HAUSA NOVELTAURA BIYU Complete Hausa Novel

TAURA BIYU Complete Hausa Novel

Wani kallo tabisu baba Mal dashi kafin tashige office ‘din officer incharge tabarsu tsaye kafin shima baba Mal yashiga daga baya.

Alamari dai baiyi kyauba sbd kaca kaca akayi a office ‘din hardasu fa’da dansu Yaya abbakar taruwa sukayi sukaiwa Finn duka Suma Nan police suka hau dukansu kan kace me gurin ya ida hargitsewa Saida akaida gaske aka shiga tsakani.

 

Kwance yake a Palo Yana hutawa Dan har lokacin qarfinsa bai gama dawowaba duk da dai tunanine wannan karon yafi hanasa qarfafa jikinsa.

Three-quarter blue jeans ne a jikinsa da farar designer shirts qal,

Fatarsa tayi kyau hutu ya da’da bayyana ajikinsa sbd tun ranarda aka sallamosa ko gate ‘din gidan bai ta6a fitaba Yana lafe kullum ana lilinsa.

 

Shigowa Murphy yayi cikin yanayi na damuwa ya kalli Nik yafara Koro masa bayanin halinda ake ciki.

Cikin wani irin yanayi zancen ke shiyarsa ya aje cup ‘din milkshake dake hannunsa ya miqe tareda kallon Murphy yace,

Take me to the station…

Gudu Murphy yayi cikin mintuna qalilian suka iso station ‘din daidai lokacinda Davina ta ‘daga handbag ‘dinta Mai qarfe ajiki zata qwalawa ayshah cikin zafin nama ya janyeta ta fa’do jikinsa cikin rashin sa’a niqaf dinta ya zame ya fa’di qasa.

Wani wahallalen numfashi yasaki kunnuwansa da idanuwansa sukai ‘dif numfashinta dake fita da sauri kawai yakeji.

Fixgosa ya Umar yayi da qarfi tareda sakar Masa wani wahallalen Marin dayasa hancinsa 6arewa da jini tayi saurin rintse idanuwanta wani nauyi na na sauka zuciyarta.

Ihu mum tasaki tareda shararawa Umar wani gigitaccen Marin itama.

Zaburowa su abbakar sukai aka damqesu tareda turasu cell shikuma mum da Murphy sukaja hannunsa zuwa mota Dan kaisa asibiti Dan hancinsa dake jini
Shikuwa duk baimasan sunayiba idanuwansa na kanta ko qiftawa bayayi

Itakuwa kanta na qasa takasa ‘dagowa Dan jikinta yabata idonsa har lokacin na kanta.

A asibiti bayan anyi treating ‘dinsa sun dawo gida kwantawa yayi kamar Mai bacci tareda dunqulewa cikin bargo bugun zuciyarsa na tsananta.

Daqyar da biyan ku’din suka samu aka sakosu abbakar suka dawo gida zuciyoyinsu duk a qone da tsananin 6acin Rai da baqin ciki ace wai su rasa abin arxikin dazasuyi fa’da dashi Sai kafirai.

Fa’da da nasiha Kam ayshah tashasu harta gaji.,

Sati ‘daya kenan da faruwar alamarin kullum tana ‘daki kwance lamo ko doguwar magana batason yi Dan ita tuni tacire Rai da batun komawa makaranta Dan tasan yanada wuya abarta takoma.

Zaune take da safe tana a ‘dakinsu tana karanta wani hadisi su husnah nata Shirin tafiya makaranta.

Nuratu ce tashigo cikin uniform ‘din makarantarsu takalleta tace,

Anty ayshah ya Umar nakira.

Lumshe idanu tayi tareda rufe hadisin ta miqe tsaye tasaka dogon hijabinta ta nufi ‘dakin mama sakina Dan tasan yanacan.

Kallo ‘daya yayi Mata ya ‘dauke Kai sbd duk ya kalleta yanxu tunowa yakeda fixgowarda wannan shegen Christian yayi Mata ta fa’da jikinsa saiyaji zuciyarsa na tafasa Dan duk ranar dayakuma ganin wannan gayen ko a hanyane saiya cire Masa hannun daya ta6a Masa aysharsa dashi.

Gaishesa tayi a ladafce taredayin qasa dakai tana sauraron abinda zai fa’da.

Cikin danne baqin cikinsa yace,

Ki shirya kici gabada zuwa makaranta munyi mgn dasu baba sbd bazakibar karatunki kan wasu kafiran banxaba.

Lumshe ido tayi sbd yanda hakanan zancensa ya daki zuciyarta ahankali tace,. To tareda ficewa tabar ‘dakin.

 

 

Mamuh????

*_MAMUH GEEE_*

 

_*TAURA BIYU….*_????
_Mi amor-mi vida_….

 

_viawattpad@mamuhgee_

*11&12*

A sanyaye ta shirya tanajin fargaba da tsoron sake ha’duwarta da Nik a makaranta.

