HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Ayshah Nima ayau na tabbatarda kece qaddarata,
Nasoki abaya so Mai tsanani,
Yanxuma Dana manta komai still zuciyata saidata kamu da sabon sonki nakuma tabbatarda dazan Kuma samun wani memory loss ‘din I will still fall for you but wannan shine sakayyar….

Rintse idanuwansa yayi ga mamakinsa saiga hawaye na tsiyayo Masa ya girgixa Kai zuciyarsa na qara ‘daci yace,

Ayshah go, leave, I don’t want to see you again.

Tashi tsaye tayi cikin tsananin zafi da qunar Rai tana kallon tsakiyar idanuwansa hawaye na qoqarin sauko mata tace,

Deen me kake zargi dashi?

‘dauke Kai yayi yace,

Just leave,.

Juyosa tayi da qarfi cikin kuka tace,

Deen ni kake zargi da wani?
Ni ayshah kana tunanin Zan iya rayuwa da wani namijin bayan kai.?
Deen do you really hate me that much da har kakemin wannan zargin after all the years danayi batareda kaiba Amma na tsare mutunci aurenka.?

Wannan shine nawa sakamakon?
Deen when will you stop hurting me and ruining my life?

Girgixa Kai tayi cikin hawaye idanuwanta na kadawa jajir sbd wannan shine Abu mafi Muni dayayi Mata arayuwa and this mark the end of their relationship.

Share hawayenta tayi tace,
Bazan ta6a manta wannan ranarba sbd itace ranarda na datse duk wani sauran hope na tsakanina dakai,
Nagama dakai Deen.

Juyawa yayi ya fice a fusace hawayensa na qara 6allewa.

Zubewa tayi bakin gado tareda sakin kuka ahankali zuciyarta na Kara karyewa tace,

Baba kuyi hkr gida Zan dawo wlh zuciyata fashewa zatayi Ina cikin tsananin rayuwa Ina buqatarku ku yafemin.

Har time ‘din mahmud bai tashi bacci ba hakanan ta tadashi ta saka Masa Kaya ko wanka batayi masaba suka fito.

Mum da Khadija tagani bakin qofar palonta jiki asanyaye Khadija kuwa kuka takeyi sosai.

Kallon Khadija tayi itama idanuwanta na sake 6arewa da hawaye tace,

Khadija mum yau ta qara tabbatarminda Bata qaunata and she will never do sbd nasan she’s behind all this,,, anyways dama I should be ready for even more of these since she’s here Amma komai yariga ya qare…

Hawaye ne suka ganagarowa mum ta bu’de baki da zatayi magana ayshar tayi wucewarta riqeda hannun ‘danta.

Ayshah na fita gidan kamar daga sama Khadija taga mutum bayan flowers ‘din bayan windon ‘dakin ayshah ta zaro idanuwa tayi cikin tsoro harzata gudu ‘daki Sai tafasa ta nufi part ‘dinsa da sauri jiki na rawa tafada Masa
A zafafe ya qaraso gurin tareda cakumosa siyama dake bayansu ta lalla6o da ta6aryarsu ta aiki ta ‘daga da qarfi ta kwalawa Deen akai Nan take ya zube agurin Khadija ma na juyowa ta qwala Mata tasaki qara Mai qarfi itama ta zube qasa.

Hanya ta nuna Masa tareda basa kudin aikinsa da sauri ya fice haryana tuntu6e bayan ya maida uniform ‘dinsa na aikin security agidan.

Ta6aryar ta maida kicin da sauri kafin tadawo gurin tareda daka kururuwa tana Kiran mum na mum ta qaraso tana ganin ‘yayanta biyu zube qasa hankalinta yayi mumman tashi suka kwashesu Sai asibiti.

 

 

 

 

 

Mamuh????

 

_dont forget to follow, vote and comment_
[7/29, 10:07 AM] ‪+234 902 378 7901‬: *_MAMUH GEEE_*

 

_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida…._

_Viawattpad@mamuhgee_

 

*34*

 

Tafiya ka’dan tayi bayan tabar gidan taji takasa riqe kukan dake son fito Mata ta durqushe agurin tasaki kukan cikin qaramin sauti zuciyarta na neman tarwatsewa..

Zama kusada ita Mahmud yayi tareda 6ata fuska zai fashe da kukan shima yace,

Mummy who beat you?

Sake sakin Wani kukan tayi tana jawo ‘danta jikinta.

Saida tayi iya Wanda zuciyarta ta ‘dan rage nauyi kafin tafara qoqarin tashi taji ankira sunanta cikin sanyayar murya Mai taushi.

