TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Cikin sanyi da karyewar murya tace,
Duk lokacinda Abu yasamu ‘dan uwanka Mara kyau to kayi qoqarin nesanta kanka da abun Nan sbd gujewa mummunan sakamako irin wannan.
Zuciyata takasa nutsuwa da zuwa makarantar ki Dan haka ki guje afkawa cikin irin wannan mummunan halin.
Tsit tayi tana sauraron nasihar umminta duk datasan Sam ita bazata iya fadawa soyayya da wani yarenba bayan nata Dan itama gwargwado tana qyamatar wani yaren.
Washe gari ga murna ga baqin ciki Dan kuwa Banda iyayensu maza da sauran manyan mazajen gidan Babu Mai farin ciki musamman saudat data kwana tana kuka.
Koda zasu tafi bayan ‘daurin auren daqyar aka 6an6areta daga jikin umma sakina.
Ayshah kasa tsayawa tayi takoma ‘daki ta lafe tana tsiyayar hawayen tausayin saudat Dan jitake idan itace bazata iya rayuwa ba iyayenta da ‘yan uwantaba ko qin ji daga garesu.
Yau Monday kusan kowa nada lectures shiyasa makarantar take cike kowa Sai kaida kawo yake.
Lecture ‘daya tayi 8 to 10 Kuma bazatai wataba Sai 2 shiyasa Kai tsaye ta fito ta nufi masallacin Mata na cikin school din ko karatun alqur’ani tayi kafin time ‘din.
Tun safe mum ‘dinsa ke rigima dashi akan yaje makaranta ya dage akan bazashiba sbd tsoron ninja lady.
Zama tayi bakin lafiyayyan gadonsa dayake dunqule cikin lallausan bargo ta kamo hannunsa
Ya zame hannunsa tareda 6ata fuska yace,
Mum please don’t force me,I don’t wanna go.
Never Nik,,I will never force you but please Christ sake don’t leave your studies for some stupid crazy mask lady,, you’re a man Nik so please act like one..
Kwantowa jikinta cikin sanyin murya yace,
I’m scared mum.
Murmushi Murphy dake tsaye tuni yayi yace,
Nik she’s a normal human being just like you….
Hararsa mum tayi tareda ‘daure fuska tace,
Not like him,
And I’m giving you 7days if she tries even coming closer to him talk to the pc make sure she leaves the school for good,
And you Nik get up and get ready I’m giving you 15 minutes to leave.
Tana gama fa’da ta Fice ‘dakin Dan itama akwai zafi tana lalla6asa ne sbd tsananin sonda take Masa Amma Bata wasa da harkar karatun ‘yayanta hardaishi Nik ‘din daba karatun yakesoba sbd son jikinsa da rashin son wahala.
Wurgi yayi da pillow kamar wani qaramin yaro yanajin kamar yayi kuka sbd har cikin ransa tsoranta yake.
Wanka yayi ya shirya yafito tsaf Sai qamshi yake ga wani shining da fatarsa take.
Saukowa yayi Yana ‘daura wani tsadadden Rolex watch ‘dins na diamond.
Davina ce kawai zaune a dining tana breakfast taci ado cikin wata tsinananniyar gown iya cinya black saita da’da fiddo hasken fatarta gata dama kyakkyawa kamar Nik din.
Ko kallo dining ‘din bai ishesaba ya fice sbd haushin ansashi tafiya makaranta dole
Da hanzari Murphy ya aje tea ‘din dayake Sha yabi bayansa.
Tunda suka shiga makarantar yake dube dube gabansa na fa’duwa.
Murmushi Murphy yayi Yana mamakin halayya irinta Nik sbd komai nasa kamar mace yake yinsa Dan qila ko Davina dake mace Kuma qanwarsa tafisa juriya da qarfin zuciya.
Daqyar yaga sun fito first lecture dinsu suka nufi restaurant sbd yunwa yakeji.
Harsun kusa isa ya dakata Yana tuno abinda yafaru last time dasuka zo.
Kallon Murphy yayi tareda nuna restaurant din da ido yace,
Buy everything and Meet me in the car.
Daria Murphy yasaki kafin ya wuce sbd ganin duk Nik din a firgice yake.
Cikin nutsuwarta take tafiya kamar ko yaushe kanta a qasa gurin lectures zata koma Dan Time yayi.
Saurin ja da baya tayi sbd karo datayi da mutum.
Ajiyar zuciya tasaki ahankali sbd ganin macece tayi karo da ita ba namiji ba.
Da sanyin muryarta tace,
Sorry..
