HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Datse Kiran yayi Yana kallon ‘daya daga cikinsu Mai suna Josh.

Murmushi Josh ‘din yayi tareda Hawa tasa motar ya zauna yace,

Unbelievable Niklaus Aiden…
How could you let yourself get embarrassed by letting people know you’re scared of some stupid mask lady afterall you’re a man..

Kallonsa yayi da fararen idanuwansa ya lumshesu batareda yace komai ba sbd shima Sam bada son ransaba yake tsoronta gashi yanxu zancen yafara ya’duwa acikin makarantar.

Matsowa Josh yayi daf fuskarsa yace,

Let’s do one,, let’s get rid of this problem..

How?
Yace Yana Danna wayarsa.

Let’s scare her….

Meaning?””’yakuma fa’da Yana kallon fuskar Josh ‘din.

Kashe Masa ido ‘daya yayi Yana murmushi.

Shiru yayi Yana nazarin shawarar Josh ‘din sbd zuciyarsa tayi na’am da zancen.
Murmushi yasaki tareda dirowa motarsa yashige Yana cewa,

I will see you guys tomorrow.

 

Washe da hadari sosai aka tashi shiyasa jiki ba qwari ta shirya ta wuce makarantar.

Tana Isa makaranta ruwan ya 6arke masu qarfi Nan kowa yafara gudu Dan fakewa.

Fixgota taji anyi tareda jefata cikin mota akabar makarantar a guje da ita batareda kowa ya luraba sbd qarfin ruwan.

Babban filin qwallo ne daya ha’du,
Tsakiyar filin yake zaune kan kujera sauran abokanansu biyu na tsaye riqeda umbrella sun Kare Masa ruwa.

Three quarter jins ne a jikinsa da boot Sai wata jibgegiyar rigar sanyi Mai laushi da hula.

Tsakiyar gurin motarsu ta tsaya suka bu’de tareda jefota inda yake zaune gabansa.

Qanqame jikinta tayi tareda sakin kukan tausayi da fargabar masifar dake gabanta ga ruwan saima tsananta qarfi suke.

Fa’duwa gabansa yayi ya miqe tsaye tareda juya musu baya Dan har lokacin akwai sauran tsoranta a ransa.

Zagayeta su Josh sukayi suna qyakyata dariya.

Rintse idanuwanta tayi tareda qanqame jikinta tana sake sakin Wani sabon kukan.

Niqaf ‘dinta Josh ya fixgo tareda wurgi dashi tayi saurin duqar da kanta tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskar.

Hijab ‘dinta yakuma fixgowa da qarfi Saida ya 6arke tundaga sama har qasa.

Doguwar rigar wani red shaking material ne ajikinta ruwan dake dukanta yasa tuni ya lafe ya kwanta ko ina a jikinta.

Wani yawu dukkaninsu suka ha’de sbd wata irin kyakkyawar surar fuxgar hankali dasuka gani.

Hannu Josh yakai zai janye hannuwanta don ganin fuskarta sbd shi tuni yagama kwa’daituwa Dan idanuwansa harsun fara wani Jan kwa’dayinta.

Caraf yaji anriqe hannunsa da qarfa.

Dagowa yayi sukai ido hu’du da Murphy.

Murmushi yasaki yace,

What is the rush Murphy?
We’re all gonna enjoy so let me go first.

Turesa Murphy yayi da qarfi
Jin sunan Murphy yasa Nik juyowa ahankali idanuwansa Basu sauka ko inaba Sai kanta
Gabansa yayi mummunar fa’duwa…,

Fuskarta soke take tsakinin qafafuwanta babu Wanda yaga fuskarta Sai kyakkyawar farar fatarta da surarta data bayyana.

Kuka take sosai Amma ba’anjin qarar kukan sbd qarar ruwan saman dake sauka Dan dukkaninsu akansu ruwan ke sauka idan kacire shi shida baya shiga ruwan sama Dan yanxun ne zai kwanta ciwo.

Qura Mata ido yayi Yana kallon yanda jikinta ke girgixawa sbd sheshekar kukan datakeyi,,

Duk qarar ruwan saman masu qarfi dasuka hana kowa Jin kukanta shi tsaf yake Jin sautin kukan na shiga kunnuwansa suna amsa amo.
Cak ya qame agurin dukan zuciyarsa na tsananta.

Hijab ‘dinta Murphy ya ‘dauka ya yafa Mata
‘dagowa tayi akaro na farko ta takallesa da manyan idanuwanta dasukai jajir.

Bugawa gabansa yayi da qarfi yaja Baya da qarfi Yana kallon fuskarta.

Dukkaninsu ja da baya sukayi cikin tsoro sbd ganin Murphy ya tsorata da ganin fuskarta sbd dukkaninsu babu Wanda yagani Dan baya ta Basu.

