TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Don’t you dare touch him with these dirty hands dasuke aikata sa6on Allah,,,just leave here quitly sbd I won’t tolerate your nonsense again so just leave..
Kallonsa tayi ido cikin Ido idanuwanta na cikowa da ruwa tace,
I hate you,,I hate you so very much,,I’ve never regretted anything the way I regret knowing you in my life,,
You take away my son from me you cheat….
Riqeta shanty tayi da sauri sbd tuni tafara jawo musu attention ‘din mutane..
Kallon Khadija dake kukan ganin mummunar rayuwar da ayshah ta tsinci kanta aciki yayi cikin 6acin Rai da takaici ya nuna ayshah yace,
See,,, see the woman you’ve been praising and talking about.,,
Girgixa Kai tayi cikin kuka tace,
Shaikh ayshah is a decent and…..
Will you please keep quiet,
If this is the kind of girl I once loved then I must say mum is right she’s not the kind of girl I should loved or married,,,,,
Kallonsa ayshah tayi da sauri idanuwanta na 6arewa da hawaye ta kalli Khadija tace,
I will never forgive your family for this,,,,
Juyawa yayi a fusace tareda riqo hannun siyama da Mahmud yabar gurin.
Duk yanda taso daurewa kasawa tayi ta durqushe a gurin tareda fashewa da kuka cikin qunar zuciya.
Tabbas ba itaba ko shanty yau zuciyarta ta ta6u da abinda yayiwa ayshah..
Koda suka koma gida gabaki ‘daya kukanta sabo yadawo Dan kuwa saiyau ta qara gane kuskuran data tafka.
Kwana biyu duk yarasa gane kansa Dan duk yatuno abinda yafaru saiyaji ransa yayi mummunan 6aci sbd hakanan wani gefe na zuciyarsa ke cewa bai kyautaba koba komai bai kamata ace da aurensa akanta yabarta tacigaba da gantali agari Dole dai ya kawota gidansa ya killace ko kuwa ya sauwaqe mata.
Siyama Kam duk inda hankalinta yake ya tashi sbd ba qaramin ka’duwa tayi da ganin ayshah ba Dan kuwa Bata ta6a tsammanin tanada kyau ko ma’ana ba sbd Jin cewar kullum cikin hijab take,,,indai har tana cikin hijab Deen yakamu da mugun sonta to kuwa yanxu ma data zare hakan bazaiyi wuyaba itakuwa bazata ta6a yarda ko Bari ayshah tadawo rayuwar mijintaba Dan tasan itace da rabon barinsa.
Khadija kuwa rayuwa tayi Mata zafi sbd muh’d daya fito fili ya nuna rashin sha’awar sonta gareshi,
Nan komai ya dagule Mata ta rasa Ina zata saka kanta Dan har ciwo ta kwanta Amma qememe yaqi ko zuwa dubota sbd har cikin ransa yakejin zafin abinda mum tayiwa ayshansa.
Su shanty tafara bi batareda sanin shaikh ba tun suna wulaqantata har shanty ta ‘dorata akan network ita kuwa ayshah cewa tayi ba ruwanta kowa tasa ta fishshesa….
Tun Abu na wasa saigashi zance ya bayyana har cikin jaridu cewar matar babban matashi shaikh nuraddeen da qanwarsa sun kar6i number ‘daya a fannen shaye shaye..
Ranar da jaridar ta fito kasa bacci yayi tuni ciwo yafara qoqarin kamasa sbd baqin ciki da takaici,
Mum lokacinda taga abinda ke faruwa zubewa zaune tayi tana tsiyayar hawaye sbd inda qaddarar Khadijar tafi muni ita harda maza sha’aninta takeyi.
Tun ranarda jaridar ta fito Bata dawo gidaba sbd tasan mummunan hukuncinsa dazata tarar Sai kawai suka cigaba da sha’aninsu duk wannan sha’anin dasukeyi ayshah Bata ko kallon Khadija bare Bata cika ko amsa maganartaba Dan duk wani Wanda ya danganci Deen ta tsanesa.
Yau zaune suke a garden din gidan suna shaqatawa su duka ukun,,
Shanty da khadeee Sai annashuwarsu suke ita kuwa wayarta take daddanawa duk da kallo ‘daya zakayiwa ayshah kasan Sam ta manta da ya farin ciki yake,
Dogon pencil jeans blue ne ajikinta da Pink armless top ta ‘daure gashinta tsakiyar kanta Yana lilo…
Gate sukaga anbude hankinsu Yakoma can Banda ayshah dako ‘dagowa batayiba taci gaba da kallon wayarta.
