji dasu ayanxu,,
Hutu, kwanciyar hankali da arziki Mai tarin yawa sun samu Zama sosai arayuwarsa shiyasa Mata da dama ke sha’awarsa musamman kyawunsa da class ‘dinsa dake fuzgar duk wata mace Mai sauraron fatawarsa.
Siyama salees shine cikakken sunan yarinyar data maqale Masa tun ranar farko data fara ganinsa a wani taro dayazo Nigeria a Abuja tun Yana share Mata hardai ya amince akayi aurensu Wanda ranar ‘daurin aurensu a ranar mahaifinsa ya musulunta Kuma a ranar mum tagano ayshah hartasa aka sato Mata Mahmud takaisa qofar gidan Deen ta aje tareda doguwar wasiqar cewa ayshah ce takawosa akan Bata buqatar sake ganinsa ga dansa Nan yariqe…
Sosai yaji zafin hakan datayi Sai kawai ya ‘dauke yaron ya bar qasar dashi bayan yayi dna ya tabbatarda dansa ne,
Murmushi mum tayi cikin farin cikin ganin tasamu hanyar fara cusa tsanar ayshah cikin zuciyar Deen kamar yanda tasan ayshah ta tsanesa yanzu danso take ko kallon juna karsuyi da mutunci duk ranar dasuka ha’du
Muh’d kuwa duk wani tunaninsa ya karkatasa ga binciken inda zai gano ayshah Dan kuwa lokaci yayi da zai kar6i abarsa kamar yanda ya qudurta.
Mamuh????
_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida…._
_Viawattpad@mamuhgee_
*30*
*_gskia I really appreciate_*????
*_masoyan taura biyu_*????
Zaune take gaban mum Banda tsayayar hawaye ba abinda take sbd duk duniya batajin zata iya abinda mum ‘din tace na cewar ta cire muh’d cikin ranta sbd tasan ba abune Mai yiyuwa ba,
Cikin baqin ciki da damuwa mum ‘din tace,
I will never forgive that horrible ninja lady for wat she has done to my family,,
The family I build with so much love,
She distroy everything for me,,,,
Cikin hawaye Khadija (Davina) tace,
Mum please stop blaming ayshah sbd mu muka dama muka za6i rayuwar datafi, rayuwa Mai ‘dorewa ta gobe a qiyama,,
Tashi mum ‘din tayi jiki a sanyaye sbd gabaki ‘daya yanxu Bata iya zaman mintuna da ‘yayanta sbd zancen addininsu dasuke yimata akoda yaushe.
Cikin sallama yashigo qayataccen palon Yana tashin qamshin turaren Arabian oud cikin farar tsadaddiyar jallabiya fara blue Sai Kyau da hasken fatarsa ya da’da bayyana.
Kallo ‘daya mum tayi Masa ta ‘dauke Kai ta nufi hanyar bedroom ‘dinta yayi saurin Shan gabanta tareda riqo hannunta fuskarsa ‘dauke da wani lallausan murmushi yace,
My sweet mum please don’t stop ignoring me like this,,
I love you so very much mum so will you please stop ignoring me mum,,
Kallonsa tayi tayi son ‘danta da kewarsa na ‘dawainiya da ita ta rintse ido tareda juyawa zatabar gurin..
Granny,,,,
Cak ta tsaya tareda sakin tareda juyowa Nan take tasaki fuska kamar ba itaba da gudu ya qaraso gurinta ta ‘daukesa sama duk da yaqara girma sosai tace,
I miss you so much my beautiful boy..
Kumatunta yaja cikin dariya kamar yanda taja nasa yace,
I miss you too granny but I won’t stay with you today since you’re angry with my daddy.
Bedroom ‘dinta ta nufa dashi tana cewa,
Your daddy is a stubborn man he doesn’t care for me now….
Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka ‘dan bayyana sbd yasan mum ta sauko sosai sbd tsananin sonda takewa mahmud Amma yakasa gane meyasa ta tsani ko sunan uwar Mahmud ‘din afada.
Juyowa yayi gefen Khadija dayar kolacin take zaune tana kuka ahankali ya zauna a sofa Yana kallonta yace,
Menene Kuma Khadija?
Ahankali tace,
Shaikh just pray for me sbd naji ajikina nice Zan biya dukkanin haqqin ayshah da aka zalunta Dan kuwa tun yanxu nafara ganin ishara Kuma na tabbatarda duk inda ayshah take Bata cikin kwanciyar hankali tunda Bata tareda iyayenta da ‘danta duk sbd soyayya.,,,,
Katseta yayi cikin ‘dan yamutse fuska yace,
Karki ha’da kanki da ita sbd ita itace ta za6i kawo ‘danta dantayi rayuwar dataga dama afterall tasan inda nake tunda harta kawomin ‘dana so inda tanada niyyar Zama Dani da tuni ta bayyana kanta Amma she chooses to stay away and wani gefen zuciyana is telling me we are better without each other…..
Kallonsa tayi da jajayen idanuwanta tana girgixa Kai cikin kuka tace,