TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Shaikh kaiba butulu bane karkayi butulci da raharamarda Allah yayi maka ta musulunci ta dalilinta,
Shaikh kome ayshah tazama arayuwa Kaine sanadi,
Koda yake basai nafada ba Zaku gani akaina duk da banjiba banganiba Amma haqqi zai sauka akaina.
Miqewa yayi batareda yakuma tanka zancentaba yace,
Maganar zuwana Nigeria ne yataso sbd gobe Zan wuce insha Allah if you’re still interested in coming with us ki shirya.
Wucewa yayi yabarta farin ciki na ratsa zuciyarta najin maganar zuwansu Nigeria zataje taga muh’d dinta.
Washe gari shida matarsa siyama da ‘dansu mahmud tareda Khadija suka diro Nigeria suka baro mum cikin ‘dibbin damuwar ganin gabaki ‘daya yayanta yanxu kamar ba nataba nantafara tunanin mezai Hana tabi nasu addinin matuqar familynsu zai qara Zama Happy family kamar da.
A qaton lafiyayyan gidansa dake asokoro suka sauka Wanda Nan aka qaro securities agidan
Siyama hankalinta ya qara kwantawa Dan dama tafison zamansu a Nigeria akan can Paris ‘din,,
Babbar damuwa da tashin hankalinda take ciki shine rashin haihuwarta har yanxu,,
Tayita yimasa compain akan hakan Amma bai damu ba sbd ganin mahmud dayake jinsa cikin jinin jikinsa Dan ba qaramin so yakewa yaronba.
Hakan yasa gabaki ‘daya hankalinta ya tashi dason haihuwa sbd batason Koda wasa yayi tunanin maido karuwarsa tada Dan ita Bata ‘dauketa matarsaba saidai karuwa Dan bataga dalilin ha’da shimfida da kafiriba tunda alokacin yanada sauran dabiar kafirai ataredashi.
********
Wani qaton babban hotel daya amsa sunansa na manyan mutane,
Acikinsa akwai manyan halls na alfarma dan meetings ko taron manyan mutane.,
Hakama akwai club na ‘yayan manya dake cikin gurin Wanda ya tsaru ya ha’du ba kadanba.,,
Zaune take cikin club ‘din tayi crossing legs tana sanye da wata designer English gown red datayi masifar yimata kyau sbd kwantawar datayi ajikinta Sai wani siririn black scarf Mai adon red data ‘daure gashinta gefe dashi Wanda duk Rabin gashinta a waje yake sbd tsawonsa Sai hakan ya qara Mata kyau,,
Abuge take banda lumshe idanu ba abinda take shanty dake zaune gefenta waya take tana kur6a ruwan qwayoyi ahankali tana lumshe ido,,,
Wani kyakkyawan saurayine ya qaraso gurinsu cikin qasaita na kasancewarsa ‘dan senator ya kalli Ayshah dako kallo bai ishetaba yace,
Eshaah my love look at me please,,,,look wat your love has done to m..
Banza tayi dashi tareda ‘daka cup ‘din dake gabanta ta shanye zuciyarta na tafasa taji Bata dainajin qunar zuciyarba ta ‘daga wani cup ‘din takai bakinta yayi saurin Kai hannunsa zai riqe cup ‘din ta miqe tsaye ta ‘daga hannu ta sharara Masa wani lafiyayyan Mari Nan take ‘yan koransa sukayo kanta kafin suyi wani yunqurin takuma yanka Masa wani Marin Nan take guri ya kaure da hayaniyar fa’da sbd wani ‘dan governor dayake matuqar son ayshan ya shiga fadan dama yanajin haushin Abbas ‘din sbd yanason ayshah Nan suka hau fa’da harda fasa kwalabe.
Shanty datafi ayshah qarfin jini Dan yanada wuya ta bugu duk abinda Tasha kuwa,
Kamo hannun ayshar tayi suka fito harabar hotel ‘din inda Nan take gurin yacika sbd fadan Nan yadawo.
Fixge hannunta tayi cikin maye tace,
Let go of me shanty,,,I’m not done,,,let me teach the bastard a lesson…
Fitowarsa kenan daga meeting ‘din dasukayi agurin yayi mamakin ganin mutane agurin tunda ko hayaniya ba’ayi sosai agurin.
Kamar a mafarki idanuwanta suka sauka akansa ta lumshesu tasake bu’dewa sai kawai tasaki dariya Mai qarfi cikin tsananin maye tareda nunasa tace,
There he is,,,,the one and only Niklaus Aiden,
The greatest cheat so far…
Kanta securities dinsa sukayo sbd tuni gurin yayi tsit kallo Yakoma kansu ganin tana qoqarin 6atawa shaikh suna cikin bainar jama’a Amma Abbas yayi saurin Shan gabansu cikin rashin mutunci yace,,,,.