Motar Deen khadee tagani ta miqe da sauri tareda Kiran sunansa.
Itadai ayshah banxa tayi dasu duk da taji abinda Khadijar tafada tacigaba da abinda takeyi.
Cikin takun qasaita da burgewa yake takowa fuskarnan a ‘daure Amma kyawun fuskar ya Hana aga mummunan 6acin Randa ke tattareda ita bayyana,
Tsayawa yayi gabansu tareda kallon Khadija Rai amatuqar 6ace ya nuna Mata mota.
Turo baki tayi cikin qunquni tayi cikin gida Dan dauko kayanta.
Har ya juya ya tsaya cak tareda juyowa ya kalli gefenta ahankali yaga Sam ko kallo duk Basu ishetaba saima game ‘dinta datakeyi…
Kayan dake jikinta ya kalla yaji ransa ya 6aci a qule yace,
You’re also coming so just stop that rubbish and get up….
Rintse idanuwa tayi tana qoqarin danne hawayenta zuciyarta na karyewa tace,,,, why is he doing this to me ya Allah,,i loved him more than anything is this the punishment for the mistake I’ve done,,,he is always the reason for my tears…
Hawayen datake dannewa ne suka gangaro Mata ta miqe zuciya karye zatabar gurin baisan sanda ya riqo hannunta ba sbd yaga hawayen dasuka gangaro Mata Kuma sunyi matuqar tasiri a zuciyarsa ta yanda bazai iya tafiya yabarta ba.
Juyowa tayi ta kallesa da idanuwanta dasuka ka’da cikin karyewar zuciya tace,
I’m not coming Deen,
Nida Kai yanxu akwai matuqar banbanci duk da ko awancen lokacin akwai banbancin Amma so yarufemin Ido nakasa gani I don’t want to repeat dsame mistake now,,
Kaci gaba naci baya so let’s just end this now sbd bamai Sona yanxu bamai iya Zama Dani Dan nazama abin kunya,abin gudu abin kyama…
Fixge hannunta tayi ta juya da sauri tabar gurin sbd kukan daya qwace Mata Dan kuwa tabbas tana tausawa kanta duk ranar da shanty ta tattara takoma gurin iyayenta.
Harya shiga mota yaji bazai iya tafiyaba gwara ya ‘dauketa ko gidan uwayenta yamayarda ita maimakon wannan mummunar rayuwar datakeyi.
Kuka take ahankali zuciyarta na qara karyewa taji anriqo hannunta a hasale ta ‘dago tareda fixgewa Amma ba qaramin riqo yayi Mata ba yafara janta tana tirjewa harya saka mota ya rufe yashiga yabar gidan da shanty tsaye tana hawaye..
Koda ya Isa gidansa dama part biyu ne Sai nasa atsakiya ya bu’de part ‘din datun farko akayi da sunanta sbd baisan haka halinta yakomaba ya jefata ciki tareda koma gate yabawa securities gargadin karsu kuskura subarta fita Koda wasa tukuna ya juyo ya nufi part ‘dinsa inda anan ya tararda siyama zaune cikin ado tana kallo Mahmud kuwa dama Yana school.
Mamuh????
_dont forget to follow, vote and comment_
*_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida…._
_Viawattpad@mamuhgee_
*31*
Tunda tazo gidan kwananta biyu Bata Kuma sakashi a Ido Bata damu ba Dan dama bashine a gabanta ba hasalima iskancinta ta tsulawa a gidan son ranta sbd ganin take taken siyama data ‘dauki tsana da kishi ta saka Mata,,
Abu ‘daya ke damunta shine yanda tun ranar data dawo gidan ya ‘dauke ‘danta yamaida gurin mum sbd wai karyaga munanan ‘dabi’unta,,,,
Khadija ce kawai abokiyar firarta wani lokacin musamman yanda suke cikin tsananin kewar kayan mayensu hardai ita ayshah Dan jitake kamar ta zare sbd rashinsu shiyasa kowa ya ta6ata a gidan Bata raga Masa sbd takaicin rashin kayan caza kwakwalwa,..
Tunda ayshah tadawo gidan siyama take cikin baqin ciki da takaici tayi mitar harta gaji Amma Yama qi sauraronta sbd idan har ayshah tabar gidan to gurin iyayenta zai maidata Amma ba yanxu ba saita dawo cikakkiyar nutsuwarta sbd yasan suka ganta ahaka zuciyarsu bazatayi dadiba,,,,
Kwance take cikin tsararen palonta ta qurawa tv Ido Amma ba kallon takeba tunani take ta yanda zata samu ganin shanty Dan tayi kewarta da Kuma kayan korawa.,