Kodata fito nasiha da da’da su baba Mal da babanta suka sake yimata akan kwata kwata ko hanyar da wainnan kafiran sukabi karta kalla bare tayi sha’awar bi.

Tunda suka iso ta fito bus taji hankalinta ya ninka tashi ta rintse idanuwanta ta karanto addua tareda gyara zaman niqaf dinta ta nufi hanyar lecture hall ‘dinsu cikin nutsuwa da sanyi.

Cikin ikon Allah har lokacin dawowanta gida Bata ha’du da matsalarta,,,,sunandata saka Masa kenan.

One day,,,two days,,,,three,, four,,, five har one week ko maikama dashi Bata Kuma ganiba shiyasa hankalinta ya ‘dan kwanta sbd Sam Bata qaunar sake ganinsa kodan gudun faruwar abinda take gudun ya faru..

 

Yau Kam gabaki ‘daya jikinta a sanyaye take jinsa shiyasa
Daqyar tasamu taga sun fito first lecture dinsu tafito Kai tsaye ta nufi hanyar mosque Dan Sai after two hours zasu shiga wata lecture ‘din.

Saukowa stairs take cikin nutsuwa kanta a qasa sbd hango su zeey datayi duk da dai tasaba da tsokanarsu da cin zarafinsu.

Wucesu tazoyi zeey tayi saurin Shan gabanta tana dariya tace,

Ninja lady bazaki fa’da Mana yaya zaman police station yake?

Dariya sauran suka sheqe da ita suna cewa,

The officers mst be very scary to see what’s behind the niqaf…

Cika idanuwanta sukaida hawaye ta ra6asu zata wuce idonta ya sauka cikin nasa Yana tsare yayi folding hannuwansa Yana kallon duk abinda ke faruwa da alama bai Jima da isowa gudinba.

Cak ta tsaya hawayen datake riqewa suka gangaro Mata Wanda shika’dai ne yaga gangarowarsu daga idonta sbd niqaf ‘dinta Amma qurewar kallonsa akanta yasa yaga hawayen.

Lumshe fararen lazy eyes dinsa yayi sbd Jin wani mugun zafi a zuciyarsa yayi saurin dafewa tareda kallon saitin zuciyarsa.

Cikeda tsoro da mamaki ya ‘dago saiyaga Bata gurin da sauri Yakoma mota tareda rufewa ya kunna AC Yana sauke numfashi.

Murphy kuwa matsowa yayi gaban guys din yakallesu cikin ‘daure fuska yace,

This should be the last ok… because the next time I see you guys making any troubles…hmm it won’t be good…so careful guys.

Juyawa yayi yabarsu suna binsa da kallo zuciyoyinsu cikeda haushinsa Dan ganin suke ina ruwansa dasu afterall sune musulmai ‘yan uwanta bashi dayake Christan ba.

Ido ‘daya mujahid ya kashewa shafii Yana murmushin mugunta.

Dariyar Jin da’din shafii yasaki sbd gano Mai mujahid ‘din ke nufi.

Wucewa sukai suna fiton Jin dadi Dan sukadai sukasan abinda suke Shirin qullawa.

 

Kodata Isa gida yau ta tu6e tayi wanka tareda sallah taci abinci yini tayi
Karatun alqur’ani sbd zuciyarta datakejinta cikin yanayi na damuwa.

 

 

Kwance yake bakin pool ‘din cikin gidansu cikin rumfar dake gurin Dan hutawa,
dagashi Sai three-quarter farar fatarsa Sai glowing take sbd hutu,
Idanuwansa a rufe suke Banda tunani Babu abinda yake.

Mum ‘dinsa dake tsaye bayansa nesa dashi tana kallonsa cikin damuwa ta ‘daga waya takira Murphy tace tanason ganinsa now now.

Tana tsaye gurin harya shigo gidan ya iso gurinta tareda gaidata.

Bata amsa gaisuwarda yake mataba ta nuna Masa inda Nik ke kwance da ido cikin damuwa tace,

For the past few days he’s been acting so weird and it’s killing me…

Juyowa tayi ta fuskanceshi tace,

Can you please tell me what is happening,,,…I asked him so many times he said he don’t know wat his problem is…

Kallonsa Murphy yayi kafin ya juyo ya kalli mum ‘din yace,

I don’t know anything mum but……

Katsesa tayi da fa’din,

I want to know wat his problem is by tomorrow so go and make sure you know it all.

Juyawa tayi tabar gurin shikuma ya doshi Nik ‘din cikeda tunani kala kala aransa.

Zama yayi kusada Nik din tareda ‘daukar cup ‘din ruwan dake gabansa yasha kafin ya ‘dan juyo ya kalli Nik ‘din da still idanuwansa ke lumshe cikin sauke nannauyan numfashi yace,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button