Karku fara ta6amin babe okay…
Dariya takuma saki tareda nunasa cikin maye tareda kallon shanty da juyayun idanuwanta tace,
Look at him shanty my sweet friend,,,
He is the father of my poor son Mahmud…
He is nothing but a cheat,,,,he uses me and run away like a,,,,, like a,,,
Yesssss like a mosquito..hahhhhhhh
Rintse idanuwansa yayi zuciyarsa na mugun tafasa gashi tuni yafara ganin hasken cameras na tashi ana ‘dauka koba’a fa’daba ya tabbatarda itace ayshah uwar ‘dansa,,,
Kanta securities sukayo tayi saurin zillewa tana dariya ta isa gabansa takallesa from head cikin dariya ta ta6a Masa tana cewa,
Wow Mama’s boy yatara muscles bayan yasha duka agunsu ummmmnnn Yama sunansa,,,,,yesss ya Umar the great heartless parson of the universe,,,,look shanty everyone look”””””tafada tana qoqarin Kai hannunta kan damutsansa cikin tsananin 6acin Rai da baqin ciki ya watsa Mata Marin dayasa Rabin mayen dake tareda ita sakinta ya fa’da mota da qarfi driver yaja sukabar gurin wasu na tir da halinsa na 6oye da yau tsohuwar karuwarsa ta tona..
Ita kuwa baqin ciki takaici da danasani ne suka shigeta na abinda tayi cikin mayen shanty tajata sukabar gurin..
Koda ya Isa gida Zama yayi a kujera zuciyarsa na tsananin tafasa he can’t believe he once fall for that shameless crazy lady,,,no I can’t love that thing”’yafada da qarfi Yana miqewa tareda fadawa toilet yasakarwa kansa ruwa Dan ji yake kaman zaiyi bindiga sbd baqin ciki da takaicin ganin Wadda ake cewa yaso abaya.
Qin fadawa Khadija yayi yaga ayshah sbd bayajin zai iya cigaba da Zama da mace kamarta,,,
Koda yafadawa muh’d kuwa ganin yayi hankalinsa yatashi Nan yaqara labarta Masa halayen ayshar nada shidai shiru yayi Dan baiga duk wasu gud qualities dake cewa tanadasu ba atareda ita.
Kwana biyu da faruwar hakan sukaje shopping a wata qatuwar sabuwar mall da’aka bu’de itada shanty duk da har lokacin ranta da zuciyarta kullum qara qonewa suke da baqin ciki da tsanarsa akan gagarumar qiyayyar daya nuna Mata ta hanyar marinta Dan abin ya daki zuciyarta matuqa Dan kwana tayi ta wuni tana kuka bayan mayen yasaketa ace mutumin dataso harta jefa kanta cikin wannan mummunan rayuwar shine ya ‘daga hannu ya mareta.
Doguwar gown ce ajikinta Ash kamar ta maza Amma tanada shape da aljihu na gaba Dana gefe gefe tayi matuqar yimata kyau sbd kaskenta da kyawunta daya fito duk da tuni ta manta wata kwalliya,,,
Facing cap tasaka akanta red duk da gashinta ba duka yashigeba Amma ko ajikinta sbd yanxu ba komai take gane shine daidaiba.
Wayartace kawai ahannunta
Shanty ma dai goduwar rigarce Amma ita normal Arabian gown baqa Sai qaramin scarf yellow ‘daure akanta.
Shanty ke ‘daukar komai itadai Banda tunani ba abinda take duk da Tasha ka’dan kafin tafito abin dai yau da ‘dan sauki bazakace Tasha komaiba matuqar ba magana tafara ba.
Daf da zasu fita taji gabanta yayi mummunan fa’duwa sbd muryar dataji har abada bazata mantataba…
Da sauri ta juyo tare jikinta har rawa yake tace,
Mahmud,,,,
Wat””””tafa’da da qarfi sbd ganin waye yake riqeda mahmud ‘din…
Riqe yake hannun siyama tana tareda Khadija suna shopping cikin nisha’di hankali kwance…
Rantane yayi mummunan 6aci zuciyarta ta rufe ta qarasa gabansu batayi wata wata ba yankawa siyama wani gigitaccen mari,
Arazane suka kallota Khadija ta zaro Ido zatayi magana a qule ta ‘daga Mata hannu tareda Kai hannu zata jawo ‘danta taji anriqe Mata hannu tareda tureta baya cikin tsananin 6acin Rai ya kalli siyama dake dafe da kumatu ya maida kallonsa kanta yace,