‘Dif gurin sukayi sbd yau shine karo na farko da wani yaji muryarta a makarantar.,
Zaqi da sanyi tareda laushin muryar yasa kowa qara kwa’daituwa dason ganin fuskarta musamman ma zeey(zeey is back)???? Wadda tafi kowa takura da tsangwama Mata ko a wancen karon itace sanadin fadowarta stairs harta fadawa ‘dan hutu.
Kallonta zeey tayi tareda sakin wani shu’umin murmushi tace,
Yaudai Kam dole muga abinda ke lullu6e cikin niqaf ‘din Nan Dan jikina nabani kilama aljana ce muke tareda ita.
Danne niqaf dinta tayi ta ra6ata zata wuce taji ta riqo hannunta tareda dawo da ita baya da qarfi.
Wani qaramin flask taga ta bu’de ba zata ta watso Mata ruwan ciki da qarfi saitin fuskarta tayi saurin juyarda fuskarta gefe daidai da kawowarsa gurin ba zato yaji saukar ruwan zafi a qirjinsa..
Da gudu suka bar gurin shukuma want azababben ihu yasaki tareda sakin wayoyinsa
Da sauri ta juya Dan ganin wanda aka qona shima ‘dagowa yayi Dan ganin wanda ya qonasa sunayin four eyes kawai saiya yanke jiki ya Fadi a sume.
Mamuh????
_dont forget to follow, vote and comments_
[7/8, 8:41 PM] 0mmer Farouk: *_MAMUH GEEE_*
_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida_….
_viawattpad@mamuhgee_
*5&6*
Mummunar fa’duwa gabanta yayi ganin wanda abin ya sama juyawa tayi da sauri tabar gurin sbd Murphy dayayi mata alamar ta ta tafi,
Cikin tashin hankali da fargabar masifar mum ya kinkimesa Sai asibiti.
Koda su mum suka iso asibiti Banda tashin hankali babu abinda take ciki sbd Murphy cemata yayi coffee mai zafi Nik ‘din yaje Sha ya zube Masa.
Koda Dr yafito yayi musu bayanin ba wata qonewa bace dan da alama ruwan basuda wani mugun zafi kawaidai yaji tsorone dakuma qila rashin sabo.
Fita mum tayi Dan Kiran waya hakama Finn bayanta yabi Davina kuwa kujerar ‘dakin ta zauna tana chatting tana taunar chewing gum ‘dinta.
Kallonta Murphy yayi lokacinda Nik ‘din ya farka yaga hankalinta nakan wayarta ya maido kallonsa kan Nik murya qasa qasa yace,
Ninja lady….
Manyan fararen idanuwansa ya ware cikin tsoro,,
Murphy yayi saurin dafesa yace,
Easy Mama’s boy,she’s not hia but she’ll soon be if you tell your mum that she is responsible for this.
Kallon wat do you mean yayi Masa,
Yace,
Yes bcox your mum won’t let it go in vain so she’s probably coming to take her revange and who knows h….
A tsorace ya katseshi da cewa,
No no no no i won’t tell my mum and you too won’t tell her anything…
Murmushi Murphy yasaki ganin ya ku6utarda ninja lady cikin sauqi sbd yasan duk mum taji the poor girl will lose everything.
Koda mum takuma tambayarsa akan qonewar yawu ya ha’diye tareda tuno abinda Murphy yafada saiya shagwa6e Mata batareda yabata amsa ba.
Aiki ja yasamesu Dan kuwa jinya ake ba sauki ‘dan lele ya qone qiri qiri akasa Dr treatment ‘din dole sbd dai shi baiga wata qonuwa ba Amma tunda Mama’s boy ya lafe yace yanajin zafi agurin hakanan ake jinyar harkusan sati biyu a asibitin kafin suka dawo gida nanma wata sabuwar kulawar ta tashi masu aikin gidan basuda hutu Sai hidima suke.
Koda yaji sauqi qara lafewa yayi Dan karyaje makaranta mum ta takurasa saiyaje sbd duk son ‘yayanta bata wasa da karatunsu.
Shika’dai yau yazo makarantar sbd Murphy na gurin wani program.
Zaune yake kan motarsa bayan ya fito lectures
sanye yakeda black dress da black speck Sai kyau da hasken fatarsa suka qara fitowa sbd duhun kayansa.
Waya yakeda dad ‘dinsu saiga wasu friends ‘dinsu dake shige Masa Amma shi Sam bai cika son mu’amala dasuba sbd sun cika neman Mata Dan ko acikin mota suna iya having sex da Mata Sam basuda class ko agurin za6ar matan shikuma mutum ne Mai son Abu Mai kyau tsaftatacce danshi qyamarma wasu matan yake shiyasa bai cika wani shiri dasuba.