HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Shigowarsa kenan tareda amininsa nako yaushe Murphy.,Sai Davina dasuka ha’du yanxu cikin school ‘din ta maqale Masa wai wani lecturer ‘dinsu ya hanata shiga lectures yau shine suka shigo department ‘din yayiwa lecturer ‘din magana sbd baya tsoron kowane lecturer shi duk da shima student ne Yana final year ‘dinsa…Amma ba ruwansa duk Wanda yatakasa takashi yake sbd gata da sakewa daya samu daga uwarsa.

Ba zato yaji saukar mutum akansa saigasu sun zube qasa atare..

Holy Christ…yace da qarfi daidai itama tace,

Ya salam””..

Da sauri Murphy da Davina sukayo kansa ya miqe Yana yarfa cikin tsananin azaba yace,

Oh God she broke hand..

Wat””’Davina tafada tana yamutsa fuska.

Zafi yakeji sosai Nan danan student ‘yan neman fada suka ‘dauko kujera aka zaunar dashi Sambatu yake sbd jiyake baitaba Jin azaba irin wannan ba duk da ba wani ciwo bane.

Mum Davina takira tana ‘dauka tace,

Hello my little princess,,,,,

Mum your Nik meet wit an accident his hand and leg got sprained….

Wat,,,, where and how?

One stupid ninja lady fell on him,her face was covered she probably doesn’t see where she was going so……

Take him to hospital now I will be there soon.

Kamasa sukayi zasu fice ya juyo cikin azaba yacewa murphy hand her to school authorities she did it on purpose.

‘dagowa tayi idanuwanta sunyi jajir sbd kuka Dan tunda tafado takasa tashi sbd qafarta da hannunta sun bugu matuqa Amma ba’a ganiba zaa miqata ga hukumar makaranta sbd tafadowa ‘dan gata.

Hannu ta zura cikin niqaf dinta ta share hawayenta tareda dafawa ta miqe tabi securities dasukazo tafiya da ita.

Sai gaf da magriba ta iso gida sbd tajima kafin subarta tatafi dukda sun mata gargadi Mai kyau akan karta Kuma ko lallon hanyarda Nik yabi bare takuma karyasa Dan mum ‘dinsa tace next time aka qara bazata yarda ba.

Kodata dawo gida hankalin ‘yan gidan tashi yayi dasuka ganta tana ‘dingisawa..

Karo na farko data fara qarya arayuwarta kenan Dan cewa tayi ‘dan adaidaita ya fa’di da ita.

 

Zazzafan zazza6i tayi tareda ‘yar qaramar jinyar qafarta Dan satinta kusan ‘daya rabonta da school Sai yau dazataje.

Sam yanxu tadaina Jin da’din makarantar Kuma takasa fadawa kowa sbd kada ahanata Dan tana matuqar qaunar karatun.

Asanyaye take shiri harsaida husna ta lura tace,

Ayshah lafiyarki kuwa?
Kodai jikin ne?

Safarta ta jawo tana sawa cikin muryar karaya tace,

Lafiya qlau kawaidai inajin kasalar zuwane.

Daria husna tayi tana saka hijab ‘dinta tace,

Kodai kin gaji da karatun ne so kike ku zarge keda ya Umar””ta qarasa zancen cikin tsokana.

Murmushi ayshan tayi tareda tuno fuskan ya Umar,,
Tabbas tana qaunar ya Umar halinsa ne bataso na rashin haquri da zafin zuciya Dan da’ace komai zai rage da tafi sha’awar auren nasu yanxu sbd ta huta da karatun Dan tuni yafara fita ranta sbd jikinta na Bata ba alkhairi a karatun Nan gaba.

 

Kwana goma ya share ko cup ‘din ruwa baya iya ‘dagawa da hannun duk da Dr ya tabbatarda ba wata karaya ‘yar bugewace Amma sun ‘dauki ciwon wani irin babba Dan mum har hutu ta ‘dauka Dan kula dashi kawai ko dad ‘dinsu Saida yazo yadubasa Yakoma Germany and yanda suka ‘dau ciwon wani babba.

 

Koda ya warke Yafara zuwa makaranta Sam hankalinsa bai wani kwantaba sbd ayyanawa ransa da yayi Sam ita ba mutum bace aljana ce shiyasa ko mace Mai hijab ya gani koba niqaf Sai ha’diye yawu
Yanxu ko bakin gate baya iya zuwa Saida Murphy sbd tsoron karya ganta.

 

Yau suna fitowa lectures din farko ta fito ta nufi ladies toilet ‘dinsu sbd period take tanason canza pad Dan ita Sam Bata iya wuce two hours da pad ajiki Bata canzaba.

Restaurant ta nufa danta siyo ruwan dazatayi amfani dashi.