‘dagowa tayi tareda miqewa tana juyowa idanuwanta suka sauka kan muh’d dake tsaye akansu yayi folding ‘din hannuwansa a qirjinsa Yana kallonsu cikin tsananin sonta da tausayinta sbd mum takirasa tafada Masa Amma bayajin zaifara zuwa asibiti gurinsu Deen batareda yafara sanin inda ayshan da ‘danta sukeba.

Sabbin Hawaye ne suka gangaro Mata cikin karyewar zuciya tace,

Murphy..

Lumshe idanu yayi zuciyarsa na tsananta tafasa da ganin yanda ayshan takoma.

Cikin kukan da baya fita sosai take kallonsa tace,

Where were you Murphy?
Deen has destroyed my life,,
I’m not dsame ayshah you used to know,,
I’m a shame now…… kukane ya qwace Mata ahankali tayi shiru tana rerowa zuciyarta na qara kaririyewa.

Matsowa yayi gabanta ya tsaya murya a karye yace,

Ayshah insha Allah wahalanki da kukanki ya qare,,
Girgixa Masa Kai tayi cikin kuka tana cewa,

I have no one to see or call my own..,I’m all alone..

Karki cire Kai daga rahamar ubangiji ayshah,
Have faith in Allah insha Allah everything will be alright again.

Kamo hannun Mahmud yayi tareda Jan akwatinta ya kalleta yace,

Let’s go.

Kallonsa tayi saikuma ta sunkuyar dakai tabi bayansa ya bu’de musu motarsa suka shiga ya tada suka tafi.

Tunda taga sun fita garin Abuja ya gyara Zama tareda qarawa motar gudu sosai suka ‘dau hanya ta rintse idanuwanta hawaye suka gangaro zuciyarta ta karye Dan kuwa kobai fa’daba tasan gida zai kaita.

 

 

********
Zaune suke suna sauraron abinda shaikh abdallah yake fa’da zuciyarsa ba da’di..

Tabbas malam babba kun Bari shai’dan dason zuciya sunyi galaba akan sani da kukedashi na addini,

Meye al’ada?
Al’ada fa ba musulunci bace hasalima gurarare da dama tayi hannun Riga da abinda musulunci yace ayi.,

Malam babba wannan al’ada da kuka ‘dabbaqa gatanan Kuna gani tayi sanadin rushewar mutumci da girmanku a idon masu mutuntaku sbd yanzu meye amfanin wanna?””””yafada Yana ‘daga jaridar hannunsa ta ayshah da aka bugo.

Gyara Zama yayi ransa na qara ‘daci yace,

Wlh nayi baqin cikin rayuwar data samu ayshah sbd nida ban haifetaba nafi Jin zafin mummunar qaddarar data sameta,

Shi Wanda kuka wulaqanta ‘yartaku akansa gashinan Kuna gani a tv da jaridu irin kyakkyawar rayuwar dayake yi duk sanadin ‘yarku data Zama silar musuluntarsa.,

Maimakon da kuka gane komai ku gadewa Allah da aure sukayi ba zaman sa6on Allah ba saiku aje wata al’ada ku rufawa kanku asiri kubarsu.,
Idanma har hakan bazata yiyuba ku binciki ‘yarku Mana ku gano ta inda Zaku warware matsalar cikin ilimi,

Cikin tsananin sanyin jiki baba qarami yace,

Tabbas ayshah taso bayani Amma sharrin zuciya da 6acin ran laifin datayi ya Hana a saurareta…

Wannan shine babban kuskuren da kuka tafka amatsayinku na masana addini,

Wlh Koda yaushe aikin zuciya Babu komai atareda dashi Sai nadama da kuka.,

Yanxu gashi duk masu zuwa ‘daukar karatu da da’ira sun daina sbd ganin bakuyi aiki da alimin da kuke dashiba to maizasu cigaba da zuwa koya.?,

Da bahaushe,da yoruba,da kanuri,da buzu da Fulani da kowane yare ‘daya agurin Allah matuqar musulmaine,

Gskia wannan hukuncin da kuka ‘daukarwa ‘yarku yayi Muni ko a al’adar bare a musulunci,
Yanxu gashi Nan atsakanin ‘yayanku dakuka aurarma Sai sa6ani ake samu sbd yawancinsu bason juna sukeba tauyesu kuke sbd al’ada,

Ayshah tayi kuskure Amma Kuma tayi jahadi babba sbd yau musulmai da dama suna alfahari da shaikh nuraddeen hakama zuri’arsa kaf sun musulunta duk ta dalilin ‘yarku shin wannan bai isheku alfahariba?

Nine na ‘daura auren ayshah da nuraddeen akan sadaki naira dubu hamsin,
Ciro bundle ‘din 500 yayi ya aje gabansu yace,

Wannan shine sadakin ayshah danaketa ajiya Ina jiran ranarda komai zai daidaita namiqawa iyayenta Amma kun rigada kun tarwatse rayuwarta banga amfanin cigaba da ajewarba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button