HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Cak ya tsaya akanta sbd bacci daya tarar tayi abinta hankali akwance,

Zama yayi kusada ita tareda qurawa face ‘dinta Ido Yana kallon natural beauty da kuma yanda fatarta ke kyalli saidai tayi wata irin Rama duk da yamanta yanda take ada Amma yasan tabbas wannan ramace,

Wayarta dake aljihun wandonta tafara haske alamar shigowar Kira ahankali yakai hannu yazaro ya Duba dakyau saiyaga shanty ce ke kiranta Sai kawai yayi rejecting tareda blocking ‘dinta ya shiga contact ‘dinta yayi wiping komai sbd karma tasamu damar Kiran wani akawo Mata kayan mayen.

Miqewa yayi ya fice daga palon ya nufi motarsa yashiga yabar gidan.

 

Siyama kuwa tunda tashiga palonta takasa zama takasa tsayi Jin zuciyarta take kamar zata bindige ta watse sbd baqin ciki da takaicin dake cinta.

Tabbas Dole tayi gaggawar ‘daukarwa isakancin ayshah mataki tun kafin mijinta yafara son ayshan ko yanxu Dan hakan na gaf da faruwa matuqar ayshah nacikin gidan,,,,Dole ne ayshah tabar gidan Nan da gaggawa.,,,,,,tafada tana Zama kan kujera ranta na Dan saki sbd tunanin daya fa’do Mata.

 

Baidawo gidanba Sai dare Koda yadawo tuni tabar ‘dakin takoma part dinta tacigaba da sha’anin gabanta.

Haryayi Shirin kwanciya ya kwanta siyama Bata shigoba tanacan tana fushi,

Fitowa yayi cikin kayan bacci na maza Ash color ya nufi part ‘dinta.

Kwance take itama cikin kayan bacci tana ganinsa ta ‘dan ‘daure fuska ya lura Amma ya share ya tsaya bakin gadon tareda zura hannunwansa cikin aljihun wandonsa yace,

Are you ok?

Yes”””””tace Masa Kai tsaye batareda ta saki fuska ba.

‘daga kafada yayi yace,

Ok Saida safe.
Ya juya ya wucewarsa.

Sabon takaici ne yataso Mata ganin ya tafiyarsa da gske kenan bazai iya rarrashinta ba.

Qasa hakuri tayi ta sauko gadon tabi bayansa.

Shikuwa kasa komawa part ‘dinsa yayi yasamu kansa dason zuwa yayiwa ayshah Saida safe itama.

Cikin nutsuwa yashigo bu’de qofar yashiga,
Bata palon saidai kayan kallon palon a kunne suke musamman ma qararsu datayi yawa ya girgixa Kai Yana cewa,

Problem queen.

Kashe kayan yayi harzai fice yaji sheahekar kuka na fito daga bedroom ‘dinta.

Shiru yayi kamar ta tafiyarsa saikuma zuciyarsa takasa nutsuwa ya nufi bedroom ‘din ahankali ya shiga.

Zaune take qasa can qarshen gado ta cusa kanta tsakiyar qafafunta kuka take sosai kamar ranta zai fita Wanda tunda rayuwarta ta ta6ar6are kullum komin dare saitayisa da hakan ne take ‘dan rage nauyi da qunar zuciyarta.

Tsayawa yayi daga bakin qofar kansa na fara sarawa sbd qarar sautin kukan dake shiga kunnuwansa na dawo Masa da sautin kukanta adah,

Rintse idanuwansa yayi da qarfi sbd kukan namatuqar motsa qwaqwalwarsa musamman yanda abubuwa keson dawowa qwaqwalwansa da qarfi Nan take kansa yafara juyawa ya dafe kan da qarfi Nan ‘dakin yafara juyawa dashi Sai kawai ya yanke jiki agurin ya zube.

Qarar fa’duwarsa tasata ‘dagowa ahankali saita gansa zube qasa kamar ba Rai ajikinsa.

Fa’duwa gabanta yayi mummunan yi ta taso jikinta na 6ari ta zube gabansa tareda Kiran sunan Amma ba motsi
Yawu ta ha’diye cikin tsananin tashin hankali ta jijjigasa iya qarfinta bai motsaba da gudu ta ‘debo ruwa toilet cikeda roba ta zuba Masa Dan tuni ta manta da yayyafa ruwan ake.

Wurgi tayi da robar ta zube qasa tareda kamosa jiki na rawa ta qara Kiran sunansa kuka na su6uce Mata Nan tafara rera kuka ahankali Mai tattareda kashe jiki sbd Bata ta6a tunanin sonda takewa Deen ‘dinba haryanzu yananan kamarma kullum qaruwa yake,.

Ahankali ya bu’de idanuwansa tareda ‘daga hannu da qyar ya dafe kansa saiyaji jikinsa yayi tsananin mutuwa na wani mugun tausayinta sbd kukan dayaga tanayi sosai sbd ganin halinda yashiga,

Murya qasan maqoshi yakira sunanta kawai saita miqe da gudu tabar gurin sabon kuka na zuwar Mata na yanda ko yaushe dai sonsa keyiwa zuciyarta galaba Wanda Kuma taga illar hakan yakamata ace takoyi darasi Amma gashinan cikin mintuna qalilan ta manta halinda take ciki duk akansa ta rikice ganin halinda yashiga yanxu.