Ku’di ta miqa aka miqo mata ruwan tajuyo kenan yakawo kowannensu cak ya tsaya cikeda tsoron ‘dan uwansa yanda jikinta ya’dau rawa haka shima nasa Murphy yayi saurin riqesa tafara takowa ahankali jikinta na tsananta rawa zata bar gun sbd tarigada ta tabbatarda ganinsa ba alherineba.

Ganin ta nufo gurinsu yayi saurin sakin Murphy cikin tsoro da qarfi yace,,

Ghost,,,,
Ghost, ghost…

Aikuwa bashi kadaiba duka sauran mutanen gurin da gudu aka watse Sai ihu ake wasu harsuna fa’duwa.

Tsayawa tayi cak tareda duqawa ta fashewa da wani irin siririn kuka jikinta na sakewa.

Murphy dake tsaye shika’dai ne bai guduba Nan take yaji tabasa tausayi ya tako ahankali ya tsaya akanta cikin tausaya mata yace,

Ki daina kuka Kuma karkiji haushinsu sbd basusan Mai suke taredashiba acikin lullu6inki.

Miqewa tsaye tayi tareda ra6ashi ta wuce kukanta na tsananta.

 

 

Mamuh????

 

_dont forget to vote, follow and comments_
[7/8, 8:41 PM] 0mmer Farouk: *_MAMUH GEEE_*

 

_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida_….

 

_viawattpad@mamuhgee_

*3&4*

Toilet tashige da hanzari tareda rufowa tasaki wani sabon kuka ahankali,

Gabaki ‘daya rayuwarta a makarantar ta zamar mata masifa Wanda take danganta hakan da qaddararta.

Rarrashin kanta tayi daqyar kafin ta zare niqaf dinta ahankali takalli fuskarta jikin mudubi taga baiwa ta kyau da tsarin halitta da Allah yayi mata rashin sani yasa ana mata ‘daukar mummunar halitta.

Share hawayenta tayi tareda maida niqaf dinta tafito tawucewarta gida gabaki ‘daya batareda ta tsaya attending sauran lectures ‘dinta ba.

Da daddare bayan sunci abinci itada su husna tareda sauran yaran gidan suka nufi babban palon baba malam gurin ‘daukar karatun dare Wanda qaidar gidance kullum da dare saisun ‘dau karatu.

Awa ‘daya da rabi sukayi sunayi kafin aka gama.

Gyara Zama baba malam yayi tareda gyaran murya
Nan kowa ya nutsu sbd sauraron Mai zai fa’da.

Kallon sauran dattijawan qannensa yayi kafin yace,

Mustapha ‘dana ne Kuma ya ‘dauko zance Mai girma Don kuwa ya take akidar gidan Nan daya tarar tun kakanni tunma kafin ni mahaifinsa a haifeni..
Ma’ana dai bayan mun tsayarda maganar ha’dashi aure da yar uwarsa jininsa ya tsallake waje yana neman auren wani yaren ma’ana bahaushiya.

Wani yawu iya lami ta ha’diye Dan kuwa tasan mummunan hukunci ‘danta zai fuskanta Dan anta6a irin haka can baya abun baiyi kyau ba sbd Saida aka rasa rayuka.

Tsit palon yayi babu Wanda ya motsa sbd jinjina girman laifin da mustaphan yayi.

Cigaba baba Mal yayi da fa’din,
Mustapha kaje kashirya gobe bayan sallar juma’a za’a ‘daura aurenka saudat a goben zaka koma gida nijar tareda matarka Kuma bamu yafe katako qafarka Nigeria ba kokuma Kiran ‘daya daga cikinmu Sai bayan shekaru biyar.

Sunkuyar da kansa yayi hawayen baqin ciki da damuwa suka ciko idanuwansa sbd hukuncin da iyayensa suka yanke Masa bazai iya jadasuba Wanda wannan tarbiyace da’aka ba zuriar gidan kaf tun suna yara.

Saudat kuwa wani irin kukane ya kufce mata ahankali batajiba Bata ganiba laifinsa ya shafeta bayan auren bazata an datse mata karatu gakuma nesa dazatai da gida bako waya har tsawon shekara biyar.

Jikin kowane yasaki Banda iyayensu maxa dake da’da nanata yi musu fadan kowa ya kiyaye aikata irin hakan,

Baba Mal ma fa’da Mai tsanani ya ‘dora dashi sbd ran iyayensu ya 6aci matuqa.

Umma sakina kuwa Jan ‘yarta tayi cikeda tausayawa suka fice kowama ya fice jiki a sanyaye.

Ayshah kuwa ‘dakin ummi tashige ta kwanta jiki asanyaye tana tsiyayar hawayen tausayin saudat da yaya mustapha.

Kallo ‘daya umminta tayi Mata ta ‘dauke Kai sbd Bata cika kulata kasancewarta ‘yar farin..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button