Rintse idanuwanta tayi hawayen ciki suka gangaro takuma kallonsa.

Niqaf ‘dinta ya wawuro ya miqa Mata sbd shi kansa bayason yacigaba da kallon wannan kyakkyawar fuskar da baita6a ganin irinta ba Dan zai iya zaucewa.

Kar6a tayi tasaka tareda gyara zaman 6arkaken hijab ‘dinta tabar gurin tana tsiyayar hawayen baqin ciki.

A tsorace suke kallon Murphy Dan son yafada musu abinda yagani a fuskarta daya tsoratashi.

Dahar zai fa’da musu saiya fasa ya kalli Nik da ke tsaye kamar andasashi sbd har lokacin kukanta na amsa kuwa a kunnuwansa zuwa zuciyarsa.

 

 

Mamuh????

 

 

_Dont forget to follow, vote and comments_.
[7/8, 8:41 PM] 0mmer Farouk: *_MAMUH GEEE_*

 

_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida_….

 

_viawattpad@mamuhgee_

*7&8*

 

Harta Isa iga ruwa ake sosai shiya Hana aga 6arkewar hijabinta da jajayen idanuwanta.

Shigewa ‘daki tayi ta dunqule da jiqaqun kayan tasaki wani sabon kukan.

Wasa wasa saigata da zazza6i ciwo kwance rigis sbd kukan datake yawan yi batareda anluraba.
Jinya tayi tsawon kwanaki kotaji alamar sauqi saita lafe sbd Sam batako qaunar taji ankira sunan makaranta bare hartayi sha’awar zuwa
Babu abinda tafi buqata yanxu kamar ace antsaida ranar aurenta da ya Umar anyi ta huta.

 

 

*********
Kwance yake cikin lallausan bargon gadonsa idanuwansa a lumshe Yana sauraron Murphy dake Masa fa’da akan abinda ya yarda su Josh suyiwa ninja lady.

Sautin kukan tane yadawo Masa ya cikin kunnuwa ya lumshe idanu tareda qara shigewa cikin bargo.

Kwana biyu mum ‘dinsa tarasa gane kansa sbd son jikinsa ya da’du dan kullum daga makaranta Sai gida yazo ya kwanta ya lumshe idanu.

Kwana ‘daya kwana biyu har sati batazo makaranta son ganinta yake sbd kullum Murphy bayada zance Sai nata shiyasa yanxu yakeson yaganta yayi Mata kallon mintuna sbd kawai ya cire tsoronsa akanta.

 

Yau kwana goma rabonta da makaranta dole tashirya zuwa sbd yawan tambayarta da ya Umar keyi akan rashin son zuwanta makaranta yanxu.

Tsaf tashirya cikin dogon hijab ‘dinta maroon da niqaf dinta harma da safarta ta hannu da qafa kamar kullum.

Tunda tafito gida take addua harta Isa makarantar.

Sosai takuma Kama kanta sbd fahimta datayi komai zai iya faruwa matuqar batayiwa kanta babbar katanga da duk wata hanyarda Nik yabi ba.

 

Cikin ikon Allah hankalinta ya ‘dan kwanta sbd kusan sati biyu kenan Basu ha’duba acikin makarantar Nan tasawa ranta Allah ne ya kar6i adduarta yayi Mata tsari dashi.

 

Sun fara exam shiyasa Bata cika Zama cikin mutane ba saidai taje can baya inda Babu mutane ta zauna tayi karatu kokuma ta zauna tana nazarin rayuwarta a makarantar.

Yau zaune take baya gurin wasu ciyayi dasuka kwanta luf iskar ni’ima na ka’dowa ahankali tana ratsata.

Ba karatu takeba kawai zaune take tareda lumshe idanu tayi zurfi cikin tunanin rigimar dasukayi jiya da ya Umar akan shima nijar yakeson komawa bayan aurensu itakuma Sam bazata iya rabuwa da iyaye da sauran ‘yan uwantab dukda Sam Bata iya ko ‘dagowa tayi Masa dogon kallo bare harta iya musa masa saidai tashige ‘daki tayita hawayenta.

 

Zaune yake shima agurin ammashi Saida aka kafa Masa ‘yar rumfa sbd iskar tayi Masa yawa sbd Sam ko ka’dan jikinsa bayason sanyi sosai Dan Nan take ne zai fara mura ko zazza6i.

Tare sukeda Murphy Amma yaje ya dubo Davina data kirasu yanxu wai gatanan tareda police cikin school ‘din sbd glass ‘din motarta da’aka fasa aka ‘dauke Mata purse da laptop aciki.

Shika’dai ya rage zaune agurin fuskarsa sanye da black goggles daya qara fiddo haske,kyau,hutu tareda wayewarsa a fili.

Wayarsa yake ta6abawa kamar daga sama yaji Abu na tafiya a kafa’darsa ya zabura da sauri ya Duba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button