Kasa barin ‘dakin yayi ya zauna bakin gadonta jikinsa na rawar sanyin ruwan data jiqasa tsaf dasu ga sanyin ac.,

Lafewa yayi jikinsa amatuqar mace Dan tabbas kukanta ya ta6a zuciyarsa.

Har tsakiyar dare tana Palo rakube tana kuka saidataji shiru ta miqe jiki a sanyaye ta nufi bedroom ‘din,

Kwance yake bacci ya ‘daukesa ya takure guri ‘daya alamar sanyi.

Qarasowa tayi bakin gadon ta zauna tana kallon face ‘dinsa hawaye nacigaba da gangaro Mata tajawo bargo ta rufa Masa cikin sanyin muryar kuka tace,

Deen na yarda da soyayyarka itace qaddata,
Banta6a tunanin zuciyata zata so wani Abu duniya kamar yanda take sonkaba,
Duk wata tarbiyata da alada ta iyayena da kakanni na asuli na zubar na za6i soyayyarka sbd Kaine farin ciki Ashe bansaniba Kuma Kaine baqin cikina,
Tabbas Dana tankwara zuciyata nabi za6in iyayena na auri ya Umar da duk wahalarda zansha arayuwa inada ladar hakurinta sbd iyayena nakewa biyayya,

Deen banyi Dana saninkaba arayuwa sbd har yanxu zuciyata takasa yimin adalcin cireka acikinta musamman ma yanxu danake ganin qiyayyata qarara a idanuwanka Wanda hakan ba qaramin karya zuciyata yayiba Dan kuwa na tabbata hasararriyar data rasa komai.,

Mahmud ‘dina danake ganin shine ‘dan farin cikin daya saura arayuwata shima karabani dashi sbd kaima kana gudun ‘danka yayi irin halina sbd na Zama abar gudu ga kowa,
Ka rabani da iyayena,
karabani da farin cikina,
Ka tarwatse rayuwata,
Qarshe ka rabani da kanka but still zuciyata kaitake so why deen.?

Kukane yaci qarfinta tayi shiru zuciyarta na tsananin zafi da qunar halinda take ciki…

Da sauri ta miqe sbd kukanta daya fara sauti Dan karta tadashi Wanda ita Bata saniba duk abinda take fa’da yanaji
Jikinsa yayi matuqar sanyi Dan baita6a tunanin haka take sonsaba Sai yanxu,
After what all happened she really wants to give his love a chance…

Rintse idanuwansa yayi jijiyoyin kansa na tashi tausayinta da sonta na shigarsa lokaci ‘daya musamman yanda yakejin ‘dacin rabata ‘da ‘danta da akayi lokaci ‘daya kenan wanine ya ‘dauke mahmud yakawo Masa ba itace takaisa da kantaba.

I’m the reason for all her pains and sorrows,
I’ve been acting to harsh towards her,
I’ve insulted her for no reason,

Rintse idanu yayi zafin abubuwan na shigarsa kamar yayi kuka,
Ayshah kukanki yazo qarshe insha Allah..
From tomorrow i will give you your full right as a lovely respected first wife.

Har akayi asuba idonsa biyu cikin tsananin tunani Nan take Sai kansa yafara wani mummunan ciwo Wanda baita6a irinsa ba musamman yanda kaman tunaninsa ke neman dawowa da qarfi out of control.

Da qayar ya iya fitowa yaje masallacin gidansa sallar asuba.

Akan idon siyama ya fito hawayen datake dannewa suka silalo Mata kenan dai agurin ayshar ya kwana.

Daga masallaci part ‘dinsa ya wuce Kai tsaye ya kwanta sbd har time ‘din jiyake kaman kansa zai buga Dan har wani jiri ya ke gani.

 

 

 

Mamuh????

 

_dont forget to follow, vote and comment_
[7/29, 10:07 AM] ‪+234 902 378 7901‬: *_MAMUH GEEE_*

 

_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida…._

_Viawattpad@mamuhgee_

*33*

 

Qarfe bakwai na safe motar muh’d tashigo harabar gidan badan yasoba sbd tun ranarda Deen yamaido ayshah gidan ya yafe gidan gabaki sbd zuciyarsa bazata ta6a iya ‘daukar ganin ayshah da waninsa ba.,
Amma yau dolece sbd tun jiya mum ke Kiran Deen Bata samunsa shine takirashi ta sanardashi mutuwar Finn cikin tsananin kuka da tashin hankali gashi daddynsu tuni Yakoma Madina da Zama saidai yakan ziyarceta time to time.,
Ga Deen da Khadija basanan tayi kuka harta gaji shine ta yanke shawara ta sallami duka masu aikinta da zarah Mai kulada mahmud tayo Nigeria gurin ‘yayanta danta gaji da muguwar rayuwar ka’daicin datake ciki tana buqatar ‘yayanta atareda ita Koda hakan na nufin saita musulunta infact she’s ready to become Muslim kamar mijinta da yaranta musamman ma Mahmud shiyasa tana dirowa qasar takira muh’d yazo ya ‘dauketa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button